An Kaɗa Hantar Shugaba Tinubu kan Matsalar Tsaro, da Yiwuwar a Kifar da APC a Zaben 2027

An Kaɗa Hantar Shugaba Tinubu kan Matsalar Tsaro, da Yiwuwar a Kifar da APC a Zaben 2027

  • Fitaccen dattijo daga Arewa kuma mai sharhi kan harkokin ƙasa, Alhaji Dabo Sambo ya gargaɗi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu
  • Dabo Sambo ya bukaci Tinubu ya gaggauta kawo ƙarshen matsalar tsaro musamman a Arewa matukar yana son tazarce a 2027
  • Ya ce matsalar tsaron da ta addabi Najeriya ita ta jawo ƙarancin abinci, faɗuwar darajar Naira da tsadar kayayyakin amfanin yau da kullum

Dattijon Arewa kuma mai sharhi kan harkokin ƙasa, Alhaji Dabo Sambo ya gargaɗi shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu kan matsalar tsaro da ta addabi Najeriya.

Alhaji Dabo ya buƙaci Tinubu ya ɗauki matakan magance duk wani nau'i na matsalar tsaro da ta'addanci musamman a Arewa ko kuma mutane su juya masa baya a zaɓen 2027.

Shugaba Tinubu na fuskantar matsala gabanin 2027.
Alhaji Dabo Sambo ya gargaɗi Tinubu game da matsalar tsaro da karancin abinci Hoto: @aonanuga1956
Source: Facebook

Jigon na Arewa ya bayyana haka ne a wani taron manema labarai da ya gudanar yau Alhamis, kamar yadda Daily Trust ta tattaro.

Sambo ya bukaci Tinubu ya dawo da tsaro

Kara karanta wannan

"Tsarin Tinubu ya zo da alheri," An ji abin da ya jawo man fetur ya yi araha a Najeriya

Dabo Sambo ya jaddada cewa rashin tsaro ita ce babbar barazana da ke addabar Najeriya, inda rayuka da dukiyoyi ke salwanta a kullum.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce dawo da zaman lafiya da kwanciyar hankali shi ne ainihin aikin kowace gwamnati, kuma gazawa a wannan fanni na iya jawo faduwar gwamnati.

Babu wadatar abinci a Najeriya, kuma jama’a na cikin yunwa,” in ji shi, yana danganta hakan da tasirin rashin tsaro a yankunan Arewa maso Gabas da Arewa maso Yamma.

Matsalar taaro ta hana manoma zuwa gona

Dabo Sambo ya bayyana cewa manoma da dama na gujewa gonakinsu saboda barazanar ‘yan bindiga, garkuwa da mutane, da kuma ayyukan ‘yan ta’adda.

A cewarsa, hakan ne babban abin da ke haddasa ƙarancin amfanin gona da hauhawar farashin kayayyaki a Najeriya, rahoton Leadership.

Ya kuma tabo tasirin rashin tsaro ga tattalin arzikin ƙasa, yana mai nuna cewa hakan ya ƙara jawo faɗuwar Naira, tsadar sufuri da tsadar abinci wanda ke neman ya fi ƙarfin talaka.

An ja kunnen shugaban ƙasa, Bola Tinubu kan matsalar tsaro.
Dattijon Arewa ya ce ƴan Najeriya za su sake zaɓen Tinubu ne kawai idan ya magance matsalolinsu Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Sambo ya yi hasashen faɗuwar Tinubu a 2027

“Ina roƙon Shugaba Tinubu da ya magance matsalar tsaro cikin watanni shida, sannan ya farfado da noma a cikin shekara guda.

Kara karanta wannan

Malamin addini ya yabi Shugaba Tinubu, ya fadi inda ya kerewa Buhari

“Idan Shugaba Tinubu bai magance waɗannan matsaloli ba, tabbas ba zai lashe zaben 2027 ba. Zamanin rabon indomie da gishiri a lokacin kamfen ya wuce.
“Yanzu mutane na bukatar tsaro da abinci. Idan ba a samar da wadannan abubuwa ba, ba za su kada kuri’a ba.”

- Alhaji Dabo Sambo.

Dattijon ya jaddada cewa idan shugaban kasa ya gaza tinkarar tushen matsalolin tsaro da tattalin arziki, to ko magudi ba zai ceto shi daga faduwa a zaɓe ba.

Wani ɗan PDP a Katsina, Abdullahi Sule ya shaida wa Legit Hausa cewa ko a samu zaman lafiya ko kada a samu, alamu sun nuna talakawa sun gaji da wannan gwamnati.

"Kamar yadda ya faɗa ne, ba wadatar abinci, ga yunwa, ba kudi a hannun mutane, kudin ma idan ka samu ba su daraja, ba ɗin ta yi yawa, to da me mutane za su ji?"

Amma a cewar wani malamin makaranta, Aminu Kabir, har yanzu ƴan Arewa ba su hankalta ba, za su iya sake kaɗa wa Tinubu ƙuri'unsu a 2027.

Ya ce a ganinsa mutane za su sake zaɓen APC da zaran an ba su wasu ƴan kuɗaɗe a ranar zaɓe.

Kara karanta wannan

Musulmi sun yi babban rashi, Sarki mai martaba a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya

Fasto Tunde Bakare ya gana da Tinubu

Kuna da labarin, fitaccen malamin kirista, Fasto Tunde Bakare ya ziyarci shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu a gidansa da ke jihar Legas.

Babban malamin ya gana da Shugaba Tinubu kuma sun tattauna kan muhimman batutuwa da suka shafi ƙasa a ranar Laraba, 4 ga watan Yuni, 2025.

Bakare ya kasance tsohon dan takarar mataimakin shugaban kasa, ya yi takara tare da Muhammadu Buhari a zaben 2011 a karkashin inuwar jam’iyyar CPC.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262