Ajiye Shettima a 2027: Kungiyar Sanata Barau Ta Rikida zuwa 'Tinubu Barau'
- Sanata Barau Jibrin ya karɓi shugabanni da mambobin kungiyar matasa ta Tinubu/Barau Youth Movement a ofishinsa da ke Majalisar Tarayya
- Shugaban kungiyar, Abdullahi A.C, ya jagoranci tawagar zuwa birnin Abuja domin nuna goyon baya ga jam’iyyar APC da ci gaban Najeriya
- Sanata Barau ya nuna godiya tare da bukatar a sauya sunan kungiyar zuwa Tinubu/Barau domin lura da ayyukan shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya karɓi bakuncin shugabanni da mambobin kungiyar matasa ta Barau Youth Movement Organization.
Yayin ganawa da kungiyar, an sauya sunanta zuwa Tinubu/Barau Youth Movement Organization, a ofishinsa da ke Majalisar Tarayya Abuja.

Source: Twitter
Legit ta gano haka ne a cikin wani sako da Sanata Barau Jibrin da ya wallafa a shafinsa na Facebook a ranar Jumu'a.

Kara karanta wannan
Shekarar Hijira: Sarkin Musulmi ya yi magana kan rashin tsaro, yakin Iran da Isra'ila
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ziyarar, wadda shugaban kungiyar Abdullahi A.C ya jagoranta, ta kasance ce domin sake tabbatar da goyon bayan kungiyar ga jam’iyyar APC da kuma ci gaban Najeriya baki ɗaya.
Sanata Barau ya yaba da irin ƙoƙarin da kungiyar ke yi na wayar da kan matasa da kuma ƙarfafa turbar ci gaba a matakin ƙasa da na jihar Kano.
Barau ya saka sunan Tinubu a kungiyar shi
A yayin ganawar, Sanata Barau ya nuna godiya ga matasan bisa jajircewarsu wajen tallata muradun jam’iyyar APC.
Mataimakin shugaban majalisar ya kuma yaba wa matasan bisa jajircewarsu wajen cusa kyakkyawar manufa ta ci gaba a zukatan al’umma.
Ya kuma buƙaci su sauya sunan kungiyar zuwa Tinubu/Barau Youth Movement domin haka zai fi dacewa da irin rawar da Shugaba Bola Ahmed Tinubu ke takawa a yanzu.
Sanata Barau ya ce:
“Shugaba Tinubu ya amince da duk wasu bukatu da muka gabatar masa domin ci gaban jihar Kano da yankinmu,”

Kara karanta wannan
An samu karin masu son a sauya Kashim, kungiyar APC na son Tinubu ya dauko Dogara
Ya bayyana cewa wannan goyon baya ne ya haifar da kirkirar Hukumar Raya Arewa Maso Yamma (NWDC), gina jami’o’in tarayya da kuma wasu muhimman ayyuka da ke tafe.
Ziyarar ta zo ne a daidai lokacin da ake ta rade-radin cewa ana tunanin maye gurbin Mataimakin Shugaban Kasa, Kashim Shettima da Sanata Barau Jibrin a zaben 2027.
Duk da cewa ba a tabbatar da wannan ba, kuma Sanata Barau ya fito da kan shi ya ce yanzu ba lokacin siyasa ba ne.

Source: Facebook
Tun a kwanakin baya dai aka fara rade radin yiwuwar sauya mataimakin shugaban kasa, Sanata Kashim Shettima a zaben 2027 duk da cewa babu maganar daga Bola Tinubu ko APC kai tsaye.
Matsayar Barau kan takara da Tinubu
A wani rahoton, kun ji cewa mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin ya yi magana kan zama mataimakin Bola Tinubu.
Barau Jibrin ya ce yana biyayya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu kuma duk abin da ya fada zai masa biyayya a kai.
Tun bayan fara rade radin ajiye Kashim Shettima ake cigaba da magana kan wanda Tinubu zai zaba a takarar 2027 a Arewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng