Akpabio: Sanata Natasha Ta Saki Sabon Bidiyo kan Yadda Ake 'Wawure Kuɗi' a Majalisa
- Sanata Natasha Akpoti-Uduaghan mai wakiltar Ƙogi ta Tsakiya ta fallasa badaƙalar da ake tafka wa a Majalisar Dattawan Najeriya
- Natasha ta ce ba ta san 'rahoton ayyukan kwamiti' na da wata ma'ana ta daban a Majalisa ba sai ta je gabatar da nata rahoton
- Ta yi zargin cewa shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio na karɓar kuɗi daga kwamitoci lokaci bayan lokaci
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan ta bayyana yadda ake tafka cin hanci da satar dukiyar talakawa a Majalisar Dattawa.
Sanata Natasha ta ce ba ta san mai ake nufi da rahoton ayyukan kwamiti ba sai da ta zama shugabar kwamitin majalisar Dattawa mai kula da abubuwan cikin gida.

Source: Facebook
Natasha, wacce ke takun saƙa da shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio ta faɗi hakan ne a wani faifan bidiyo da wani Chuks Erice ya wallafa a shafin X.

Kara karanta wannan
'Gwamnatinka ta jefa talakawa a masifa,' Kungiyar Yarbawa, Afenifere ta soki Tinubu
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Halin da Sanata Natasha ke ciki a Majalisa
Idan ba ku manta ba Majalisar Dattawa ta dakatar da Natasha na tsawon watanni shida tare da hana ta duk wasu haƙƙoƙinta saboda rashin ɗa'a da karya dokar zama a Majalisa.
Wannan hukunci ya biyo bayan cacar bakin da ta yi da shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Akpabio kan sauya mata kujerar zama.
Bayan haka, Natasha ta fito ta zargi Sanata Akpabio da neman lalata da ita, lamarin da Shugaban Majalisa ya ƙaryata.
Sanata Natasha ta tona baɗakalar da ake yi
A sabon bidiyon da ke yawo a kafafen sada zumunta, Sanata Natasha ta yi zargin cewa kusan duka shugabannin kwamitocin Majalisa na kai wa shugaban Majalisa kudi.
Ta ce bayan ta fara aiki a matsayin shugabar kwamitin kula da kayayyakin cikin gida, an nemi ta kawo rahoton aikinta ba tare da sanin ana nufin kudi ba.
"Watanni uku bayan na kama aiki a matsayin shugabar kwamitin kula da abubuwan cikin gida, na kan halarci tarurruka, a ɗaya daga cikin taron da na je (Akpabio) ya ce da ni sanata ba ki kawo mana rahoton ayyukanku ba."
"Na ce masa ba damuwa a ba ni wasu ƴan kwanaki, daga nan na je na haɗa bayanan ayyukan da kwamitina ya yi, na koma wurinsa, na ce na shirya ba da rahoton ci gaban da aka samu."
"Ya ba ni dama na buɗe kwamfuta ta, na fara bayanai kawai sai ya fashe da dariya, na ce yallabai me na dariya, sai ya tambaye ni, baki gane ma'anar rahoton da nake nufi ba."
- In ji Sanata Natasha.

Source: Facebook
Natasha ta zargi Akpabio da badaƙalar kuɗi
Sanatar ta kara da cewa daga nan ya tura ta zuwa wurin wani sanata da ya jima a Majalisar domin domin ya mata bayanin abin da ake nufi da rahoton ayyukan kwamiti.
"Na je wurin wannan sanata saboda ina girmama abokan aikina, don ya mani bayani, shi ma ya yi dariya, ya ce zan kawo wani abu, na ce ban gane ba, sai ya amsa da cewa kudi.
"Wannan ta faru ne da ni, ban san sauran ba, alamu dai sun nuna Shugaban Majalisar Dattawa na karɓar kudi daga shugabannin kwamitoci lokaci zuwa lokaci," in ji ta.
Ana ba ƴan Majalisa Naira biliyan 1?

Kara karanta wannan
Ambaliya: Sheikh Pantami ya yi magana kan mutuwar mutane sama da 100 a Jihar Neja
A wani labarin, kun ji cewa Majalisar Wakilai ta yi watsi da ikirarin wani jigon APC, wanda ya ce ana ba kowane ɗan Majalisa N1bn na ayyukan mazaɓa.
Mai magana da yawun Majalisar Wakilai, Hon. Akin Rotimi, ya bayyana zargin da ake yadawa a matsayin ƙarya mara tushe ballantana makama.
Ya ce majalisar wakilai ta yi shiru a farkon lamari ne domin ba wa ’yan majalisa damar bayyana gaskiya kai tsaye ga mutanen mazabunsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
