2027: 'Yan Adawa Sun Nemi Tayar da Rigima da Ɗan Majalisar Tarayya Ya Sauya Sheƙa zuwa APC
- Ɗan Majalisar Wakilan Tarayya daga jihar Enugu, Hon. Chimaobi Atu ya sauya sheƙa daga LP zuwa APC mai mulki yau Alhamis
- Kakakin Majalisar Wakilai, Rt. Hon Tajudeen Abbas ne ya sanar da hakan da yake karanta wasiƙar sauya sheƙar Hon. Atu a zaman Majalisa
- A cewarsa, rikicin cikin gida da ya hana LP motsi ne ya tilasta masa sauya sheka zuwa APC domin wakiltar al'ummarsa yadda ya kamata
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan Majalisar Wakilai ta Tarayya, Hon. Chimaobi Atu, ya sauya sheka daga jam’iyyar LP zuwa APC mai mulki a hukumance.
Shugaban Majalisar Wakilai, Rt. Hon. Tajudeen Abbas, ne ya bayyana sauya shekar Atu a zauren majalisar yayin zamansu na ranar Alhamis.

Source: Facebook
Jaridar The Cable ta tattaro cewa Hon. Atu na wakiltar mazabar Enugu ta Arewa/Kudu a majalisar wakilan tarayya ta 10.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa ɗan Majalisar ya bar LP zuwa APC?
A wasiƙar da ɗan majalisar ya miƙa wa Tajudeen Abbas, ya ce ya ɗauki wannan matakin ne saboda rigingimun cikin gida da suka hana LP kataɓus.
Hon. Atu ya ce ba zai iya ci gaba da zama a jam'iyyar da ke fama da rikice-rikice na shugabanci ba, domin hakan yana taɓa wakilcin da yake wa al'ummarsa.
Ɗan majalisar ya ƙarƙare da cewa waɗannan dalilai da ma wasu, sune suka tilasta masa sauya sheka daga LP zuwa APC, inda yake tunanin zai fi samun nutsuwa.
Ɓangaren ƴan adawa sun nemi tayar da ƙura
Sai dai mai tsawatarwa na marasa rinjaye a Majalisar, Hon. Ali Isa ya yi fatali da sauya sheƙar Hon, Atu, yana mai rokon a ayyana kujerarsa a matsayin wacce babu kowa a kai.
Kakakin Majalisa, Rt. Hon Tajudeen Abbas ya karɓi ƙorafin shugaban marasa rinjaye, amma ya ƙi cika bukatar da ya nema ta ƙwace kujerar Atu.
A ranar Talata, wasu ‘yan majalisar biyu, Peter Akpanke da Paul Nnamchi, suka sanar da sauya sheka zuwa APC.
APC na ta ƙara ƙarfi a Majalisar Wakilai
Hon. Akpanke na wakiltar mazabar Obanliku/Obudu/Bekwara ta jihar Cross River, wanda aka zaɓe shi a karkashin inuwar PDP a zaɓen 2023.
Shi kuma Hon. Nnamchi, shi ne mamba mai wakiltar mazabar Enugu gabas/Isi-Uzo, kuma ɗan jam’iyyar LP ne kafin sauya shekar zuwa APC, rahoton The Nation.

Source: Twitter
Haka kuma, Hon. Joseph Nwobashi, wanda ke wakiltar mazabar Ezza Arewa/Ishielu ta Jihar Ebonyi, ya sauya sheka daga jam’iyyar APGA zuwa APC a hukumance.
Kwana biyu bayan haka, Hon. Atu ya bi sahunsu, ya mika takardar sauya shekarsu daga LP zuwa APC ga shugaban Majalisar Wakilai yau Alhamis.
Umar Sani, ɗaya daga cikin matasan da suka koma APC tare da ɗan Majalisar Bakori/Ɗanja, ya ce babu abin da ya rage a jam'iyyun adawa.
Da yake zantawa da wakilin Legit Hausa, Umar ya ce duk wani shugaba da ya san abin da yake tunkara musamman zaɓen 2027, ba zai zauna a PDP ko LP ba.

Kara karanta wannan
2027: Dalillai 5 da ka iya sa Tinubu ya sauya Kashim Shettima a matsayin mataimaki
"Ni ina ganin babu abin da ya rage a LP da PDP face rikici, yau waɗannan su ware su ce, sune shugabanni na haƙiƙa, abin ya yi yawa, ni bana ganin laifin ƴan Majalisar da suke komawa APC."
"Kowa mafitarsa yake dubawa a siyasance, kuma mutane ba jam'iyya suke zaɓa ba yanzu, wanda zai masu aiki, ya taimaki rayuwarsu shi suke dubawa," in ji shi.
Sanatan LP daga jihar Edo ya koma APC
A wani labarin, kun ji cewa sanata mai wakiltar Edo ta Kudu, Sanata Neda Imasuen, ya sanar da ficewarsa daga LP tare da komawa jam'iyyar APC.
Sanatan ya ce rikicin cikin gida da ya addabi LP da kuma ƙoƙarin daidaita siyasarsa ne suka tilasta masa ɗaukar wannan mataki.
A cewarsa, ba haka kurum ya yanke shawarar shiga APC ba sai da ya tattauna da neman shawari daga al'ummar da yake wakilta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

