Wike da Fubara Sun Sasanta Watanni da Dakatar da Zababbun Shugabannin Ribas

Wike da Fubara Sun Sasanta Watanni da Dakatar da Zababbun Shugabannin Ribas

  • Bola Ahmed Tinubu ya yi nasarar kawo karshen takaddamar da ke tsakanin Ministan Abuja, Nyesom Wike da gwamnan Ribas, Siminalayi Fubara
  • An cimma yarjejeniya a tsakanin shugabannin biyu a wani taro da shugaban kasa ya kira, inda aka fitar da sharuddan sasanta wa da ciyar da Ribas gaba
  • Daya daga cikin sharuddan yarjejeniyar shi ne dawo da Fubara kan kujerarsa bayan dakatarwar da aka yi masa tun a watan Maris

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Ministan birnin tarayya (FCT), Nyesom Wike, da gwamnan da aka dakatar na Ribas, Siminalayi Fubara, sun amince da daina rikici da sake jaddada zaman lafiya a jihar.

Wannan mataki ya biyo bayan wani taro da Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya kira da dare a ranar Alhamis a Abuja domin shawo kan rikicin siyasar jihar.

Kara karanta wannan

An samu karin masu son a sauya Kashim, kungiyar APC na son Tinubu ya dauko Dogara

An yi tattaunawa tsakanin Wike da Fubara a Abuja
Tinubu ya kira Wike da Fubara domin sasanta su Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa Wike ya tabbatar da dawo da zaman lafiya a jihar Ribas, inda ya bayyana cewa sun cimma matsaya da Fubara da kuma 'yan majalisar dokoki na jihar.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An sasanta tsakanin Wike da Fubara

Peoples Gazette ta wallafa cewa a taron, an bukaci bangarorin biyu su tsara hanyoyin aiwatar da yarjejeniyar da aka cimma.

Daya daga cikin sharuddan sulhun shi ne mayar da Siminalayi Fubara a matsayin gwamnan jihar Ribas, wanda aka dakatar a watan Maris da ta gabata.

Dakatarwar Gwamna Fubara ta janyo ce-ce-ku-ce sosai, musamman bayan da aka nada wani jami’in soja domin tafiyar da harkokin mulki a jihar mai arzikin man fetur.

Yadda aka caccaki Tinubu kan Ribas

Wasu sun zargi Shugaba Tinubu da karya tsarin mulkin kasa, inda suka bayyana cewa daukar irin wannan mataki ya kara dagula siyasar jihar Ribas.

Sai dai bayan taron sulhun, Wike ya ce shi da Fubara da kuma 'yan majalisa sun daidaita, kuma za su ci gaba da aiki tare domin zaman lafiya da cigaban jihar.

Kara karanta wannan

Rikici ya kare: Tinubu ya gana da Fubara, Wike da 'yan majalisar Rivers a Aso Villa

Ministan Abuja, Nyesom Wike
Wike ya tabbatar da cewa an yi sulhi da Fubara Hoto: Nyesom Ezenwo Wike
Source: Facebook

A kalamansa:

"Mun sasanta. Ni da Gwamna Fubara da kuma 'yan majalisa mun cimma matsaya. Rikicin ya kare."

Rikicin tsakanin Nyesom Wike da Fubara ya samo asali ne daga sabani kan iko da jagoranci a jihar Ribas, wanda ya rikide zuwa rikici da ya kai ga rabuwar kai a majalisar dokoki.

Wannan ya kara dagula al'amura, yayin da jagorin biyu suka rika musayar yawu a kan mulkin jihar Ribas.

Tinubu ya gana da Wike da Fubara

A wani labarin, mun wallafa cewa Shugaban Bola Tinubu ya kammala sasanta rikicin siyasa tsakanin Ministan Babban Birnin Tarayya, Nyesom Wike, da Gwamnan Ribas Siminalayi Fubara.

Wannan sulhu ya biyo bayan wata ganawa ta musamman da shugaban ya jagoranta a daren jiya Alhamis a fadar Villa da ke Abuja, inda ya haɗa bangarorin da rikicin ya shafa domin sasanci.

Alamomi sun nuna cewa an cimma matsaya tsakanin ɓangarorin biyu, kuma ana sa ran zaman lafiya zai tabbata gaba ɗaya a jihar, wanda zai bayar da damar mayar da Fubara kujerarsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng