Bayan Tafiyar Ganduje, 'Yan Majalisar Wakilai 7 Sun Bar PDP da YPP, Sun Koma APC
- 'Yan majalisar wakilai bakwai daga Akwa Ibom sun sauya sheka zuwa APC, shida daga PDP ɗaya kuma daga YPP, saboda rikicin cikin gida
- Sakamakon wannan sauya sheƙa, Mark Esset, ya zama ɗan jam'iyyar PDP ɗaya tilo daga jihar Akwa Ibom da ya yi saura majalisar wakilai
- Shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya bukaci shugaban majalisa, Tajudeen Abbas da ya wofantar da kujerun wadanda suka sauya shekar
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Guguwar sauya sheƙa ta sake kadawa yayin da 'yan majalisar wakilai bakwai daga jihar Akwa Ibom suka sanar da komawasu zuwa jam'iyyar APC.
Daga cikin waɗanda suka sauya sheƙar har da 'yan majalisa shida daga jam'iyyar PDP da kuma ɗan majalisa ɗaya daga jam'iyyar YPP.

Source: Twitter
'Yan majalisar PDP 6 sun koma jam'iyyar APC
Kakakin majalisar wakilai, Tajudeen Abbas, ne ya karanta sakonnin sauya sheƙar 'yan majalisar a yayin zaman majalisar na ranar Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Mambobi shida na babbar jam'iyar adawa ta PDP da suka sanar da sauya sheƙa zuwa APC su ne:
- Unyime Idem, mai wakiltar mazabar Ukanafun/Oruk Anam;
- Esin Etim, mai wakiltar mazabar Mbo/Okobo/Oron/Udung Uko/Urue;
- Ekpo Asuquo, wanda ke wakiltar mazabar Etinan/Nsit Ibom/Nsit Ubium;
- Uduak Odudoh, ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Ikot Abasi/Mkpat Enin/Eastern Obolo;
- Okpolupm Etteh, mai wakiltar mazabar Eket/Esit Eket/Ibeno/Onna;
- Okon Bassey, mai wakiltar mazabar Itu/Ibiono Ibom.
Sauya shekarar Ukpong-Udo da tasirin hakan
'Yan majalisar sun bayyana rarrabuwar kai da tsawaitar rikice-rikicen cikin gida a jam'iyyar PDP a matsayin dalilansu na yanke shawarar barin jam'iyyar.
Haka kuma, Emmanuel Ukpong-Udo, ɗan majalisar da ke wakiltar mazabar Ikono/Ini a Akwa Ibom, shi ma ya sauya sheƙa daga jam'iyyar YPP zuwa APC.
Da waɗannan sauye-sauye, Mark Esset, wanda ke wakiltar mazabar Uyo/Uruan/Nsit Atai/Asutan/Ibesikpo, ya kasance ɗan PDP ɗaya tilo daga Akwa Ibom a majalisar wakilai.
Wannan sauya sheƙa ya biyo bayan na Umo Eno, gwamnan Akwa Ibom, wanda ya fice daga PDP zuwa APC a watan Yunin 2025.

Source: Twitter
Martanin shugaban marasa rinjaye na majalisar
The Cable ta rahoto cewa shugaban marasa rinjaye, Kingsley Chinda, ya nuna adawa ga sauya sheƙar, yana mai cewa ficewa daga jam'iyyar da ta ɗauki nauyin zaɓen dan majalisa na raunana dimokuraɗiyya.
Chinda ya ce Kotun Koli ta bayar da bayani game da abin da ya idan ya faru ne za a kira shi da rabuwar kai a jam'iyya, yana mai lura da cewa babu wani rikici a PDP da 'yan majalisar suka fada.
Ya bayyana sauya sheƙar a matsayin haramtacciya kuma ya buƙaci shugaban majalisar da ya yi aiki da Sashe na 68 (1) (g) na Tsarin Mulki ta hanyar wofantar da kujerunsu.
'Dan majalisar Enugu ya sauya sheka zuwa APC
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Hon. Chimaobi Atu, ɗan majalisar wakilai daga jihar Enugu, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar LP zuwa APC mai mulki.
Kakakin majalisar wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas ne ya karanta wasiƙar sauya shekar ɗan majalisar yayin zaman majalisar da aka gudanar.
A cikin wasiƙar, Hon. Atu ya bayyana cewa rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye jam’iyyar LP ne suka sa ya ɗauki matakin sauya sheka, domin ci gaba da wakiltar jama’arsa yadda ya dace.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


