2027: Atiku da Manyan 'Yan Siyasa 7 da Suka Dauki Aniyar Raba Tinubu da Ofis
Yayin da ‘yan Najeriya ke fama da hauhawar farashi da matsalolin tattalin arziki, siyasar 2027 ta fara daukar zafi ganin yadda manyan yan siyasa suka fara shirin babban zabe.
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaba Bola Ahmed Tinubu, wanda ke cika shekaru biyu da fara mulkin Najeriya na fuskantar karuwar adawa daga fitattun ‘yan siyasa da ke neman hana APC komawa kujerar shugaban kasa.
Masu sukar gwamnatin na zargin Tinubu da aiwatar da manufofi marasa amfani, gazawa wajen rage radadin tattalin arziki, da kuma kokarin mayar da Najeriya mulkin jam’iyya daya.

Source: Twitter
Jaridar Punch ta ruwaito cewa a yayin da jama’a ke nuna rashin jin dadi da gazawar manufofin gwamnati, wata hadaka ta manyan ‘yan siyasa na kunno kai, da burin kawar da Tinubu daga mulki a 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ana kokarin kawar da gwamnatin Tinubu
A cewar wasu jiga-jigan siyasa, ciki har da tsohon mataimakin shugaban kasa, gwamnati mai ci na kara jefa kasar cikin halin kunci, kamar yadda Atiku Abubakar ya bayyana a shafinsa na X.
Ba Atiku ne kadai ke da irin wannan ra'ayi ba, kamar yadda za a gani a jerin wasu daga cikin fitattun 'yan siyasa da ke kokarin hana Tinubu zarcewa mulki a 2027:
1. Atiku na jagorantar hadakar kifar da Tinubu
Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar, wanda ya tsaya takara a karkashin PDP a 2023, bai nuna wata alamar janyewa daga siyasa ba.
Atiku Abubakar da hadin gwiwar wasu manyan yan siyasa sun kirkiro hadakar adawa da za a taru a ciki domin tabbatar da cewa APC ba ta koma shugabancin Najeriya a 2027 ba.

Source: Facebook
Rahotanni na nuna cewa akwai yiwuwar Atiku ya mika tayin yin wa’adi daya na shugabanci tare da Peter Obi a matsayin mataimakinsa, don hada karfi da karfe a zaben 2027.
Har yanzu, hadakar adawar da aka kafa tana shawarwari a kan matsayar da za a cimma.
2. Peter Obi na adawa da gwamnatin Tinubu
Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, ya bayyana cewa ta yiwu ba zai sake tsayawa takara a 2027, amma yana tare da hadakar ceto talaka.
Obi na ci gaba da bayyana bukatarsa ta sauya salon siyasar Najeriya, tare da shirin kafa hadaka da wasu manyan ‘yan siyasa.

Source: Twitter
A watan Maris, Obi ya hada kai da Atiku Abubakar da Nasir El-Rufa'i domin kafa wata sabuwar hadaka da za ta kalubalanci Tinubu a zaben da ke tafe.
Wasu rahotanni ma sun nuna yiwuwar Obi zai amince da matsayin mataimaki ga Atiku karkashin yarjejeniyar wa’adi daya, duk da cewa ba daya daga cikinsu ya tabbatar da hakan ba.
3. El-Rufa'i na kalubalantar gwamantin APC
Tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufa'i, na daga cikin masu sukar gwamnatin Bola Tinubu da suka fi bayyana rashin gamsuwarsu da tsarin da ake kai.
A wata ganawa a watan Mayu, El-Rufai ya ce:
“Duk wanda ke ganin Tinubu zai iya komawa mulki a 2027 yana zaune a wata kasa daban, ba Najeriya ba."
El-Rufai ya ce halin da tattalin arzikin kasa ke ciki a yanzu, da tsarin siyasarsa ya sa Tinubu ya rasa goyon bayan jama’a.
4. Seyi Makinde na son karbar mulki
A watan Afrilu, gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana cewa yana da kwarewar jagorantar Najeriya, kodayake ya ce zai duba ra’ayin ‘yan Najeriya da jam’iyyarsa kafin batun takara.

Source: Facebook
Ya ce:
“Babu shakka ina da kwarewar jagorantar kasar nan… amma abin da nake so in yi yanzu, shin shi ne abin da ‘yan Najeriya ke bukata?”
Gwamnan, wanda ke daga cikin 'yan adawa masu rajin kishin jam'iyyarsa ta PDP ya kara da bayyana cewa babu shakka, ana bukatar sauyi a kasar nan.
5. Babachir ya fusata da salon mulkin Tinubu
Babachir Lawal, tsohon sakataren gwamnatin tarayya, na daga cikin fitattun masu adawa da gwamnatin Bola Tinubu.
Lawal na taka muhimmiyar rawa wajen tsara dabarun hadakar siyasa da ke shirin kalubalantar Tinubu a 2027.

Source: Twitter
Ya sha nanata cewa an kai matakin fahimtar juna a hadakar, kuma ba sa bukatar tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya sa albarka kafin a barar da gwamnatin APC.
6. Amaechi da Imoke na adawa da gwamnati
Tsofaffin gwamnonin jihohin Ribas da Kuros Riba, Rotimi Amaechi da Liyel Imoke, na cikin masu tsara dandalin siyasa da hadakar za ta yi amfani da shi wajen korar Tinubu daga ofis.

Source: Facebook
Amaechi na jagorantar kwamitin da ke duba yiwuwar rajistar sabuwar jam’iyya, yayin da Imoke ke jagorantar bangaren da ke nazarin hadin gwiwa da jam’iyyun da suka riga suna kasa.

Source: Facebook
7. Nwosu na ganin ADC za ta ja da Tinubu
Shugaban jam’iyyar ADC, Ralph Okey Nwosu, ya yi watsi da ra’ayin cewa ba za a iya kayar da Tinubu a 2027 ba.
A wata hira da aka yi da shi kwanan nan, Nwosu ya ce daga Legas zuwa Fatakwal, Kano, Uyo, da Sakkwato, talauci da rashin tsaro sun hada kan ‘yan Najeriya.
Ya bayyana cewa matsalolin da ake fama da su sun bayyana gazawar gwamnatin Bola Tinubu wajen hana ci gaban Najeriya.
Ya ce:
“Talauci da rashin tsaro da gwamnatin APC ta jawo suna cinye kasar nan. Gwamnatin APC ta gaza matuka… APC a matsayin jam’iyya ta wuce kima.”
Atiku ya soki mulkin Tinubu
A baya, kun ji cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, ya sake caccakar gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu, yana zargin ta gaza cika alkawari.
Atiku, wanda ke wannan batu bayan Shugaba Bola Tinubu ya shekara biyu a karagar mulki ya ce gwamnati na kara jefa ‘yan Najeriya cikin kunci da talauci, da halin ni 'ya su.
Ya kara da cewa gwamnatin Tinubu ta ci amanar ‘yan kasa tare da gazawa wajen cika alkawurran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe na inganta rayuwarsu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng




