Rigimar APC: Ganduje Ya Yi Murabus daga Kujerarsa Ta Shugabancin Jam'iyya
- Rahotanni sun ce Abdullahi Ganduje ya yi murabus daga shugabancin jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya bayan shekaru biyu a ofis
- An ce za a maye gurbinsa da wani mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa har zuwa lokacin babban taron jam’iyya da za a yi a Disamba
- Wannan matakin ya biyo bayan matsin lamba daga yankin Arewa ta Tsakiya da kuma rikice-rikicen cikin gida da ke kara ƙaruwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Bisa ga dukan alamu rigimar da ke cikin jam'iyyar APC a Najeriya na neman rikidewa wanda ake zargin ya kawo karshen jagorancin Abdullahi Ganduje.
An tabbatar da cewa shugaban jam'iyyar APC ta kasa a Najeriya, Dr. Abdullahi Umar Ganduje ya yi murabus.

Source: Facebook
Majiyoyi sun shaida wa Daily Nigerian cewa shugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje, zai mika takardar murabus dinsa a ranar Juma’a.

Kara karanta wannan
'Murabus ɗin ya fi masa alheri': Jigon APC ya faɗi wulaƙanci da aka shiryawa Ganduje
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Yadda aka taso Ganduje a gaba kan shugabanci
Za a iya tunawa, an naɗa Ganduje a watan Agustan 2023 bayan murabus din Abdullahi Adamu daga kujerar shugabancin jam’iyyar mai mulki.
Tsohon gwamnan Kano ya karɓi muƙamin ne wata uku bayan barin kujerar gwamnan jihar bayan jam'iyyar NNPP ta kwace ragamar jagorancinta.
Tun daga lokacin, wasu jiga-jigan Arewa ta Tsakiya ke neman a maido da kujerar shugaban jam’iyyar zuwa yankinsu na asali.

Source: Facebook
An yi hasashen wanda zai maye gurbin Ganduje
An tabbatar da cewa za a maye gurbin Ganduje da wani mataimakin shugaban jam’iyya na ƙasa kafin taron Disamba.
Dr. Ganduje ya ce dalilin murabus dinsa na da alaƙa lafiyarsa, yana mai cewa yana bukatar mayar da hankali kan lafiyarsa.
Duk da cewa wasikar murabus dinsa ta bayyana haka, wasu majiyoyi da ke da masaniya sun ce rikicin siyasa a cikin jam’iyyar na iya taimakawa wajen yanke shawarar sauka daga mukamin.
Ana danganta zargin almundahana da kudi da murabus dinsa, inda wasu 'yan jam’iyya ke zargin ofishinsa da sanya “bukatu masu yawa na kudi” da suka haifar da korafi.
An yi hasashen dalilin murabus na Ganduje
Wasu na zargin matakin yana da nufin rage ƙorafe-ƙorafe daga Arewa ta Tsakiya da kuma adawa daga cikin jam’iyyar, cewar rahoton Premium Times.
Majiyoyi sun ce an lallashi Ganduje wanda ɗan asalin Kano da ya yi murabus yayin da jam’iyya ke tsara dabarun siyasa na zaɓen shekarar 2027 da ke tafe.
Legit Hausa ta tattauna da ɗan APC
Wani dan APC a Gombe, Yahaya Ibrahim ya ce daman kujerar tana da wuyar sha'ani a Najeriya.
Ya ce:
"Mafi yawan masu rike kujerar ba su fiye cikawa da imani ba a karshe ko a tarihin jam'iyyar da sauran jam'iyyu."
Ya ce hakan ya zama kamar al'ada idan ka rike kujerar to ba zaka kare lafiya ba.
Makusancin Ganduje ya bar APC a Kano
Kun ji cewa jam'iyyar APC a jihar Kano ta yi rashi bayan makusancin Abdullahi Ganduje a siyasa, Mustapha Bakwana ya bar cikinta.

Kara karanta wannan
Bayan hasashe da dama, an gano 'dalilin' murabus din Ganduje daga shugabancin APC
Bakwana ya sauya sheƙa daga APC zuwa tafiyar Kwankwasiyya a jihar inda hakan ke nuna cewa ya yi watsi da mukaminsa a ofishin mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin.
'Dan siyasar ya zargi jam'iyyar da nuna halin ko-in-kula gare su da mutanensu duk da irin wahalar da su ka yi wa Abdullahi Umar Ganduje a APC.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
