'Shirin Ɗaukar Kwankwaso a matsayin Abokin Takarar Tinubu a 2027 Ya Ƙara Karfi'

'Shirin Ɗaukar Kwankwaso a matsayin Abokin Takarar Tinubu a 2027 Ya Ƙara Karfi'

  • Kakakin NNPP na ƙasa, Ladipo Johnson ya bayyana cewa ƴan APC na son Rabiu Kwankwaso ya zama abokin takarar Bola Tinubu
  • Johnson ya ce jiga-jigan APC sun tuntuɓe shi, suna rokon ya shawo kan Kwankwaso idan an masa tayin mataimakin shugaban ƙasa a 2027
  • Wannan na zuwa ne bayan Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus daga matsayin shugaban APC na ƙasa a ranar Juma'a da ta shige

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Abuja - Mai magana da yawun jam’iyyar NNPP, Ladipo Johnson ya ce raɗe-raɗin da ke yawo cewa Rabiu Musa Kwankwaso na iya zama abokin takarar Shugaba Bola Tinubu a 2027 ba abin mamaki ba ne.

Johnson ya ce NNPP a shirye take ta yi haɗaka wacce za ta yi daidai da manufofinta na samar da daidaito da ci gaban al'ummar Najeriya.

Kara karanta wannan

Kwankwaso zai koma APC bayan Ganduje ya yi murabus? Shugaban NNPP na Kano ya yi bayani

Jagoran NNPP na ƙasa, Rabiu Musa Kwankwaso.
NNPP ta ce an fara tuntubarta kan batun ɗaukar Kwankwaso abokin takarar Tinubu Hoto: @KwankwasoRM
Source: Facebook

Kakakin NNPP ya bayyana haka ne a ranar Litinin a hirar da aka yi da shi a cikin shirin The Morning Brief na tashar Channels TV.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Kwankwaso zai amince ya haɗe da Tinubu?

Ya ce Kwankwaso, wanda ya yi takarar shugaban ƙasa a inuwar NNPP a zaɓen 2023, ƙofarsa bude take ga kowace haɗaka da ta yi daidai da akidunsa da manufofinsa.

Johnson ya ce:

"Ba cin mutunci ba ne a ba shi tayin mataimakin shugaban ƙasa, ko zai amince ko ba zai amince ba, wannan wata magana ce daban.
“Tun daga 2013 ko 2014 nake tare da Kwankwaso, kuma kullum batun ra’ayoyi da akidu ne, waɗanda kake mu’amala da su za su goyi bayan waɗannan ra’ayoyi su tabbata.
"Eh, akwai jita-jita a yanzu haka, amma hakan zai iya faruwa domin bayan zaɓen 2023 mun bayyana cewa mun buɗe ƙofa domin tattaunawa da kowa muddin zai taimaka a cigaban ƙasar nan.”

Kara karanta wannan

'Abin da ya sa APC ke ƙoƙarin jawo Kwankwaso ya haɗe da Tinubu kafin zaɓen 2027'

Shirin jawo Kwankwaso zuwa APC ya yi ƙarfi

Ladipo Johnson ya ƙara da cewa wasu daga cikin mambobin jam’iyyar APC sun tuntube shi kan yiwuwar haɗin gwiwa tsakanin Kwankwaso da Shugaba Tinubu.

“Wasu daga cikin ƴan APC sun kira ni suna cewa, ‘idan aka yi masa tayin, da fatan za ka ƙarfafa masa gwiwa ya amince.’ Amma idan batu ne na jam'iyya, to wannan daban.”

Wannan maganar tasa na zuwa ne a daidai lokacin da ake cigaba da ce-ce-ku-ce bayan taron masu ruwa da tsaki na APC da aka yi a Gombe, The Cable ta rahoto.

Kwankwaso tare da Bola Tinubu a fadar shugaban ƙasa.
'Yan APC sun fara tuntubar na kusa da Kwankwaso domin shawo kansa Hoto: @SaifullahiHon
Source: Twitter

A taron dai wasu daga cikin masu jawabi ciki har da Ganduje sun nuna goyon bayansu ga Tinubu ya tsaya takara karo na biyu, amma ba tare da ambaton mataimakinsa, Kashim Shettima ba.

Bayan murabus ɗin Abdullahi Umar Ganduje daga kujerar shugaban APC na ƙasa a ranar Juma’a, rahotanni sun danganta hakan da wani shiri da ake yi na shigar Kwankwaso jam’iyyar mai mulki.

Kara karanta wannan

Bayan Ganduje, APC ta budewa Kwankwaso kofar sauya sheka da aiki da Bola Tinubu

APC ta ce za ta karbi Kwankwaso hannu biyu

A wani labarin, kun ji cewa jam'iyyar APC ta buɗe kofa ga tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso idan yana da niyar dawowa cikinta.

Mai magana da yawun APC na ƙasa, Felix Morka ya bayyana cewa ƙofarsu a buɗe take ga duk wanda ke sha'awar shigowa cikin jam'iyyar ciki har da Kwankwaso.

Morka ya ƙara da cewa APC za ta ci gaba da karɓar mutane daga kowane sashe na ƙasa, domin ƙarfafa jam’iyyar da kuma aiwatar da manufofinta.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262