'Duk Mun Koma Mayunwata': Tsohon Minista Ya Fadi abin da ke Jiran Tinubu a 2027
- Rotimi Amaechi ya caccaki gwamnatin Bola Tinubu kan tabarbarewar tsaro da yunwa, yana mai zargin cewa kowa ya koma mayunwaci yanzu
- Tsohon gwamnan na Rivers ya bukaci 'yan adawa da su tashi tsaye domin kawar da Tinubu a 2027, domin dawo da kasar kan tubar kwarai
- Amaechi ya bayyana cewa ikon kawar da gwamnati yana hannun talakawa, inda ya soki yadda wasu ke zaɓe don kabilanci ko kuma addini
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon gwamnan jihar Rivers, Rotimi Amaechi, ya caccaki shugaba Bola Tinubu kan tabarbarewar tsaro, yunwa da talauci da ke ƙara ta'azzara a ƙasar.
Amaechi ya ce talauci da rashin tsaro, sun shafi kowa a kasar inda ya kalubalanci 'yan adawa da su tashi tsaye domin kawar da Tinubu a 2027.

Source: Facebook
"Yunwa ba ta san kabila ko addini ba" - Amaechi
Jaridar Daily Trust ta ruwaito Amaechi, yayin taron tattaunawa da jama'a a bikin murnar cikarsa shekaru 60 a duniya, ya na cewa:
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
“Kowa na jin yunwa yanzu, duk mun zama mayunwata. Idan kai ba ka jin yunwa, to ni ina ji. Idan muka daura damara, za mu iya cire shi daga mulki.
"Dole mu haɗa kai da zuciya ɗaya idan muna son fita daga wannan matsala. Idan 'yan adawa za su shirya shirin ceton ƙasa, to dole mu fifita ƙasar a kan buƙatunmu.”
Ya ƙara da cewa:
"Yunwa ba ta banbanta Musulmi da Kirista, ko Bahaushe da Yarabawa ba. Wannan gwamnati ta ƙara jefa jama'a cikin talauci da laifi."
"Yan Najeriya ke da ikon sauya gwamnati' - Amaechi
Jaridar The Guardian ta rahoto tsohon gwamnan ya ce ikon cire gwamnati da ta gaza cika alkawuranta kan tsaro da tattalin arziki yana hannun talakawa ba 'yan siyasa ba.
A cewar Amaechi:
“Akwai bukatar 'yan Najeriya su fahimci cewa ikon sauke gwamnatin nan na hannunsu. Idan muna son sauyi na gaske, talaka ne ke da ikon kawo shi.”
Ya ce ya ƙi marawa Tinubu baya a 2023 ne saboda ya yi imani da cewa Tinubu ba shi da ƙwarewar jagoranci kasa irin Najeriya.
“Na gaya wa Tinubu a Yola: 'Ba zan goyi bayanka ba; ba zan yi aiki da kai ba'. Kuma ban yi ba. Ban zaɓe shi ba. Iya aiki na duba, ba wai alaka ba."

Source: Facebook
Yadda aka tsare Amaechi a Jamus
Ya soki yadda wasu suka zaɓi gwamnatin Tinubu bisa kabila da addini, yana mai cewa:
“Wasu daga cikinmu sun zaɓe su bisa kabila ko addini. Jahilci da yaɗuwar ƙarya ne ke sa talakawa yin zaɓe mara amfani da kuma jefa mu a halin da muke ciki.
“Yanzu wa zai zo ya fada mana amfanin cire tallafin mai? Su wanene cire tallafin ya amfana? Kowa ya san amsar, wasu azzaluman manya ne kawai ke amfana da shi.”
Amaechi ya ce ya ji kunya da irin yadda aka tsare shi a ƙasar Jamus saboda yana ɗauke da fasfo ɗin Najeriya.
“Na ji kunya sosai. An tsare ni a Jamus na tsawon mintuna 30. Ba don na aikata wani laifi ba. Ni na je duba lafiya ta ne ma. Na nuna musu tikitin jirgi na, amma suka tsare ni, saboda kawai ina ɗauke da koren fasfo."
- Rotimi Amaechi.
"Tinubu zai sake lashe zabe a 2027" - Amaechi
A wani labarin, mun ruwaito cewa, shahararren fasto, Samuel Ojo, ya bayyana cewa ƙoƙarin ‘yan adawa na hana Shugaba Bola Tinubu yin tazarce a zaben 2027 ba zai yi nasara ba.
A cewarsa, nasarar Tinubu a karo na biyu ta tabbata tun da farko, domin Ubangiji ne ya ƙaddara hakan, kuma babu dabara ko haɗin kai da zai hana hakan.
Ojo ya ja kunnen ‘yan adawa da su daina shirin kawar da Tinubu, yana mai cewa har yanzu Ubangiji na da sauran aikin da zai ba shi, kuma akwai manyan ayyuka a gabansa.
Asali: Legit.ng


