Aregbesola: Tsohon Gwamna Ya Rikide daga Aminin Tinubu Ya Koma Sakataren Haɗaka

Aregbesola: Tsohon Gwamna Ya Rikide daga Aminin Tinubu Ya Koma Sakataren Haɗaka

Abuja - Rauf Aregbesola, fitaccen ɗan siyasar Najeriya ne da ya rikiɗe daga zama babban na hannun-daman Shugaba Bola Tinubu zuwa sakataren riko na ƙasa na jam'iyyar ADC.

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

ADC ita ce jam'iyyar da ƙungiyar hadakar 'yan adawa, karkashin Atiku Abubakar ta amince da ita don kalubalantar Tinubu da jam'iyyar APC a zaɓen 2027.

Duk da kyakkyawar alakarsa da Tinubu a baya, yanzu Aregbesola ya zama sakataren jam'iyyar adawa ta ADC
Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya gana da Shugaba Bola Tinubu. Hoto: @raufaregbesola
Source: Twitter

Asalin dangantakar siyasar Aregbesola da Tinubu

A wannan rahoton, Legit Hausa ta yi bayani dalla dalla kan tsohuwar alakalar Aregbesola da Tinubu da yadda ta rikide zuwa adawa mai tsanani.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aregbesola, wanda aka haifa a ranar 25 ga Mayu, 1957, a Ilesa, jihar Osun ya fara siyasa ne ƙarƙashin jagorancin Tinubu a Legas, a cewar bayanai daga WikiPedia.

Bayan dawowar Najeriya zuwa mulkin dimokuradiyya a 1999, Aregbesola ya kasance jigo a jam'iyyar AD, wadda Sanata Bola Tinubu ke jagoranta a lokacin, kuma ya zama gwamnan Legas a shekarar.

Kara karanta wannan

2027: Dalilai 4 da ke iya sa Tinubu ya rike Kashim Shettima a matsayin mataimaki

Aregbesola ya kasance daraktan kwamitin yakin neman zaben Bola Tinubu (BATCO), wanda ya jagoranci nasarar zaben Tinubu a 1999.

Ya yi irin wannan aiki tare da kungiyar Independent Campaign, inda ya tabbatar da sake zaɓen Tinubu karo na biyu a matsayin gwamnan Legas.

Kwamishinan ayyuka a karkashin Tinubu

Bayan rantsar da Tinubu a matsayin gwamnan jihar Legas, ya naɗa Aregbesola matsayin kwamishinan ayyuka da kadarori, wanda ya haɗa da kula da kamfanin ayyukan jama'a da hukumar lantarki ta jihar.

Aregbesola ya haifar da babban tsarin da ya zama tushen ci gaban ababen more rayuwa da faɗaɗa ayyukan da aka gani a Legas har ma bayan wa'adin mulkin Tinubu guda biyu.

Takarar Aregbesola na neman gwamnan Osun

Bayan wa'adin mulkin Tinubu a matsayin gwamnan jihar Legas ya kare, Aregbesola ya tsaya takarar gwamnan Osun a karkashin jam'iyyar AC a zaɓen Afrilun 2007.

Aregbesola ya gamu da kalubale daga gwamnatin jihar mai ci na hana cikar burinsa, ciki har da yunkurin soke ƙaddamar da Oranmiyan, ƙungiyar yakin neman zaɓensa.

Kara karanta wannan

A ƙarshe, Atiku, El Rufai da Obi sun haɗe kansu, sun zabi jam'iyyar doke Tinubu a 2027

The Nation ta rahoto cewa a ranar 16 ga Mayu, 2005, aka kashe babban mai daukar nauyin yakin neman zaɓen Aregbesola, Alhaji Sulaimon Hassan-Olajoku, a Gbongan.

Shi kansa, Aregbesola ya tsallake rijiya da baya a hare-haren kisan kai a Ilesha a 2005 da kuma a ranar Osogbo Oroki a 2006.

A karshe dai, Aregbesola ya zama gwamnan Osun daga 2010 zuwa 2018, yayin da aiwatar da ayyukan ci gaba a karkashin jam'iyyar APC, wadda Tinubu ya taimaka wajen kafa ta a 2013.

Idan za a tuna, Aregbesola ya yi ta faman shari'a kafin ya samu damar shiga ofis.

