"Ina Sha'awar Shiga APC saboda Mutum 2," Tsohon Hadimin Atiku Ya Yi Barazanar Barin PDP
- Segun Showunmi ya bayyana cewa idan abubuwa suka ci gaba da lalacewa a jam'iyyar PDP, to zai tattara kayansa ya koma APC
- Tsohon kakakin kwamitin kamfen PDP yana sha'awar shiga APC saboda yadda Bola Tinubu da Muhammadu Buhari suka zama tsayayyu
- Ya ce saɓanin sauran manyan ƴan siyasa, Tinubu da Buhari sun tsaya ɓangare ɗaya ba tare da yawan sauya jam'iyyar siyasa ba
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon hadimin Atiku Abubakar, Segun Showunmi ya ce da yiwuwar ya sauya sheƙa daga jam'iyyar PDP zuwa APC mai mulkin Najeriya.
Mista Showunmi, tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku Abubakar a zaɓen 2023, ya ce zai bar PDP idan ya fahimci shugabannin jam'iyyar ba za su gyara ta ba.

Source: Facebook
Jigon PDP ya bayyan haka ne a wata hira da aka yi da shi a cikin shirin 'Your View' na kafar watsa labarai ta TVC ranar Talata, 10 ga watan Yuni, 2025.
Kalaman Segun Showunmi na zuwa ne kwanaki ƙalilan bayan ya gana da shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke jihar Legas.
Tsohon hadimin Atiku na shirin barin PDP
Tsohon mai magana da yawun kwamitin kamfen Atiku a 2023 ya ce zai fice daga PDP idan shugabannin jam’iyyar suka nace wajen lalata ta.
Showunmi ya ce yana jin sha’awar shiga APC saboda yadda shugaban kasa Bola Tinubu da wanda ya gabace shi, Muhammadu Buhari, suka zama tsayayyun shugabanni.
A cewarsa:
"Bari ku ji, na sha faɗa kuma zan maimaita a yau, idan har na bar PDP to babu shakka APC zan shiga, kun san me yasa? Saboda ginshikan APC biyu, Bola Tinubu da Muhammadu Buhari tsayayyun mutane ne.
"Tinubu da Buhari ba su tsalle-tsallen sauya jam'iyyun siyasa, sun tsayu a tsagi ɗaya tun 1998."
Sowunmi ya faɗi alaƙarsa da kakakin APC na ƙasa

Kara karanta wannan
"Ba laifin Fubara ba ne," Yan Majalisa sun yi magana kan yiwuwar 'gwamna' ya koma APC
Showunmi ya ƙara da cewa idan har zai shiga APC, zai fara tuntubar abokinsa Felix Morka, mai magana da yawun APC na ƙasa, domin ya ji kundin tsarin jam'iyyar.
"Idan zan shiga APC, zan fara da ziyartar abokina Felix Morka. Zan zauna da shi, in nemi kundin tsarin mulki na jam’iyyar, in karanta shi," in ji shi.

Source: Facebook
Jigon PDP ya soki shirin haɗakar Atiku
Haka kuma, Showunmi ya nuna rashin amincewarsa da yunƙurin kafa haɗakar siyasa da Atiku ke jagoranta, yana mai cewa hakan ya kawo ruɗani a PDP.
A rahoton Vanguard, Showunmi ya ce:
“Ɗaya daga cikin abubuwan da ke damuna game da wannan magana ta haɗaka da ake yi ita ce ban ga dalilin da zai sa ‘yan siyasa na kirki su rika neman kafa sabon tsarin siyasa ba.
Ya kuma bayyana cewa ya shafe fiye da shekaru 27 a cikin PDP kuma ba zai ci gaba da jure rashin tabbas a jam’iyyar ba.
Sowunmi ya ɗora Tinubu a kan Obi da Atiku
A baya, kun ji cewa Segun Sowunmi ya yi ikirarin cewa shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu ya fi duka manyan masu adawa da shi a ƙasar nan dabara.

Kara karanta wannan
Tsohon na kusa da Atiku ya fadi fannin da Tinubu ya yi wa abokan hamayyarsa zarra
A cewar jigon na PDP, Shugaɓa Tinubu ya iya mu'amala da mutane yadda zai jawo ra'ayinsu, saɓanin abokan hamayyarsa irinsu Peter Obi.
Bugu da ƙari, ya yi bayani kan ziyarar da ya kaiwa Tinubu a Legas, yana mai cewa bai ci amanar alaƙarsa da tsohon mataimakin shugaban ƙasa, Atiku Abubakar ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
