Takarar Shugaban Ƙasa Za Ta Tarwatsa Atiku, Obi da Sauran Ƴan Haɗaka a ADC? An Samu Bayani

Takarar Shugaban Ƙasa Za Ta Tarwatsa Atiku, Obi da Sauran Ƴan Haɗaka a ADC? An Samu Bayani

  • Babban jigon siyasa kuma ɗan jarida, Dele Momodu ya ce batun tikitin takarar shugaban kasa ba zai raba haɗakar jam'iyyar ADC ba
  • Cif Momodu ya ce Atiku Abubakar, Peter Obi da sauran jagororin adawa sun amince babu abin da zai tarwatsa wannan haɗaka
  • Ya bayyana farin cikinsa kan yadda manyan jagororin adawa suka haɗa kansu wuri ɗaya domin ceto Najeriya daga mawuyacin hali

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Fitaccen ɗan jaridar nan, Cif Dele Momodu ya ce babu wani abu da sunan rikicin cikin gida da zai raba kan jagororin adawa da suka ƙulla haɗaka a ADC.

Momodu ya ce duka manyan adawar da suka shiga wannan haɗaka sun amince babu wani abu da zai zo ya tarwatsa su a ƙoƙarinsu na karɓe mulkin Najeriya a 2027.

Kara karanta wannan

ADC: Bayan hasashen El-Rufa'i, sabon rikici ya danno jam'iyyar hadakar adawa

Dele Momodu ya shiga haɗaka gadan gadan.
Yan adawa sun amince ba za su bar kowace irin matsala ta raba haɗakarsu a ADC ba Hoto: Dele Momodu
Source: Facebook

Jigon siyasar ya bayyana hakn ne da yake jawabi a cikin shirin Prime Time na gidan talabijin na Arise TV a ranar Laraba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadakar Atiku, Obi da jiga-jigan ADC ta kankama

Momodu ya bayyana farin cikinsa bisa ƙaddamar da wannan ƙawance, yana mai cewa ’yan adawar da ke cikin jam’iyyar ADC sun shirya tsaf domin kayar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu da APC.

An ƙaddamar da haɗakar ne ƙarƙashin jagorancin tsohon Mataimakin Shugaban Ƙasa, Atiku Abubakar, kuma manyan ’yan siyasa da dama sun halarta a Abuja.

Daga ciki akwai dan takarar shugaban ƙasa na LP A 2023, Peter Obi; tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola da tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark.

Sauran sun ƙunshi tsohon shugaban APC na ƙasa, John Odigie-Oyegun, tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai; tsohon ministan shari’a, Abubakar Malami, tsohon ministan sufuri, Rotimi Amaechi da sauran jiga-jigai.

Tikitin shugaban ƙasa zai tarwatsa ADC?

Kara karanta wannan

2027: Muhimman Dalilan da suka sa Atiku, Peter Obi da ƴan haɗaka suka zaɓi jam'iyyar ADC

Momodu ya ce ’yan siyasar da ke cikin haɗakar ADC Nigeria suka sa a gaba fiye da muradin kansu.

Da aka tambaye shi ko an riga an raba mukamai irinsu tikitin shugaban kasa tsakanin manyan jiga-jigan haɗakar, Dele Momodu ya ce a’a ba a kai wannan matakin ba.

Jiga-jigan adawa sun shirya tunkarar zaben 2027.
Dele.Momodu ya ce yan adawa da suka yi haɗaka a ADC kishin ƙasa suka sa a gaba Hoto: @Atiku
Source: Twitter

Ya ƙara da cewa duk da cewa kowa ya san abin da ka iya faruwa, sun amince ba za su bari wani saɓani ya raba kansu ba.

“Ina da tabbacin cewa sun san irin abubuwan da za su faru, amma sun yanke shawara kuma sun yi alkawari cewa ba za su bari hakan ya raba haɗakarsu ba.
"Wannan abin farin ciki ne a wurina. Ina murna sosai,” in ji Momodu.

Ya ƙara da cewa ’yan siyasar da ke cikin ADC ba don neman mulki suka shiga ba, sai don ceto ƙasar nan, kamar yadda Vanguard ta ruwaito.

El-Rufai ya faɗi dalilinsu na rungumar ADC

A wani labarin, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya ce haɗakar ƴan adawa ta shirya gwabzawa da jam'iyyar APC mai mulki a zaɓen 2027.

Kara karanta wannan

ADC: An bayyana wanda zai jagoranci haɗakar su Atiku zuwa fadar shugaban ƙasa a 2027

El-Rufa'i ya ce hakan na daga cikin dalilan da ya sa suka amince da amfani da jam’iyyar ADC domin cimma manufofinsu na ceto Najeriya.

Bugu da ƙari, ya yi zargin cewa gwamnatin APC na iya shiga duk wata sabuwar jam’iyya da ‘yan adawa suka koma domin kawo masu cikas ta hanyar haɗa su faɗa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262