David Mark: Takaitaccen Tarihin Jagoran Hadakar ADC da Ya Yi Gwamna tun a 1984

David Mark: Takaitaccen Tarihin Jagoran Hadakar ADC da Ya Yi Gwamna tun a 1984

A yau Laraba, 2 ga watan Yuli, 2025, David Mark ya zama shugaban riko na jam'iyyar ADC bayan an amince da taruwa a cikin don adawa da APC a zabe 2027.

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja David Mark, wanda tsohon shugaban majalisa ne na daya daga cikin sanannun shugabannin Najeriya da ya taka rawar gani a siyasa da hidimar soja tun daga shekarun 1980s.

Sanata David Mark, sabon shugaban ADC na kasa
David Mark ya fara zama gwamna a zamanin mulkin soja Hoto: @SenDavidMark
Source: Twitter

Legit, ta binciko kadan daga cikin tarihin rayuwarsa da tasirinsa a siyasar Najeriya ta cikin wannan rahoto.

Wanene David Mark, sabon shugaban ADC?

Politicians Data ta wallafa cewa Sanata David Alechenu Bonaventure Mark na daga cikin fitattun ‘yan Najeriya da suka haɗa gogewa a fagen soja da kuma siyasa.

Kara karanta wannan

Haɗaka: Atiku, El Rufai da jiga jigai sun hallara domin ƙaddamar da jam'iyyar ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An haife shi a ranar 8 ga Afrilu, 1948, a Otukpo, jihar Benue, inda a nan ya yi karatunsa na firamare da sakandare.

Daga baya ya shiga makarantar horar da sojoji ta NDA, inda ya kware a fannin sadarwa.

Ya kuma yi karatu a Ingila inda ya samu digiri a fannin injiniyan sadarwa, wato “Telecommunications Engineering" a turance.

Ayyuka da mukaman da David Mark ya rike

A matsayinsa na soja, David Mark ya yi aiki a sassa daban-daban na rundunar sojin Najeriya.

Ya rike mukamai masu daraja, ciki har da kwamandan rundunar sadarwa ta soji da kuma shugaban kamfanin sadarwa na gwamnati, NITEL.

Haɗaka adawa ta amince da shuga ADC
Yadda David Mark zai tallafa wa ADC Hoton: AbdulRasheeth Shehu
Source: Facebook

Ya kuma kasance Ministan sadarwa a karkashin mulkin soja, kuma ana yi masa kallon wanda ba ya saurara wa a harkar gudanar da aiki.

David Mark ya taba gwamnan Neja

A shekarar 1984, lokacin mulkin soja na Janar Muhammadu Buhari, David Mark ya zama gwamnan jihar Neja, yana daga cikin matasa sojojin da aka bai wa mukamin gwamna a wancan lokaci.

Kara karanta wannan

ADC: Haɗakar Atiku ta fara ƙarfi, tsohon shugaban Majalisar Dattawa ya fice daga PDP

Bayan janyewar mulkin soja, David Mark ya shiga siyasa kai tsaye, inda a 1999, ya zama Sanata mai wakiltar Binuwai ta Kudu.

Ya ci gaba da sanun nasara a kan kujerar har ma tsawon shekara da shekaru a jere daga 1999 har zuwa 2019.

David Mark ya yi shugabancin majalisa

Daga shekarar a 2007 zuwa ta 2015, Sanata David Mark ya rike mukamin shugaban majalisar dattawan Najeriya.

Wannnan ta sa ya zama shi ne shugaban majalisar dattawa da ya fi kowa dadewa yana rike da mukamin.

An san shi da kwarewar sassautawa da sulhu a siyasa, wanda hakan ya sa ya kasance mai karɓuwa a wurare daban-daban.

David Mark ya zama shugaban ADC

A ranar Laraba, 2 ga watan Yuli, 2025, Ralph Nwosu, tsohon shugaban jam'iyyar hamayya ta ADC ya tabbatar da cewa shi da jagorancin jam'iyyar.

An dauki matakin ne domin bayar da dama ga Mark ya zama shugaban riko na jam'iyyar a matakin kasa bayan ya fice daga PDP.

Manyan yan adawa da suka hada da Nasiru El-Rufa'i, Atiku Abubakar, Peter Obi, Abubakar Malami SAN da sauransu sun yanke shawarar cure wa wuri guda.

Kara karanta wannan

ADC: Atiku ya fara kokarin jawo jagorori zuwa tafiyar fatattakar APC a 2027

Ana sa ran sauran jagororin siyasa za su shiga ADC a karkashin David domin kai su ga nasara a babban zaben 2027 da ke tunkaro yan Najeriya.

David Mark ya fice daga PDP

A wani labarin, mun ruwaito cewa tsohon shugaban majalisar dattawa, Sanata David Mark, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP da ya hidimtawa tun daga kafuwarta a 1998.

David Mark ya bayyana cewa ya yanke wannan muhimmin mataki ne bayan doguwar tattaunawa da manyan abokan shawara na siyasa duba da irin rikice-rikicen da suka dabaibaye ta.

A wata wasiƙa ta murabus da ya aika wa shugabancin PDP a jihar Binuwai, ya ce rashin warware rikicin shugabancin jam’iyyar na daga cikin abubuwan da suka tilasta masa ficewa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng