Ondo: Ɗan Majalisar Tarayya 1 Tilo da PDP ke Taƙama da Shi Ya Sauya Sheƙa zuwa APC
- Ɗan Majalisar Wakilai daga jihar Ondo da ke Kudancin Najeriya, Hon. Olarewaju Akingbaso ya sauya sheƙa daga PDP zuwa jam'iyyar APC
- Hakan na kunshe ne a wata wasiƙa da ya miƙa wa Majalisar Wakilan Tarayya a zamanta na yau Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025 a Abuja
- Ana ganin dai wannan babbar barazana ce ga PDP a jihar Ondo saboda ɗan Majalisar shi ne kaɗai mambanta a Majalisar Wakilai
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
FCT Abuja - Ɗan Majalisar Wakilai guda ɗaya tilo da jam'iyyar PDP reshen jihar Ondo ke taƙama da shi, Hon. Olarewaju Akingbaso ya sauya sheƙa zuwa APC mai mulki.
Hon. Olarewaju Akingbaso, ya tabbatar da ficewarsa daga PDP zuwa APC ne a wata wasiƙa da ya miƙawa Majalisar Wakilai yau Laraba, 28 ga watan Mayu, 2025.

Source: Twitter
Akingbaso ya ce ya yanke shawarar sauya sheka zuwa APC ne domin haɗa kai da kyawawan manufofin jam'iyyar wajen ciyar da kasar nan gaba, The Nation ta rahoto.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Meyasa Ɗan Majalisar ya fice daga PDP
A cewar ɗan majalisar, burinsa na ba da gudummuwa ga kudirin sabunta burin shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na cikin abubuwan da suka ja hankalinsa zuwa APC.
Har ila yau, Hon. Akingbaso ya ce rikice-rikicen cikin gida na PDP da kuma bukatarsa ta hadin gwiwa wajen cika buri da muradan mutanensa ne suka tilasta masa sauya sheka.
Sai dai sauyin shekar Hon. Akingbaso ta tayar da ƙura da haddasa musayar yawu a zauren Majalisar Wakilan Tarayya.
Ƴan adawa sun yi fatali da matakin 'Dan majalisar

Kara karanta wannan
Tinubu ya ƙara ƙarfi, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya haƙura da neman mulki a 2027
Shugaban marasa rinjaye a majalisar, Kingsley Chinda, ya ce lokaci ya yi da majalisar za ta fara aiwatar da tanadin Sashe na 68(1) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
A cewarsa, sashen ya tanadi cewa dan majalisar da ya sauya sheka ba tare da dalilin rabuwar kai a jam'iyyar da ya ci zaɓe ba ya rasa kujerarsa, The Cable ta rahoto.

Source: Facebook
Hon. Chinda ya jaddada cewa wasikar sauya shekar Akingbaso cike take da kalmar "ni" ba tare da ambato ko wakiltar ra’ayin mutanen da suka zabe shi ba.
“Wasikar ba ta bayyana cewa ya yanke shawara ne da amincewar wadanda ya ke wakilta ba,” in ji shi.
Wannan sauyin sheka na iya zama tamkar barazana ga PDP, musamman a jihar Ondo saboda Akingbaso ya kasance dan majalisa daya tilo na jam’iyyar. kafin yanxu da ya koma APC.
Sanata Wamako ya ƙara nakasa PDP
A wani rahoton, mun kawo muku cewa wasu jiga-jigan siyasa da magoya baya sun tattara kayansu sun fice daga jam'iyyar PDP zuwa APC a jihar Sakkwato.
Sanata mai wakiltar Sokoto ta Arewa, Sanata Aliyu Wamakko ne ya karɓi wannan babbar tawagar ƴan siyasa da suka sauya sheƙa daga PDP zuwa APC.
Masu suka sauya sheƙar sun haɗa da shugabannin ƙungiyar ƴan Kasuwa ta jihar Sokoto, a ƙarƙashin jagorancin shugabansu, Alhaji Chika Sarkin-Gishiri.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
