Abu Ya Girma: Sanata Ya Halarci Zaman Majalisar Dattawa Sanye da Rigar Tinubu
- Sanata Orji Uzor Kalu ya shiga zauren majalisar dattawa sanye da riga mai tambarin "Bola Tinubu a matsayin shugaban kasa 2027"
- Kalu ya ce ba shi kadai ne ke sanya irin rigar ba, domin sauran manyan Kudu maso Gabas sun amince da tazarce Shugaba Bola Tinubu
- Yayin da yake yabawa manufofin Tinubu, Sanatan ya ce babu wata jam'iyya ko kawancen jam'iyyun adawa da zai ba APC tsoro a 2027
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Sanata Orji Uzor Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, ya halarci zaman majalisar dattawa ranar Talata sanye da riga mai rubutun “Tinubu a matsayin shugaban kasa 2027”.
Yayin da yake zantawa da manema labarai a majalisar dokoki ta ƙasa, Kalu ya bayyana wannan shiga a matsayin cikakken goyon baya ga tazarcen Shugaba Bola Tinubu.

Source: Twitter
Sanata Orji Kalu ya sanya rigar Tinubu
Jaridar The Cable ta rahoto sanatan yana cewa:
“Ina fata kuna kallon shigar kayan da na yi. Idan kun kalli rigar da nake sanye da ita, za ku fahimci abin da nake nufi.
“Wannan riga ta na nuni da goyon baya na ga shugaban ƙasa. An tsara ta daidai da hakan, kuma gaba ɗaya kusoshin Kudu maso Gabas na tare da shi.”
Sanata Orji Kalu ya ce wasu ma sun fara dinka irin wannan kaya, yana mai cewa:
“Wasu sun fara sanya irin kayan nan, ba wai ni kaɗai ba ne. Ku ne yanzu kuka lura da ita.
“Ina sanye da wannan kayan ne domin nuna goyon baya na ga shugaban ƙasa, shugabanmu, shugaban ku, shugaban Najeriya."
Kudu maso Gabas sun yarda da tazarcen Tinubu
Ya ƙara da cewa tuni masu fada a ji a APC na yankin Kudu maso Gabas suka amince da Tinubu a matsayin dan takararsu, tun ma kafin wasu yankuna su yarda da shi.

Kara karanta wannan
'Aikin ka yana kyau,' Matasan Kaduna sun yiwa Tinubu alkawarin ruwan kuri'a a 2027
“Mun amince da shi tun makonni da suka gabata, karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma, tare da gwamnan Ebonyi da mataimakin kakakin majalisa. Mu ne muka fara amincewa da shi a matakin ƙasa."
- Sanata Kalu.
Kalu ya yaba wa manufofin tattalin arzikin Tinubu, ciki har da cire tallafin man fetur da daidaita farashin canjin Naira/Dala a kasuwa.
Tsohon gwamnan jihar Abia bai tabbatar ko wannan kaya na daga cikin shirye-shiryen yakin neman zaben shugaban kasar na 2027 ba, a cewar rahoton Punch.

Source: Twitter
APC ba ta tsoron jam'iyyun adawa a 2027
Yayin wata hira da manema labarai a majalisar dokoki ranar Talata, Kalu ya ce babu wata jam’iyya ko haɗakar siyasa da ke barazana ga APC a zaben 2027.
Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisa kan hukumar ci gaban Kudu maso Gabas, ya ce tsarin shugabancin Tinubu ya samu karɓuwa daga jam’iyyu daban-daban.
“A’a, ba na ganin APC za ta ji tsoron kowace jam’iyya. Mu ke mulki a yanzu. Muna ƙaunar Najeriya. Shi ya sa muke kafa masana’antu domin samar da ayyuka – har ma da wanda bai da alaƙa da gwamnati.”
- Sanata Orji Kalu.
Dalilin Tinubu na samun goyon bayan mutane
A wani labarin, mun ruwaito cewa, Sanata Orji Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa, ya ce Bola Tinubu na samun karɓuwa matuƙa gabanin zaben 2027.
Kalu ya bayyana cewa tururuwar goyon bayan da ake yi wa Tinubu na da nasaba da manufofinsa na gyaran tattalin arziki da kishin ƙasa.
Ya kuma jaddada cewa jam’iyyar APC ba ta jin tsoron haɗakar jam’iyyun adawa, yana mai cewa nasara za ta tsaya ne kan aiki da kwarewa.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

