2027: Atiku, Sule Lamido da Jiga Jigan PDP Sun Shiga Ganawar Gaggawa a Abuja

2027: Atiku, Sule Lamido da Jiga Jigan PDP Sun Shiga Ganawar Gaggawa a Abuja

  • Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da sauran jiga-jigan PDP sun fara ganawar sirri a birnin Abuja a yau Talata
  • Ganawar da ake yi a otal din Transcorp Hilton na duba yiwuwar ficewa gaba daya daga PDP ko yin kawancen zabe daga ciki
  • Rahotanni sun nuna za a yi amfani da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasa tare da David Mark a matsayin shugaban rikon kwarya

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar na ganawar sirri da wasu jiga-jigan PDP a yau Talata 1 ga watan Yulin 2025.

Atiku na ganawar da tsohon shugaban majalisar dattawa, David Mark, da tsohon gwamnan jihar Jigawa, Sule Lamido da ake alaƙanta haka da shirin haɗaka a zaben 2027.

Sule Lamido da Atiku suna wata ganawa a Abuja
Atiku, Sule Lamido da manyan PDP suna ganawa a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

2027: Atiku, Sule Lamido na ganawa a Abuja

Kara karanta wannan

Dantata: Dangote ya karbi tawagar gwamnatin Kano da Jigawa a Madina

Rahoton Punch ya ce sauran sun hada da manyan jiga-jigan jam’iyyar PDP wanda yanzu haka ake taron a Abuja a yau Talata 1 ga watan Yulin 2025.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan ganawar ta musamman da ake yi a wani bangare ne na tuntuba kafin sanar da sabon dandalin siyasa da za a dauru a kai.

Ana sa ran taron na da alaƙa da hadaka domin kalubalantar shugaba Bola Tinubu a zaben 2027 duba da yadda ake ta korafi kan gwamnati mai mulki a yanzu.

2027: Sauran wadanda suka halarci taron a Abuja

Baya ga Atiku da Lamido, sauran shugabannin PDP da suka halarci ganawar sun hada da tsohon shugaban PDP na kasa, Prince Uche Secondus, da tsofaffin gwamnoni.

Daga cikin tsofaffin gwamnonin akwai Aminu Tambuwal (Sokoto), Liyel Imoke (Cross River), Babangida Aliyu (Niger), da Sam Egwu (Ebonyi).

Ana ganawar sirri a Abuja kan shirin haɗaka
Atiku da jiga-jigan PDP suna ganawar sirri a Abuja. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

An yi hasashen musabbabin ganawar a Abuja

Majiyoyi daga wurin taron sun tabbatar cewa ganawar da David Mark ke jagoranta tana mayar da hankali kan yanke shawarar shiga cikakken sabon kawance ko ci gaba da zama a PDP tare da hadin gwiwa.

Kara karanta wannan

"Ba dan Allah ba ne," An gano abin da ke tilastawa gwamnonin PDP sauya sheƙa zuwa APC

Rahotannin sun bayyana cewa an zabi jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasa, kuma an nada Sanata Mark a matsayin shugaban rikon kwarya.

Sauran jiga-jigan PDP da suka halarta sun hada da Sanata Ben Obi, tsohuwar shugabar mata ta PDP Josephine Anenih, Vanguard ta ruwaito.

Sai kuma tsohon sakataren shirye-shirye na kasa Sanata Austin Akobundu, tsohon mai magana da yawun jam’iyyar, Kola Ologbondiyan, da tsohon shugaban matasa na kasa, Abdullahi Maibasira da sauransu.

Atiku zai koma jami'a bayan ritaya a siyasa

Mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya bayyana abin da zai yi bayan ya bar siyasa a rayuwarsa saboda irin sha'awa da yake da shi a bangaren ilimi.

Atiku ya ce zai koma jami’a bayan ritaya daga siyasa, yana mai bayyana sha’awarsa ga ilimi da haɓaka ɗan Adam saboda muhimmancin wannan bangare.

Tsohon dan takarar PDP ya bayyana haka ne yayin bikin yaye ɗalibai a makarantar Pacesetters Abuja, inda ya jaddada cewa ilimi mabuɗin ci gaban ƙasa ne da kuma al'umma baki daya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.