Kwana 1 bayan Kalaman El Rufai, Sabuwar Jam'iyyar Haɗaka 'ADA' Ta Gamu da Matsala a INEC
- Hukumar INEC ra ce jam'iyyar da haɗakar ƴan adawa suka nemi a yi mata rijista watau ADA ba ta cika sharuɗɗan doka ba
- Mai magana da yawun INEC na ƙasa, Mista Sam Olumekun ne ya bayyana hakan a wata hira da manema labarai ranar Talata a Abuja
- Shugaban INEC, Farfesa Mahmud Yakubu zai gana da jam'iyyun siyasa 19 masu rijista ranar Alhamis, kuma ana sa ran zai yi ƙarin haske kan lamarin
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Hukumar Zaɓe Mai Zaman Kanta (INEC) ta bayyana cewa ADA, wadda ke neman a yi mata rajista a matsayin jam’iyyar siyasa, ba ta cika sharuddan da ake buƙata ba.
Wannan bayani ya fito ne daga bakin kwamishinan INEC kuma shugaban kwamitin yaɗa labarai, Mista Sam Olumekun.

Source: Twitter
Olumekun ya bayyana hakan ne a lokacin wata tattaunawa da manema labarai a Abuja ranar Talata, kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya bayyana cewa INEC ta karɓi takardu da dama na buƙatar kafa jam’iyya, amma babu ɗaya daga cikinsu da ta cika sharuɗɗan da doka ta tanada na yin rijista.
"Gaskiyar magana ita ce muna da takardu da yawa na buƙatar kafa jam’iyya, amma babu ɗayansu da ta cika sharuɗɗan da aka shinfida. Dole ne su fara cika wasu ƙa’idoji kafin a miƙa takardar buƙata” in ji Olumekun.
Wace matsala aka samu wajen rijistar ADA?
Wannan cigaba na zuwa ne bayan jagororin adawa da ke shirin kirkiro ADA sun manta da haɗa kalmar “electoral” a cikin wasikar da suka aikewa shugaban INEC.
A cikin wasikar da ke ɗauke da kwanan wata 19 ga Yuni, an yi kuskuren rubuta "The Chairman, Independent National Commission (INEC), 436, Zambezi Crescent, Maitama, Abuja FCT.”
Wasikar na ɗauke da sa hannun Akin Ricketts, wanda ke matsayin shugaban ADA na riko, da kuma Abdullahi Musa Elayo, sakataren rikon kwarya.

Kara karanta wannan
"Abin da ya sa muke shirin ƙirƙiro jam'iyyar ADA kafin 2027," El Rufai ya yi bayani
Daga cikin fitattun mutane da ake dangantawa da shirin kafa ADA akwai tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar, da tsohon gwamnan Jihar Kaduna Nasir El-Rufai.
Sai kuma tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, tsohon Shugaban Majalisar Dattawa, David Mark, da kuma ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi, rahoton Punch.
INEC ta yi ƙarin haske kan rijistar jam'iyya
Sai dai INEC ta ce babu wata gajeriyar hanyar yin rajistar jam’iyya, dole ne ƙungiyoyin da ke neman zama jam’iyya su bi tsarin da dokar zaɓe ta 2022 da dokokin INEC suka tanada.
Ana sa ran shugaban INEC, Farfesa Mahmood Yakubu, zai gana da shugabannin jam’iyyu 19 da aka riga aka yi wa rajista a ranar Alhamis a hedkwatar hukumar da ke Abuja.

Source: Twitter
Wannan taro wani ɓangare ne na ganawar masu ruwa da tsaki, da suka haɗa da 'yan jarida, kungiyoyin farar hula, da hukumomin tsaro, karkashin jagorancin Farfesa Yakubu.
Mai ba shugaban ƙasa shawara kan harkokin tsaro, Malam Nuhu Ribadu, na cikin mahalarta taron, waɗanda ke zama shugabannin haɗin gwiwa na kwamitin tsaron zaɓe (ICCES).

Kara karanta wannan
ADA: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani game da sabuwar jam'iyyarsu Atiku da El Rufai
Wani babban jami'in INEC ya tabbatar da cewa, Shugaban INEC zai yi bayani kan ADA da sauran batutuwa masu alaka da hakan a taron ranar Alhamis.
El-Rufai ya faɗi dalilin neman rijistar ADA
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai ya ce sun yanke shawarar ƙirƙiro jam'iyya ne saboda gujewa sharrin APC.
El-Rufai ya bayyana cewa gudun tuggun da gwamnati ke shiryawa jam'iyyun adawa wanda ke hana su zaman lafiya ane ya sa suka duba yiwuwarkafa sabuwar jam'iyya.
Ya ce haɗakarsu ta shirya tsaf kuma za ta samu nasara a yunkurinta na kawo karshen mulkin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
