'Yadda Za Mu Kwace Mulki daga Hannun Tinubu a 2027,' Atiku, El Rufai Sun Magantu

'Yadda Za Mu Kwace Mulki daga Hannun Tinubu a 2027,' Atiku, El Rufai Sun Magantu

  • Atiku Abubakar da Nasir El-Rufai sun soki shugaban ƙasa Bola Tinubu kan talauci, yunwa da rashin tsaro da ke kara tsananta a Najeriya
  • Atiku ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa 'yan kasa cikin talauci da gangan domin amfani da hakan a matsayin makamin sarrafa siyasa
  • El-Rufai ya ce Najeriya na cikin mafi munin hali tun 1914, yana mai kira ga 'yan Najeriya da su taimaka wajen sauya gwamnati a 2027

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Abuja – Manyan shugabannin adawa; tsohon mataimakin shugaban ƙasa Atiku Abubakar da tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai sun caccaki shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Atiku da El-Rufai sun soki Tinubu kan gazawa wajen dakile yunwa, talauci da rashin tsaro da ke ƙara ta'azzara a Najeriya, inda suka sha alwashin hana shi cin zabe a 2027.

Kara karanta wannan

Matashi ya saya wa Tinubu ragon layya, ya yi wa mamar shugaban kasa mai suna

Atiku da El-Rufai sun yi magana kan kwace mulki daga hannun Tinubu a 2027
Tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai | Shugaba Bola Tinubu | Alhaji Atiku Abubakar. Hoto: @elrufai, @atiku, @officialABAT
Source: Twitter

Atiku ya zargi Tinubu da jefa talauci a Najeriya

Sun bayyana hakan ne a karshen makon jiya yayin wani taron tattaunawa da jama’a da aka gudanar domin bikin cika shekara 60 da haihuwar Rotimi Amaechi, inji rahoton Daily Trust.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

An gudanar da wannan taron ne karkashin taken: “Mayar da talauci makami a matsayin hanyar hana cigaba: Darasi daga Najeriya.”

Atiku, wanda ya tsaya takarar shugaban ƙasa a ƙarƙashin jam’iyyar PDP a 2023, ya zargi gwamnatin Tinubu da jefa mutane cikin talauci da gangan, domin manufa ta siyasa.

“Za ku iya kira na da kowane irin suna, amma ya zama wajibi mu samar da haɗakar da za ta taimaka wajen hana mutanen nan amfani da talauci a matsayin makamin yin mulki."

- Atiku Abubakar.

"Suna amfani da talauci a matsayin makami" - Atiku

Ya kara da cewa gwamnatin Bola Tinubu ta ci amanar jama’a, inda take amfani da halin ƙunci na tattalin arziki don cimma burinta na siyasa.

Kara karanta wannan

2027: Wasu 'yan majalisa sun yi watsi da hadaka, sun goyi bayan tazarcen Tinubu

“Wannan talaucin da muke muke fuskanta yau a Najeriya ba wai kaddara ba ce, wani makami ne da gwamnati ke amfani da shi domin ci gaba da mulki," inji Atiku

Atiku ya kwatanta yadda jihar Kano ke cikin walwala a baya, amma yanzu an wayi gari da dubban mutane na kwana a titi da ƙarkashin gada sakamakon yunwa da rashin tsaro.

Ya bayyana yadda wata hukuma a jihar ta yi ƙoƙarin taimakawa waɗanda ke kwana a titi, amma daga baya gwamnati ta umarce su da su daina yin hakan.

Mallam Nasir El-Rufai ya ce hadakar 'yan adawa za ta kawo karshen mulkin Tinubu a 2027
Tsohon gwamnan Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai | Shugaban kasa, Bola Tinubu. Hoto: @elrufai, @officialABAT
Source: Twitter

El-Rufai ya fadi dabarar kwace mulki daga Tinubu

A nasa bangaren, Mallam Nasir El-Rufai ya ce Najeriya na fuskantar mafi munin rayuwa a karkashin Tinubu tun bayan haɗewarta a shekarar 1914.

“Najeriya na cikin mafi girman matsala tun 1914. Shi ya sa muke kokarin haɗa kai da wasu domin kafa wata gagarumar kawance da za ta dawo da kasar kan turba ta gaskiya."

- Nasir El-Rufai.

Channels TV ta rahoton tsoho gwamnan na Kaduna yana cewa:

“Muna ji muna gani muka kyale 'yan ta'adda, ba na daji ba, 'yan ta'addan birni, hawa mulki ba tare da sanin abin da za su yi da mulkin ba.

Kara karanta wannan

2027: Atiku da manyan 'yan siyasa 7 da suka dauki aniyar raba Tinubu da ofis

El-Rufai ya yi kira ga 'yan Najeriya da su zabi shugabanni masu, ƙwarewa, kishin kasa da jajircewa wajen ceto ƙasar daga halin da take ciki.

LP ta nesanta kanta daga hadakarsu Atiku

A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar LP ta nesanta kanta daga duk wani yunkurin haɗaka da Atiku Abubakar ko wata jam’iyya a yanzu.

Ta fitar da gargaɗi ga ɗan takararta na 2023, Peter Obi, da sauran manyan jiga-jigan jam’iyyar da su guji shiga irin waɗannan haɗaka ba tare da izini ba.

LP ta bayyana cewa halartar Obi wani taron haɗin gwiwa ba tare da amincewar jam’iyya ba raini ne ga shugabancinta da kuma saba ka’idojin jam’iyya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com