'Ina Yawan Zubar da Hawaye': Wike Ya Faɗi Abin da Ke Sanya Shi Kuka a Rayuwarsa

'Ina Yawan Zubar da Hawaye': Wike Ya Faɗi Abin da Ke Sanya Shi Kuka a Rayuwarsa

  • Ministan Abuja, Nyesom Wike, ya kuma yin magana game da rigimarsa da Gwamna Siminalayi Fubara a Rivers
  • Wike ya ce yana kuka duk lokacin da ya tuna yadda Fubara ya ci amanarsa duk da taimakon da ya yi masa a siyasa
  • Wike ya ce shi ya dauki nauyin Fubara, ya ba shi abinci da goyon baya, amma daga baya ya zama kayan aikin abokan gabansa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

FCT, Abuja - Ministan Babban Birnin Tarayya, Abuja, Nyesom Wike ya tuno irin butulcin da Siminalayi Fubara ya yi masa.

Wike ya ce yana yawan zubar da hawaye idan ya tuna da abin da dakataccen gwamnan Rivers ya yi masa da ya shiga ofis.

Wike ya soki Fubara kan butulci
Wike ya ce butulcin Fubara na sanya shi kuka. Hoto: Sir Siminalayi Fubara.
Source: Facebook

Yadda Wike ke jin zafin 'butulcin' Fubara

Wike ya bayyana hakan ne yayin wani taron manema labarai da aka gudanar a Abuja a ranar Litinin, cewar The Guardian.

Kara karanta wannan

Wike ya cika baki kan batun korarsa daga PDP, ya kalubalanci jiga jigan jam'iyyar

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yayin hirar, Wike ya yi tone-tone game da rikicin siyasa a Jihar Rivers da sabanin da ke tsakaninsa da Fubara da aka dakatar tun watan Maris 2025.

Tsohon gwamnan Rivers ya ce duk lokacin da ya tuno da jawaban Fubara bayan ya hau mulki ya kan zubar da hawaye.

Tsohon gwamnan Jihar Ribas ya kara da cewa yana yawan tambayar kansa ko abubuwan da Fubara ya masa sun cancanta, duba da gudummawar da ya ba shi.

Ministan ya na zargin cewa gwamna Fubara ya yi masa butulci da ya samu mulki.

A cewarsa:

"Idan na yi shiru ni kadai, idan na kunna faifan jawabinsa, abin da ya fada da abin da ya yi mani, sai in yi kuka."
"Wannan mutumin ni na kawo ka, na ba ka abinci, na ba ka komai, sai ka zama kayan aikin abokan gabana don su yaƙe ni."
Wike ya caccaki yan adawa
Wike ya fadi abin da ke damun Amaechi. Hoto: Nyesom Ezenwo Wike.
Source: Facebook

Wike ya tabo batun hadakar yan adawa

Kara karanta wannan

'Cigaban mai haka rijiya,' Buba Galadima ya ce babu abin a yaba a shekaru 2 na Tinubu

A hirar da aka yi da shi, Wike ya kalubalanci masu shirin kawance da ‘yan adawa domin ganin bayan mulkin Tinubu a zaben gaba.

Wike ya zargi tsohon gwamnan Rivers, Rotimi Amaechi da cewa yana da mugun nufi da kuma buri na siyasa da neman mulki.

Hakan bai rasa nasaba da shirye-shiryen yan adawa domin tabbatar da sun kwace mulki a hannun Bola Tinubu a zaben 2027.

Wike ya ce bai yi nadamar goyon bayan APC da Tinubu a zaɓen 2023 da ta gabata ba da kuma bijirewa PDP, cewar rahoton Punch.

"Yanzu suna taruwa, mun gode da ba mu mara baya ga PDP ba; da mun goya musu baya, da ya yi alfahari. Yanzu yana cikin wata kawance.
"Ni ba na son yin surutu da yawa. Sai su hada tawagar su kuma su fara daga gida a Jihar Rivers."

- Cewar Nyesom Wike

Dokar ta-ɓaci: Fubara ya yabawa Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa dakataccen gwamnan Rivers, Siminalayi Fubara ya ce matakin Bola Tinubu na saka dokar ta-baci ya ceci jihar daga rikici da rugujewar lamura.

Kara karanta wannan

Rivers: Fubara ya ba da mamaki da ya sake maganganu kan Tinubu da Wike

Fubara ya bayyana cewa ana bin tsarin sasanci da sulhu domin dawo da zaman lafiya da aiki tsakanin bangarorin gwamnati a jihar.

Sir Siminalayi Fubara ya nuna kwarin guiwar cewa nan ba da jimawa ba mulkin dimokradiyya zai dawo da cikakken tsari a jihar Rivers.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.