"Shekara 8 Ina matsayin Gwamna amma ban Samu Komai ba," Kalu Ya Tuna Abin da Ya Faru
- Sanata Orji Uzor Kalu ya tuna halin da ya tsinci kansa daga 1999 zuwa 2007, lokacin yana matsayin gwamnan jihar Abia
- Tsohon gwamnan ya ce bai amfana da komai ba sai dai kuɗinsa da ya rika kashewa wajen tafiyar da harkokin gwamnati
- Sanatan ya yi ikirarin cewa yana ɗaya daga cikin manyan waɗanda suka taimaka wa PDP da kuɗi lokacin da aka kafa ta a 1998
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abia - Tsohon gwamnan Abia kuma sanata mai wakiltar Abia ta Arewa, Orji Uzor Kalu, ya yi ikirarin cewa bai tara komai ba lokacin da yake gwamna daga 1999 zuwa 2007.
Sanata Kalu ya ce maimakon ya amfana da wani abu a matsayinsa na gwamna, shi ne ma ya riƙa ƙashe ƙuɗinsa wajen tafiyar da harkokin mulki.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya faɗi haka ne a wata tattaunawa da aka yi da shi a shirin Politics Today na Channels TV a ranar Litinin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Sanata Kalu ya tuna lokacin da yake gwamna
Kalu ya ce siyasa ta haifar masa da babbar asara, inda gwamnatin tarayya ta rufe wasu daga cikin harkokin kasuwancinsa lokacin yana kan mulki.
“Na kashe kudi na lokacin ina gwamna, kamar yadda nake kashe kudi na yanzu da nake Sanata. Ni na riƙa taimakawa jihar Abia da kudi na.
"Ban amfana da komai ba a matsayin gwamna, sai dai asara. Gwamnatin tarayya ta kwace wasu daga cikin kasuwancin da na kafa. Don haka siyasa ba ta kawo min riba ba, sai hadari da asara.”
- Orji Kalu.
Yadda Orji Kalu ya taimaki PDP da Obasanjo
Sanata Kalu ya kara da cewa Allah ya azurta shi da miliyoyin kuɗi tun yana ɗan shekara 24, kuma ya yi ikirarin cewa yana cikin manyan masu ɗaukar nauyin PDP a lokacin da aka kafa ta a 1998.
Ya ce ya bayar da gudummawar sama da Dala miliyan daya ga kwamitin yakin neman zaben tsohon Shugaban Kasa Olusegun Obasanjo, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan
Yadda aka zabga wa Sarki lafiyayyen mari a taron da gwamnan Ondo ya kaddamar da titi
Kalu ya ce:
“Ka tambayi kowanne ɗan PDP, ni na kawo mafi yawan kudin da suka yi amfani da shi a 1998 da 1999. Na ba Shugaba Obasanjo sama da Dala miliyan daya, na ba jam’iyyar PDP fiye da Naira miliyan 500.”

Source: Facebook
Sanata Kalu ya samu saɓani da Obasanjo?
Lokacin da aka tambaye shi ko yana gaba da Obasanjo saboda abin da ya faru da kasuwancinsa, Kalu ya musanta hakan, yana mai cewa Obasanjo mai gidan su ne.
"Ba na fushi da shi, dangina na da kyakkyawar alaƙa da shi, abokinmu ne. Mahaifiyata na girmama shi, marigayi mahaifina ma haka. Har yanzu yana tare da iyalanmu," in ji shi.
Kadan daga rayuwar Kalu
Orji Uzor Kalu ɗan siyasa ne kuma ɗan kasuwa daga jihar Abia da ke kudu maso gabashin Najeriya.
An haife shi a ranar 21 ga watan Afrilu, 1960, kuma ya yi karatunsa a makarantu da dama ciki har da Jami’ar Maiduguri da kuma Jami’ar Harvard ta kasar Amurka.
Tun yana matashi, Kalu ya kasance a harkokin kasuwanci, inda ya kafa kamfanoni da dama da suka a fannin sufuri, gine-gine, da watsa labarai, musamman kamfanin SLOK Group.
Kafin ya shiga siyasa, Kalu ya riga ya tara dukiya mai tarin yawa ta hanyar sana’o’insa. Wannan ne ya ba shi damar shigowa siyasa da ƙarfi, yana ɗaya daga cikin wadanda suka taka rawar gani wajen kafa jam’iyyar PDP a shekarar 1998.
Baya ga siyasa da kasuwanci, Kalu ya sha fuskantar tuhuma da gwamnatoci daban-daban, ciki har da shari’ar cin hanci, amma yana ci gaba da kare kansa da cewa yana fafutukar ganin Najeriya ta gyaru.
Abin da ya sa Tinubu ke samun goyon baya
A wani labarin, kun ji cewa Sanata Orji Kalu ya bayyana cewa Bola Tinubu na kara samun goyon baya a kowace rana ne saboda ayyukan alherin da yake yi.
Tsohon gwamnan cewa APC ba ta damu da wata haɗakar da ƴan adawa ke shirin yi ba, yana mai cewa ba za su iya taɓuka komai ba.
A cewarsa, Shugaba Tinubu da jam'iyyar APC ba za su yi shakkar haɗuwar ƴan adawa a inuwar ɗaya ba gabanin zaɓen 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

