"Mun Shirya," Shugaba Tinubu Ya Yi Maganar Yiwuwar Wike Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC
- Shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya bayyana cewa ba abin da zai hana jam'iyyar APC karɓar Ministan Abuja idan ya shirya sauya sheƙa
- Bola Tinubu ya ce duk da Wike ba ɗan APC ba ne amma jam'iyya mai mulki za ta yi farin ciki idan ya amince zai baro PDP ya dawo cikinta
- Mai girma shugaban ƙasa ya yi wannan furucin ne a wurin kaddamar da sababbin titunan da Wike ya jagoranci yi a babban birnin tarayya Abuja
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Shugaban Ƙasa Bola Ahmed Tinubu, a ranar Laraba, ya bayyana cewa ƙofar APC a buɗe take ga ministan harkokin Abuja, Nyesom Wike a duk lokacin da ya shirya sauya sheƙa
Bola Tinubu ya ce jam'iyyar APC ta shirya karɓar Nyesom Wike hannu bibbiyu a duk lokacin da tsohon gwamnan ya yanke shawarar ficewa daga PDP.

Source: Facebook
Shugaba Tinubu ya kaddamar da ayyuka a Abuja
Vanguard ta tattaro cewa Bola Tinubu ya faɗi haka ne a wurin kaddamar da titin Arterial Road N16 a babban birnin tarayya Abuja.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Titin dai ya taso ne daga Ring Road One (Nnamdi Azikiwe Way) zuwa Arterial Road N20 (Wole Soyinka Road). Tinubu ya buɗe shi tare da wasu hanyoyi a unguwar Katampe, Abuja.
Da yake jawabi a wurin, Shugaba Tinubu ya ce duk da har yanzu Wike ɗan PDP ne amma APC a shirye take ta karɓe shi idan ya zaɓi sauya sheka zuwa cikinta.
APC ta shirya karɓar Wike hannu bibbiyu
Ya ce idan APC ta samu mutum irin Wike, jam’iyyar za ta ci gaba da kasancewa cikin farin ciki, yayin da abokan hamayyarta za su ci gaba da shan azaba da ciwon zuciya.
"Duk da Wike bai shiga APC ba tukuna, ƙofarmu na nan a buɗe, za mu karɓe shi idan ya yanke shawarar sauya sheƙa.

Kara karanta wannan
"Ina sha'awar shiga APC saboda mutum 2," Tsohon hadimin Atiku ya yi barazanar barin PDP
"Da mutane irin sa, farin ciki zai ci gaba da kasancewa tare da mu, su kuma ƴan adawa damuwa za ta musu katutu.
“Nyesom Wike ba ƙaramin mutum ba ne, bai zama ɗan jam’iyyata ba tukuna. Amma ranar da ya sauya ra’ayinsa ya yi rajista da APC za mu tarbe shi hannu biyu, domin za mu more shi."
- In ji Bola Tinubu.

Source: Twitter
Nyesom Wike na ƙwacen filaye a Abuja?
Da yake magana kan aikin da aka kaddamar, Shugaba Tinubu ya ce tuni aka biya mazauna unguwar Gishiri, da aikin titin ya shafa, diyyar filayensu, yana mai cewa ba kwace aka yi masu ba, tahoton The Nation.
Ya ƙara da cewa wannan aikin ba kawai titin kwalta ba ne, wata alama ce da ke nuna ana samun sauyi a ƙarƙashin manufar Renewed Hope Agenda.
Tinubu ya ja kunnen Wike kan masu suka
A wani rahoton, kun ji cewa Shugaba Bola Tinubu ya buƙaci Ministan Abuja, Nyesom Wike da ya yi fatali da masu suka da zagi, kada ya bari su ɗauke masa hankali.

Kara karanta wannan
"Abubuwa sun lalace," Peter Obi ya faɗi hanya 1 da ƴan Najeriya za su ƙifar da Tinubu a 2027
Mai Girma Tinubu ya faɗi haka ne a wurin taron ƙaddamar da ginin cibiyar taron ƙasa da ƙasa, wacce aka canza wa suna a Abuja.
Shugaban ƙasan ya ce gyaran da aka yi wa cibiyar taron wata alama ce da ke nuna yadda gwamnatinsa ta himmatu wajen kawo sauyi mai amfani.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
