2027: Kusa a PDP Ya ba Atiku Shawara, Ya Fadi Abin da zai Koya wajen Tinubu
- Babban ƙusa a PDP, Segun Showunmi, ya yi muhimmin kira ga Atiku Abubakar kan shirin da yake yi na kafa haɗakar ƴan adawa
- Segun Showunmi ya buƙaci tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya tsaya ya yi koyi da Shugaba Bola kan yadda ake kafa haɗaka
- Jigon na jam'iyyar PDP ya bayyana cewa duk da ƙaunar da yake yi wa Atiku, bai tare da shi a shirin da yane yi na samar da haɗaka
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Jigon jam’iyyar PDP, Segun Sowunmi, ya ba da shawara ga tsohon ubangidansa, Alhaji Atiku Abubakar.
Segun Showunmi ya shawarci Atiku Abubakar, da ya koyi yadda ake haɗa haɗaka daga wajen Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Tsohon mai magana da kwamitin yaƙin neman zaɓen Atiku a 2023, ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da aka yi da shi a tashar TVC a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A ƙoƙarinsa na ƙwace mulki daga hannun Shugaba Tinubu a 2027, Atiku ya na jagorantar wani yunƙurin ƴan siyasar hamayya domin samun haɗakar jam’iyyu kafin babban zaɓe mai zuwa.
Yayin da jam’iyyar PDP ke fama da rikicin shugabanci, tsohon mataimakin shugaban ƙasan na neman kafa wani dandalin siyasa domin ƙwace mulki daga hannun jam’iyyar APC da ke kan mulki.
Jigon PDP ya raba gari da Atiku kan haɗaka
Sai dai Showunmi, wanda ya daɗe yana tare da Atiku, bai goyi bayan wannan matakin nasa ba.
Ya bayyana cewa maimakon kafa ƙawance da wata sabuwar jam’iyya, kamata ya yi Atiku ya jawo ƴan adawa cikin jam’iyyar PDP.
Segun Showunmi ya kuma buƙaci Atiku da ya koyi dabarar kafa ƙawance daga wajen Shugaba Tinubu.
“Na kan gayawa mutane cewa, mutane na soyayya da zuciyarsu, ni ina ƙaunar Atiku da ƙasusuwa na. Amma ba zan iya taimaka masa idan ya yi kuskure da kansa ba."

Kara karanta wannan
"Ina sha'awar shiga APC saboda mutum 2," Tsohon hadimin Atiku ya yi barazanar barin PDP
"Ba zai yiwu ka yi mataimakin shugaban ƙasa a karkashin PDP sau biyu tare da Obasanjo, sannan kuma ka sake samun takarar shugaban ƙasa sau biyu a ƙarƙashin jam’iyyar, sai kuma yanzu ka ce kana neman wata sabuwar jam'iyya."
"Idan kana son ƙawance, me ya sa ba za ka haɗe su a cikin jam’iyyar ka ba?”
- Segun Showunmi

Source: Twitter
Wace shawara aka Atiku Abubakar?
Tsohon ɗan takarar gwamnan na PDP a jihar Ogun ya shawarci tsohon mataimakin shugaban ƙasar da ya yi koyi daga Tinubu kan yadda ake gina ƙawance ba tare da barin jam’iyyar da mutum ke ciki ba.
“Ka kalli abokin hamayyarka, kuma abokin ka. Kun fara tare. Ko da za ka ce yana gina kawance, shin ba yana haɗe su ba ne a jam’iyyarsa?"
- Segun Showunmi
Showunmi ya ziyarci Shugaba Bola Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa babban ƙusa a jam'iyyar PDP, Segun Showunmi ya sanya labule da Shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Segun Showunmi ya bayyana cewa ya ziyarci Shugaba Tinubu a gidansa da ke Legas don taya shi murnar bukukuwan babbat Sallah.
Jigon na PDP mai adawa ya ƙara da cewa sun yi tattaunawa mai inganci a yayin ziyarar da ya kai wa shugaban ƙasan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