Karshen dangantakar Aregbesola da Tinubu

Dangantakar Aregbesola da Tinubu, wanda aka taɓa bayyana cewa ta tabarbare a lokacin zaɓen 2023, musamman saboda adawar Aregbesola ga kudurin Gboyega Oyetola na yin wa'adi na biyu a matsayin gwamnan Osun.

Ƙungiyar Omoluabi ta Aregbesola ba ta marawa ɗan takarar jam’iyyarsu baya ba, lamarin da ya sa Oyetola ya sha kaye a hannun Ademola Adeleke na jam’iyyar PDP, inji rahoton This Day.

Kafin zaɓen, Aregbesola wanda a wancan lokacin ya ke rike da mukamin ministan harkokin cikin gida, ya caccaki Tinubu a wani jawabinsa.

Kara karanta wannan

ADC: Atiku ya fara kokarin jawo jagorori zuwa tafiyar fatattakar APC a 2027

Yayin da yake jawabi ga magoya bayansa a Ijebu-Jesa, Aregbesola ya ce ya amince da ɗan takarar da Tinubu ya zaɓa a matsayin magajinsa a 2018 ne saboda an yi yarjejeniya cewa zai ci gaba da aiwatar da manufofin da ya kafa. Sai dai ya ce Oyetola ya karya yarjejeniyar.

A cewarsa, irin hukuncin da Tinubu da tawagarsa suka yi wa tsohon gwamnan Legas, Akinwunmi Ambode, shi ne za a yi wa Oyetola, domin "shi ma ya kauce daga tsare-tsaren da aka shimfiɗa."

Waɗannan kalaman, a cewar masana siyasa da dama, sun zama mafarin gaba da Tinubu, kuma alamu ne da ke nuna cewa tsofaffin abokan siyasar ba za su sake aiki tare ba.

Rauf Aregbesola ya karbi mukamin sakataren jam'iyyar adawa ta ADC, ya sha alwashin gina ta
Tsohon gwamnan Osun, kuma tsohon ministan Najeriya, Rauf Aregbesola. Hoto: @raufaregbesola
Source: Facebook

Bayan ya yi gwamna, Muhammadu Buhari ya zabe shi a matsayin ministan harkokin gida.

Ko a lokacin ya na minista tsakanin 2019 da 2023, an zargi tsohon gwamnan na Osun da yi wa APC zagon-kasa, har hakan ya jawo PDP ta karbi mulki.

Aregbesola ya zama sakataren kasa na ADC

A watan Mayu 2025, Atiku Abubakar, tsohon Mataimakin shugaban kasa kuma jigo a jam'iyyar PDP, ya ziyarci Aregbesola a Ilesa, wanda ya haifar da ce-ce-ku-ce, a cewar rahoton Legit Hausa.

Kara karanta wannan

2027: Sakataren hadakar ADC ya yi wa 'yan Najeriya bayanin fara aiki

Ziyarar, wadda tun farko aka bayyana a matsayin ziyarar ban girma a lokacin nadin sarautar Owa Obokun na Ijesaland, daga baya an tabbatar da cewa ta haɗa da tattaunawar haɗakar siyasa.

A ranar 1 ga Yuli, 2025, aka sanar da naɗa Aregbesola matsayin sakataren riko na ADC na ƙasa, tare da tsohon shugaban majalisar dattawa David Mark a matsayin shugaban riko da Bolaji Abdullahi a matsayin kakakin yaɗa labarai.

Ƙungiyar haɗakar 'yan adawa, ciki har da manyan 'yan siyasa irin su Peter Obi da Nasir El-Rufai, sun kuduri aniyar amfani da ADC domin cire Tinubu daga mulki a 2027.

Abin da Aregbesola ya faɗa na karɓar mukamin

Tun da fari, mun ruwaito cewa, tsohon gwamnan jihar Osun, Rauf Aregbesola, ya karɓi matsayin sakataren rikon ƙwarya na jam’iyyar haɗin gwiwar adawa, watau ADC.

A jawabinsa, Aregbesola ya sha alwashin sake gina jam’iyya mai ma’ana da tsari, wadda za ta tsaya kan gaskiya da kishin al’umma yayin da ake tunkarar 2027.

Tsohon ministan harkokin cikin gida a gwamnatin Muhammadu Buhari ya ce dole ne jam’iyyun siyasa su wuce matakin neman mulki kawai.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com