Peter Obi Ya Mika wa 'Yan Adawa Bukatar Takara bayan Samun Sarauta a Pantami
- Peter Obi ya gabatar da bukatar mulki na wa’adi guda ga gamayyar ‘yan adawa da ke shirye-shiryen babban zaben 2027
- Yunusa Tanko ya ce Peter Obi na da kwarin gwiwar cewa a shekara hudu a fadar Aso Rock za a iya sauya Najeriya gaba ɗaya
- Magoya bayansa sun ce 'dan takaran na LP ya samu sarauta a jihar Gombe saboda ayyukansa na jin ƙai da inganta rayuwa
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya gabatar yin wa’adin shekara huɗu ga gamayyar ‘yan adawa.
Shugaban ƙungiyar Obidient Movement Worldwide, Dr Yunusa Tanko, ne ya bayyana hakan a ranar Talata yayin da ake karrama Obi da kambun “Sarkin Maska” a unguwar Pantami, Gombe.

Kara karanta wannan
APC ta yi martani mai zafi bayan Atiku, El Rufa'i da Peter Obi sun yi hadaka a ADC

Source: Twitter
Punch ta rahoto Tanko ya ce Obi ya miƙa tayin ne ga manyan jagororin gamayyar da suka haɗa da Atiku Abubakar, Nasir El-Rufai da David Mark, kuma suna da fata za a amince da shirin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Peter Obi ya ce shekara 4 sun ishe shi
Tanko ya jaddada cewa Peter Obi ba ya buƙatar fiye da shekara huɗu don ceto Najeriya daga matsalolinta, yana mai cewa hakan na nuna tsantsar ƙwazo da niyyar alheri.
Ya ce Obi ya tabbatar cewa ko da yake tsarin mulki bai tanadi wa’adi guda ba, amma ya yi alkawarin ba zai zarce fiye da shekara huɗu ba idan ya samu mulki.
A cewarsa, gyaran wutar lantarki kaɗai zai haifar da sauyi a fannin kasuwanci da rayuwar yau da kullum.
Gamayyar adawa ta karɓi bukatar Peter Obi
Yunusa Tanko ya tabbatar da cewa sun gabatar da tayin mulkin wa’adi guda na Obi ga gamayyar 'yan adawa, kuma suna sa ran za a duba lamarin da kyau.
A cewarsa, Obi ya na wakiltar sabon salo na shugabanci mai ma’ana wanda ke da hangen nesa da kyakkyawar makoma ga ƙasar.

Source: Twitter
An ba Obi Sarkin Maskan Pantami
The Cable ta rahoto cewa Obi ya karɓi sarauta a unguwar Pantami, lamarin da Tanko ya bayyana a matsayin wata babbar nasara da ke nuna karɓuwarsa a Arewa.
Ya ce Obi bai cika karɓar sarauta ba, amma wannan ta musamman ce daga al’ummar da ta fara yabonsa bisa ayyukan jin ƙai da ya gudanar.
Tanko ya ce Obi ya kafa rijiyoyi a yankin da ba su da ruwa, ya tallafa wa makarantu, ya gina bayan gida a makarantun Almajirai da kuma taimaka wa matasa da sana’o’i.
Ya ƙara da cewa irin waɗannan ayyuka ne ke sauya tunanin jama’a game da Obi a Arewacin Najeriya, musamman gabanin zaɓen 2027.
Sakataren 'yan adawa na ADC ya yi bayani
A wani rahoton, kun ji cewa sakataren hadakar 'yan adawa da suka zabi jam'iyyar ADC, Rauf Aregbesola ya yi bayani.
Tsohon gwamnan Osun ya bayyana cewa za su mayar da hankali kan inganta ilimi da samar da sana'o'i a kasar nan.
Aregbesola ya kara da cewa za su yi tafiya mai tsafta, inda za a ba matasa da mata damar shiga cikin sabuwar tafiyar ta su.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
