ADC: Hadakar su Atiku Ta Tsayar da Jam'iyyar Fafatawa da Tinubu a 2027

ADC: Hadakar su Atiku Ta Tsayar da Jam'iyyar Fafatawa da Tinubu a 2027

  • Bayan watanni na tattaunawa da rashin jituwa kan wacce jam’iyya za a yi amfani da ita don fatattakar APC daga mulki, a karshe an cimma matsaya
  • Rahotanni sun tabbatar da cewa hadakar manyan ‘yan adawa a Najeriya ta amince da amfani da jam’iyyar adawa ta ADC gabanin zabe mai zuwa
  • Wannan ya biyo tabbatar da cewa jam'iyyar ta cika dukkanin wasu bukatu da jiga-jigan adawa ke da shi da zai taimaka wajen cimma manufarsu

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar hadakar jam’iyyun adawa za ta zabi jam’iyyar ADC a hukumance ranar Laraba a matsayin dandalinta wajen kalubalantarsake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

Masu ruwa da tsaki cikin wannan al’amari sun ce mafi yawan shugabannin hadakar sun kai ga yanke shawarar zabar ADC bayan an tattauna.

Kara karanta wannan

2027: APC ta fadi yadda jihar Sakkwato kadai ta isa kai Tinubu ga nasara a Arewa

Ana shirin zaben ADC don yakar APC
Hadakar su Atiku na shirin sanar da jam'iyyarta Hoto: @Omoluabi_sq
Source: Twitter

Daily Trust ta wallafa cewa an dauki matakin ne saboda tsoron cewa jam’iyyar da hadakar ke kafa wa, ADA, ba za ta samu rijista daga Hukumar INEC a kan lokaci gabanin 2027 ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Hadakar Atiku: An gaza cimma matsaya da SDP

Trust radio ta ruwaito cewa mafi yawan masu ruwa da tsaki cikin hadakar sun amince da shiga ADC bayan tattaunawa da SDP ta kasa cimma matsaya.

Da farko ADC ba ta da tasiri a harkokin siyasa na kasa, amma yanzu ta zama zakaran gwajin dafi yayin da jiga-jigan yan adawa ke ganin za ta taimaka wajen yakar APC.

Muhimman ‘yan siyasa kamar tsohon Mataimakin Shugaba, Atiku Abubakar Peter Obi da tsohon gwamnan Jihar Kaduna, Nasir El-Rufai ne suka kaddamar da hadakar a ranar 20 ga Maris, 2025.

Hadakar su Atiku na neman mafita

Sai dai batun zaɓin dandalin siyasa ya dade yana bata wa hadakar lokaci, musamman ganin yadda SDP ta rika bayar da matsalolin rashin hadin kai.

Kara karanta wannan

'Babu hadaka da Atiku,' Peter Obi ya ce zai yi takara a 2027, zai yi wa'adi 1 kawai

Daya daga cikin hadakar ya shaidawa jaridar cewa a cikin Mayu, sun gano cewa ADC ta fi cancanta da zama dandalin da za a hadu domin tunkarar zabe mai zuwa.

Shugaban kasa, Bola Tinubu
Ana sa ran amfani da ADC wajen korar Tinubu daga mulki Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Ya ce:

“Jam’iyyar ta cika dukkannin bukatun hadakar. Shugabanni sun fayyace irin abubuwan da suke nema a wani dandalin siyasa, kuma ADC ta cika wadannan sharudda.”

Amma, ba da jimawa ba bayan wannan bayani, wasu cikin manyan ‘yan hadakar sun nuna rashin jin dadinsu, inda suka ce har yanzu ana tattaunawa a kan dunguma cikin ADC.

A watan Yuni, an samu rahotannin cewa hadakar ta mika takarda ga INEC don yin rijistar ADA a matsayin sabuwar jam'iyyar siyasa, kuma hukumar ta tabbatar da karbar wasikar.

Manyan yan siyasa za su koma ADC

A wani labarin, mun ruwaito cewa Atiku Abubakar, Peter Obi da Mallam Nasir El-Rufai sun cimma matsaya kan kafa kawance domin kalubalantar jam’iyyar APC a zaben 2027.

Domin aiwatar da wannan kuduri, sun amince da jam’iyyar ADC a matsayin dandalin siyasa da za su yi amfani da shi wajen hada karfi da karfe da sauran ‘yan adawa a Najeriya. bv

Baya ga tsohon dan takarar shugaban kasa Atiku, Obi da tsohon gwamna El-Rufa'i, har ila yau akwai wasu muhimman shugabanni da masu ruwa da ke cikin hadakar.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng