2027: Sakataren Hadakar ADC Ya Yi wa 'Yan Najeriya Bayanin Fara Aiki

2027: Sakataren Hadakar ADC Ya Yi wa 'Yan Najeriya Bayanin Fara Aiki

  • Tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola ya karɓi mukamin sakataren rikon ƙwarya na jam’iyyar hadakar adawa ta ADC
  • Rauf Aregbesola ya sha alwashin gina jam’iyya mai ma’ana a siyasa da dogaro da tsari da kishin al’ummar Najeriya
  • Tsohon ministan shugaba Muhammadu Buhari ya ce jam’iyyun siyasa ba za su zama wajen cika burin kai wa ga mulki kawai ba

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Tsohon ministan cikin gida na Najeriya kuma tsohon gwamnan Osun, Rauf Aregbesola, ya karɓi sabon muƙami a matsayin sakataren rikon ƙwarya na jam’iyyar ADC.

Hakan na zuwa ne bayan sanar da cewa ADC za ta zama dandalin kawancen jam’iyyun adawa kafin zaɓen 2027.

David Mark da Rauf Aregbesola da za su jagoranci hadaka a ADC
David Mark da Rauf Aregbesola da za su jagoranci hadaka a ADC. Hoto: Nasir El-Rufa'i
Source: Twitter

A cikin wata sanarwa da Nasir El-Rufa'i ya ya fitar a X, Aregbesola ya bayyana godiyarsa ga shugabancin jam’iyyar bisa amincewa da ba shi sakatare.

Kara karanta wannan

APC ta yi martani mai zafi bayan Atiku, El Rufa'i da Peter Obi sun yi hadaka a ADC

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta nuna cewa Aregbesola ya ce jam’iyya na taka rawa wajen kare muradun jama’a, ba wai kawai a matsayin hanyar samun mulki ba.

Aregbesola ya fadi tsarin da ADC za ta bi

Aregbesola ya ce siyasa a Najeriya ta fara kauce wa hanyar da ya kamata ta bi, inda jam’iyyun siyasa ke zama matattarar burin mutane ba tare da wani tsari ko manufa ba.

A cewar sa:

“Jam’iyyar siyasa ba wata hanya ba ce ta neman iko kawai ko cika burin kashin kai ba.
"Jam’iyya ita ce kafa ta gaskiya wacce ke da tsari, akida, da kishin jama’ar da ta ke yi wa hidima.”

Ya kara da cewa jam’iyyar ADC da za su gina za ta kasance mai kishin gaskiya, da dabbaka adalci, demokuradiyya, da kuma kare rayuwar al’umma har ma bayan kammala zaɓe.

Rauf Aregbesola ya ce za a yi adalci a ADC

Aregbesola ya yi alkawarin cewa karkashin jagorancinsa, za a gina jam’iyyar da ke cike da adalci da gaskiya cikin tafiyar da harkokin ta daga matakin mazaba har zuwa ƙasa baki ɗaya.

Kara karanta wannan

Sabon shugaban APC ya ragargaji Atiku da sauran masu hadaka a 2027

Ya ce za a tabbatar da cewa mata, matasa, da ƙungiyoyin da ke buƙatar wakilci za su samu wurin faɗin albarkacin bakinsu da samun madafun iko.

Bugu da ƙari, Aregbesola ya ce za su dauki kyawawan darussa daga ƙasashen duniya kamar Afirka ta Kudu, Sweden da Kenya domin gina tsarin jam’iyyar da ya dace da yanayin Najeriya.

Sakataren ADC ya ce za su ba matasa dama a jam'iyyarsu.
Sakataren ADC ya ce za su ba matasa dama a jam'iyyarsu.. Hoto: Rauf Aregbesola
Source: UGC

Me ADC za ta mayar da hankali a kai?

A cewar Aregbesola, jam’iyyar ADC ba za ta tsaya kan surutu kawai ba, za ta ɗauki matakai kai tsaye wajen farfaɗo da makarantun gwamnati, inganta tsaro da samar da ayyukan yi.

A ƙarshe, ya bukaci hadin kai da goyon bayan mambobin jam’iyyar da sauran ‘yan Najeriya wajen wannan sabon yunƙuri na sake fasalin siyasa a ƙasar.

APC ta yi wa ADC martani kan hadaka

A wani rahoton, kun ji cewa mai magana da yawun jam'iyyar APC, Bala Ibrahim ya yi martani bayan 'yan adawa sun zabi ADC.

Bala Ibrahim ya ce hadakar su Atiku Abubakar, Peter Obi da su Nasir El-Rufa'i ba za ta hana Bola Tinubu nasara ba.

Haka zalika ya yi martani wa Sule Lamido da David Mark da suka ce Bola Tinubu ya gaza tabuka komai a cikin shekara biyu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng