PDP Ta Sha Kaye, Kotun Daukaka Ƙara Ta Yanke Hukunci a Karar da Aka Nemi Tsige Gwamna
- Gwamna Monday Okpebholo ya sake doke babban abokin hamayyarsa na PDP, Asue Ighodalo a kotun ɗaukaka ƙara mai zama a Abuja
- A hukuncin da ta yanke yau Alhamis, kotun ta tabbatar da nasarar jam'iyyar APC a zaben gwamnan jihar Edo da aka yi a watan Satumba, 2024
- Sai dai duk da haka ɗan takarar jam'iyyar PDP, Ighodalo bai haƙura ba, ya sha alwashin sake ɗaukaka kara zuwa kotun kolin Najeriya
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Edo - Kotun Daukaka Kara mai zama a Abuja ta tabbatar da nasarar Gwamna Monday Okpebholo na jihar Edo a zaben da aka yi ranar 21 ga Satumba, 2024.
Hakan dai na kunshe ne a hukuncin da kwamitin alkalan kotun mai mutum uku karkashin jagorancin Mai Shari’a M. A. Danjuma ya yanke yau Alhamis a Abuja.

Source: Facebook
Gwamna Monday Okpebholo ya sake doke PDP
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa kotun ta yi watsi da karar da jam’iyyar PDP da dan takararta, Asuerinme Ighodalo, suka shigar domin kalubalantar sakamakon zaben.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kotun ta ce babu wani dalili da zai sa a rushe hukuncin da kotun sauraron ƙararrakin zaben gwamnan Edo ta yanke, wanda ya tabbatar da Gwamna Okpebholo na APC a matsayin wanda ya lashe zaben.
A baya, kotun zaɓe karkashin jagorancin Mai Shari’a Wilfred Kpochi ta yi watsi da ƙorafe-ƙorafen PDP da dan takararta; jam’iyyar AA da shugabanta na kasa, Adekunle Rufai Omoaje; da AP tare da dan takararta, Dr. Bright Enabulele.
Yadda shari'ar ta gudana a kotun zaɓen Edo
Kotun ta ce babu gamsasshen dalili da zai sa a soke sakamakon da INEC ta bayyana wanda ya ba Okpebholo na APC nasara da kuri’u 291,667.
Gwamna Okpebholo ya samu nasarar kayar da babban abokin hamayyarsa, dan takarar PDP, Ighodalo, wanda ya samu ƙuri'u 247,655.
PDP da Ighodalo sun kalubalanci sakamakon zaben da cewa an tafka kura-kurai, magudi, da kuma cewa zaben ya gudana ba kan ka’idojin dokar zabe ta 2022 ba.
Sun kuma zargi INEC da rashin sarrafa kayayyakin zabe yadda ya kamata, musamman batun rashin sanya lambobi a wasu kayan zabe masu muhimmanci, lamarin da suka ce ya taimaka wajen sauya sakamakon zaben.
Masu karar sun gabatar da shaidu 19 tare da hujjoji, inda suka ce an samu kuskuren kidayar kuri’u a rumfunan zabe 765.

Source: Facebook
Zaɓen Edo: Wane hukunci kotu ta yanke?
Da take yanke hukunci, kotun zaɓe ta ce PDP da dan takararta sun kasa gabatar da kwakkwaran shaida da za ta sa a rushe sakamakon zaben.
A yau Alhamis kuma, Kotun Daukaka Kara da ke zamanta a Abuja ta tabbatar da hukuncin kotun zaɓe, kamar yadda jaridar The Nation ta rahoto.
A gefe guda, Asuerinme Ighodalo ya bayyana cewa zai daukaka kara zuwa Kotun Koli, wadda ke da hurumin yanke hukuncin karshe kan shari’ar zaben.
Gwamnan Edo ya yi ƙarin albashi
A wani rahoton, kun ji cewa Gwamna Monday Okpebholo ya amince da ɗaga sabon mafi karancin albashi zuwa ₦75,000 ga ma’aikatan jihar Edo.
Ya ce wannan ƙari wata hanya ce ta nuna godiya ga ma’aikatan gwamnatin jihar, tare da fatan za su ƙara himma wajen ganin Edo ta ci gaba.
Gwamna Okpebholo ya kara da cewa gwamnatinsa ta ɗauki lamarin walwala da jin daɗin ma'aikata da matuƙar muhimmanci tun daga lokacin da ya hau mulki.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


