Ana Wata ga Wata: Sabuwar Rigima ta Kunno a Jam'iyyar PDP

Ana Wata ga Wata: Sabuwar Rigima ta Kunno a Jam'iyyar PDP

  • Shugaban kwamitin amintattu na PDP, Sanata Adolphus Wabara, ya soki matakin da Umar Iliya Damagum ya ɗauka
  • Sanata Adolphus Wabara ya bayyana cewa dawo da Samuel Anyanwu da Damagum ya yi, ya saɓawa ƙa'ida
  • Hakazalika ya haƙiƙance cewa taron NEC na PDP da aka shirya a ranar 30 ga watan Yuni yana nan babu fashi

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Kwamitin amintattu na PDP (BoT), ya caccaki muƙaddashin shugaban jam'iyyar na ƙasa, Umar Iliya Damagum.

Kwamitin na BoT ya nuna rashin amincewa da sanarwar da ke bayyana Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyyar na ƙasa.

Wabara ya caccaki shugaban PDP na kasa
Rigima ta kunno a jam'iyyar PDP Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Twitter

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata sanarwa da shugaban BoT, Adolphus Wabara, ya fitar a ranar Alhamis, 26 ga watan Yunin 2025, cewar rahoton jaridar The Cable.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wabara ya saɓa da Shugaban jam'iyyar PDP

Kara karanta wannan

PDP ta sake yin babban rashi: Tsohon shugabanta ya riga mu gidan gaskiya

Adolphus Wabara ya kuma bayyana rashin goyon bayansa ga jinkirta taron kwamitin zartarwa na ƙasa (NEC) da aka tsara za a gudanar a ranar 30 ga watan Yuni, rahoton jaridar Vanguard ya tabbatar.

Wabara ya ce sanarwar da shugaban riƙo na jam’iyyar, Damagum, ya yi shi kaɗai na mayar da Anyanwu a matsayin sakataren PDP da kuma soke taron NEC, babban amfani ne da ofishi ba bisa ƙa’ida ba.

"Kwamitin amintattu, domin kare kundin tsarin mulkin PDP, na bayyanawa a fili cewa waɗannan matakai da muƙaddashin da shugaban riƙo na ƙasa ya dauka, ba su da inganci kuma sun saɓawa tsarin mulkin jam’iyya wanda aka aka yi wa gyara a shekarar 2017."

- Sanata Adolphus Wabara

'Taron PDP-NEC zai gudana' - Wabara

Wabara ya bayyana cewa a yayin taron da aka yi a ranar 27 ga watan Mayu, an tsaida ranar 30 ga watan Yuni don gudanar da taron NEC, kuma dole ne kowane sashe na jam'iyyar ya yarda da hakan.

"Saboda haka, kasancewar wannan shawara ta fito daga NEC, ba wata ƙungiya ko mutum guda da ke da ikon soke ko ɗage wannan taro karo na 100 da aka tsara a ranar Litinin, 30 ga watan Yuni, 2025."

Kara karanta wannan

Nasir El Rufai ya sake dura kan Tinubu, ya yi wa ministocinsa saukale

“Wannan batu ba ya cikin ikon shugaban riƙo na ƙasa ya ɗauki matsaya da zai soke abin da NEC ta yanke."
“Irin wannan mataki ya nuna raini da wulaƙanci ga ikon kundin tsarin mulki na NEC da kuma abin da jam’iyya ta yanke."
“Bugu da kari, sanarwar da ke kokarin mayar da Sanata Samuel Anyanwu a matsayin sakataren jam’iyya na ƙasa ba ta da tushe kuma ta saɓawa kundin tsarin mulkin PDP, da kuma hukuncin kotun koli da kuma matsayar da NEC ta ɗauka."

- Sanata Adolphus Wabara

Wabara ya soki Umar Iliya Damagum
Wabara ya nuna gamsuwa da matakan da Damagum ya dauka Hoto: @OfficialPDPNig
Source: Facebook

Shugabannin PDP sun gana da INEC

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugabannin jam'iyyar PDP sun gana da hukumar zaɓe mai zaman kanta ta ƙasa (INEC).

Shugabannin na PDP sun je hedkwatar INEC ne domin nemo hanyar warware rikicin da ya addabi jam'iyyar.

A yayin ziyarar wacce ta ƙunshi manyan ƙusoshin jam'iyyar, sun gana da shugaban INEC na ƙasa, Farfesa Mahmoud Yakubu.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng