"Zan Ga Masu Kaunata na Gaskiya," Gwamna Ya Bayyana Shirinsa na Komawa APC
- Gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno ya ce lokaci ya yi da zai gane haƙiƙanin masu ƙaunarsa da masu yi masa biyayya
- Umo Eno ya ce sauya shekar da zai yi daga PDP zuwa APC nan da ƴan kwanaki, za ta gwada gaskiyar masu cewa suna tare da shi komai rintsi
- A makon jiya mai girma gwamnan ya tabbatar da shirinsa na komawa APC, inda ya buƙaci muƙarrabansa su biyo shi ko su yi murabus
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Akwa Ibom - Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom ya bayyana cewa shirin sauya shekarsa daga jam’iyyar adawa ta PDP zuwa APC mai mulki ya zama tamkar "gwajin biyayya."
Gwamnan ya ce idan ya koma APC zai gane haƙiƙanin waɗanda suke masa biyayya daga cikin abokan siyasarsa, yana mai cewa a lokacin za a ga masu zama da shi da zuciya ɗaya.

Kara karanta wannan
Ondo: Ɗan Majalisar Tarayya 1 tilo da PDP ke taƙama da shi ya sauya sheƙa zuwa APC

Source: Facebook
Umo Eno ya bayyana haka ce a wurin bikin kaddamar da sabon gidan shugaban ƙaramar hukumar Eket ranar Talata, kamar yadda Premium Times ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamna Eno ya gindaya wa hadimansa sharaɗi
A makon da ya gabata, Gwamna Eno ya tabbatar da cewa zai fice daga PDP zuwa APC, inda ya bukaci kwamishinoni da sauran ‘yan majalisar zartarwarsa su bi shi ko su yi murabus.
Tun da aka dawo mulkin dimokradiyya a 1999, jam'iyyar PDP ke mulki a jihar Akwa Ibom, wadda ke da arzikin man fetur.
A Akwa Ibom, samun tikitin takarar PDP na nufin kusan lashe zabe ne, lamarin da ya sa wasu ke ganin PDP kamar addini a jihar.
Rahotanni sun bayyana cewa Gwamna Eno yana fuskantar matsin lamba da kin amincewa daga abokan aikinsa, har ya fara barazanar korar su daga mukamansu idan basu bi shi zuwa APC ba.
Gwamna Umo Eno ya gargaɗi muƙarrabansa
A kalamansa, Gwamna Eno ya ce:
"Muna buƙatar kwamishinoninmu da ‘yan majalisa da masu mukami su biyo mu, waɗanda ba za su bi mu ba, kuna da ‘yancin hakan, amma ba za ku ci gaba da zama a majalisar zartarwa ta jiha ba.
"Ku shirya yin murabus ranar da na sanar da cewa na koma APC. Ba za ku kasance cikin gwamnatina ba ku na yi wa jam’iyyar da na fice daga cikinta aiki."

Source: Facebook
'Zan gane masu mani biyayya na gaskiya'
Yayin da yake jawabi a Eket ranar Talata, Gwamna Eno ya ce sauya shekarsa zuwa APC zai nuna wadanda suke masa biyayya tsakani da Allah.
"A ‘yan kwanaki masu zuwa, za mu fitar da sanarwa a jihar nan, amma ku sani, wani malamina ya gaya mani cewa Allah ne ya tsara haka domin a gwada masu biyayya," in ji shi.
Gwamnan ya ce nan bada jimawa ba zai gane gaskiyar waɗanda ke cewa suna tare da Eno duk rintsi duk wuya.

Kara karanta wannan
Duk da gargaɗin Tinubu ga masu sauya sheƙa, ɗan majalisa ya tattara kayansa zuwa APC
Sai dai ya ce yana da yakinin cewa shugabannin kananan hukumomi ba za su juya masa baya ba, rahoton Leadership.
Gwamna Eno ya ba shugaban APC kyautar mota
A wani labarin, kun ji cewa Gwamnan Umo Eno, wanda har yanzu ɗan PDP ne ya ba shugaban APC na jihar Akwa Ibom, Obong Stephen Ntukekpo kyautar mota.
Jam'iyyar APC ta reshen jihar Akwa Ibom ta yaba wa gwamnan bisa wannan karamci, kuma ta karɓi kyautar hannu biyu.
Kakakin APC ya kuma bayyana kyautar motar a matsayin alamar da ke nuna cewa Gwamna Eno ya rungumi siyasar wayewa da karimci.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
