Wike Ya Tono Sirrin Gwamnonin PDP, Ya Fadi Alfarmar Tinubu da Suke Nema
- Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya ce shi ne zai jagoranci kamfen Shugaba Bola Tinubu a Ribas a zaben 2027, duk da kasancewarsa dan PDP
- Ya tabbatar da cewa Tinubu zai samu rinjaye a Abuja a 2027, ko da yake jam’iyyar LP ce ta yi nasara a yankin birnin tarayya a zaben 2023
- Wike ya bayyana cewa bai jin tsoron abin da zai faru a PDP, domin ya sanar da shugabannin jam’iyyar kafin ya karɓi mukamin ministan Abuja
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya shaida cewa zai tsaya tsayin daka wajen tallafawa Shugaba Bola Ahmed Tinubu a kokarinsa na neman wa’adi na biyu a 2027.
Hakan na zuwa ne yayin da jam'iyyar PDP ke kokarin dawowa da karfinta a Najeriya, musamman gabanin zaben 2027.

Source: Facebook
Nyesom Wike zai jagoranci kamfen Tinubu a 2027
Wike, wanda har yanzu dan jam’iyyar PDP ne, ya bayyana hakan ne a tattaunawar da aka yi kai tsaye a Channels TV.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wike ya ce kasancewarsa a majalisar zartarwa ta Tinubu ba dalili ba ne da zai sa ya yi watsi da burin PDP, amma ya dage cewa zai jagoranci kamfen din Shugaba Tinubu a jihar sa.
Tinubu zai lashe Abuja a 2027 inji Wike
A tattaunawar, Wike ya yi hasashen cewa Tinubu zai yi nasara a Abuja a zaben 2027, duk da cewa bai samu kashi 10 cikin 100 na kuri’un birnin ba a 2023.
Premium Times ta wallafa cewa Wike ya ce:
“Ba ku sani ba ne cewa a 2023 bai kai kashi 10 cikin 100 Tinubu ya samu ba ne a nan FCT? Amma a 2027 zai yi nasara a nan.”
Wike ya danganta hakan da sauye-sauyen da yake ganin gwamnatin Tinubu za ta kawo a birnin da kewayen shi.

Kara karanta wannan
Wike ya cika baki kan batun korarsa daga PDP, ya kalubalanci jiga jigan jam'iyyar
Wike: 'Gwamnonin PDP sun nemi alfarmar Tinubu'
Game da yiyuwar takunkumi daga jam’iyyarsa, Wike ya ce ya rubuta wasiƙa ga dukkan matakan shugabancin PDP kafin ya karɓi mukamin minista, kuma babu wanda ya nuna adawa da hakan.
Ministan ya ce:
“Na rubuta wa sashen Kudu maso Kudu, gwamna, da shugabannin PDP a matakin ƙasa."
Wike ya kara da cewa wasu gwamnoni ma suna neman a yi wa magoya bayansu alfarma cikin gwamnatin APC da Bola Tinubu ke jagoranta.
Ministan ya ce:
"Su da suke rokon a ba mutanensu mukamai a gwamnatin APC ne suke zargi na da yi wa APC aiki."

Source: Facebook
Wike ya ce ya jima yana ba PDP gudummawa fiye da waɗanda ke ta kiransa ‘dan APC’ yana mai cewa:
“Ba wanda ya isa ya ce ba ni dan PDP ba ne. Wane ne ya bayar da gudummawa fiye da ni?” ya tambaya.
An gargadi Bola Tinubu kan hulda da Wike
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon hadimin shugaba Goodluck Jonathan, Reuben Abati ya gargadi shugaba Bola Tinubu kan huda da Nyesom Wike.
Reuben Abati ya yi zargin cewa Nyesom Wike ya saba juya baya ga mutanen da suka taimaka masa a siyasa.
A karkashin haka Abati ya ce a kwana a tashi watarana Wike zai iya zagin shugaba Bola Tinubu idan aka samu wani dalili.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

