Haɗaka: Atiku, El Rufai da Jiga Jigai Sun Hallara domin Ƙaddamar da Jam'iyyar ADC
- Ƴan adawa daga jam’iyyun siyasa daban-daban sun hallara a Cibiyar Yar’Adua domin kaddamar da kawancen ADC a Abuja ranar Laraba
- Atiku Abubakar, Peter Obi, Nasir el-Rufai, da Dino Melaye suna daga cikin wadanda suka halarci taron da kuma Solomon Dalung da Dele Momodu
- An dakatar da taron daga otal din Wells Carlton bisa “dalilan cikin gida”, amma daga baya an canza wurin zuwa Cibiyar Yar’Adua domin cigaba
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Yan siyasa daga jam’iyyun adawa daban-daban sun hallara a cibiyar Yar’Adua da ke Abuja domin taron manema labarai da jam’iyyar ADC ta shirya.
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar; dan takarar shugaban kasa na LP, Peter Obi, Nasir El-Rufai da Dino Melaye sun isa wurin.

Source: Twitter
TheCable ta ce tsohon ministan matasa da wasanni, Solomon Dalung, dan jarida, Dele Momodu, tsohon sanata, Gabriel Suswam da Ireti Kingibe wacce sanata ce mai ci daga LP sun halarta.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An soke taron haɗaka a otal din Abuja
Wannan na zuwa ne bayan shirin kaddamar da hadakar jam'iyyun adawa ya samu tasgaro bayan otal din za za a yi taron ya fasa ba su wurin taro a yau Laraba 2 ga watan Yulin 2025.
An shirya gudanar da taron ne a otal ɗin Wells Carlton da ke Asokoro, Abuja, amma daga bisani masu otal ɗin suka soke taron.
A cewar sakon soke taron da Momodu ya wallafa a Instagram, hukumomi a otal ɗin suka ce an soke taron ne saboda “batun bin doka”.
Daga bisani, shugabannin kawancen sun samo sabon wurin gudanar da taron a Cibiyar Yar’Adua, inda taron ya ci gaba kamar yadda aka tsara.

Source: Twitter
Jiga-jigan da suka halarci taron haɗaka a Abuja
Tsohon gwamnan Rivers Rotimi Amaechi, tsohon mataimakin kakakin majalisar wakilai, Emeka Ihedioha, suma suna cikin wadanda suka halarci taron, cewar Channels TV.
Taron ya haɗa da wakilai daga jam’iyyar PDP, SDP da LP, sai tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark da ya jagoranci wasu shugabanni zuwa dakin taron a Abuja.
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola da tsohon gwamnan Sokoto, Aminu Tambuwal suma sun isa wurin domin taron na ADC.
A safiyar yau, kaddamar da kawancen ADC ta fuskanci cikas bayan dakatarwar gaggawa da masu gudanar da wurin taron suka yi a ƙarshe.
2027: Peter Obi ya mika bukatar takara
Kun ji cewa dan takarar shugaban kasa a LP, Peter Obi ya gabatar da bukatar mulki na wa’adi guda ga gamayyar ‘yan adawa da ke shirye-shiryen babban zaben 2027.
Na hannun daman dan takarar LP a zaben 2023, Yunusa Tanko ya ce Peter Obi na da kwarin gwiwar cewa a shekara hudu a fadar Aso Rock za a iya sauya Najeriya gaba ɗaya.
Hakan ya biyo bayan samun sarauta daga unguwar Pantami da dan takarar LP inda magoya bayansa suka ce ayyukansa na jin ƙai da inganta rayuwa ne dalili.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

