2027: Sanatan APC Ya Fadi Dalilin da Ya Sa Tinubu ke Samun Goyon Baya
- Sanata mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa, Orji Kalu, ya taɓo batun goyon bayan da Bola Tinubu ke samu kan zaɓen 2027
- Orji Kalu ya bayyana cewa ana tururuwar nuna goyon baya ga Tinubu saboda ayyukan da ya gudanar a ƙasar nan
- Hakazalika sanatan ya nuna cewa jam'iyyar APC ba ta jin shakkar haɗakar ƴan adawa da ake ƙoƙarin kafawa
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
FCT, Abuja - Sanata Orji Kalu, mai wakiltar Abia ta Arewa a majalisar dattawa ya yi magama kan goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu yake samu.
Sanata Orji Kalu ya ce yawan goyon bayan da ake yi wa Shugaba Bola Tinubu domin sake tsayawa takara ya ta’allaka ne da ayyukan da ya gudanar.

Source: Facebook
Sanata Orji Kalu ya bayyana hakan ne yayin da yake magana da manema labarai a majalisar tarayya a ranar Talata, 27 ga watan Mayun 2025, cewar rahoton jaridar TheCable.

Kara karanta wannan
2027: An samu wanda zai buga da Tinubu, jigo zai fito takarar shugaban ƙasa a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kalu ya ce APC ba ta tsoron haɗaka
Kalu ya bayyana cewa jam’iyyar APC ba ta jin wata barazana daga kowace haɗakar siyasa gabanin zaɓen 2027, rahoton jaridar The Nation ya tabbatar.
Sanata Orji Kalu, wanda shi ne shugaban kwamitin majalisar dattawa kan hukumar raya yankin Kudu maso Gabas, ya ce shugabancin Tinubu ya samar da ƙwarin gwiwa tsakanin mambobin jam’iyyun siyasa daban-daban.
“Ah-ah, ah-ah. Ban yi tunanin cewa jam’iyya kamar APC tana da wanda za ta ji tsoro ba."
“Muna da mulki a hannunmu. Muna ƙaunar Najeriya. Shi ya sa da yawa daga cikinmu ke gina masana’antu a fadin ƙasa domin samar da ayyukan yi, ba tare da dogaro da gwamnati ba."
“Aikin ƴan adawa shi ne su ƙalubalance mu. Amma na mu aikin shi ne mu gudanar mulki, kuma muna yin hakan cikin ƙwarewa. A shekaru masu zuwa, ƴan Najeriya za su yaba da abin da shugaban ƙasa ke yi."
- Sanata Orji Kalu
Kalu ya taɓo batun zuwan Tinubu Vatican
Dangane da ziyarar da shugaban ƙasa ya kai kwanan nan zuwa Vatican, Kalu ya ce hakan ya kasance ne sakamakon gayyatar da Paparoma Francis ya yi masa kai tsaye.

Source: Facebook
“Da zai zama rashin girmamawa ne idan ya ƙi amsa gayyatar Paparoma."
“Kimanin mabiya ɗarikar Katolika biliyan 1.8, ciki har da ni kaina, muna godiya da wannan ziyara. A shekarar 2027, ƴan Katolika za su tuna da hakan."
- Sanata Orji Kalu
Sanata Kalu ya kuma bayyana cewa ƙusoshin Kudu maso Gabas a APC sun riga sun marawa Tinubu baya tun kafin sauran masu mara masa baya a yanzu.
“Mun mara masa baya tun makonni da suka wuce, karkashin jagorancin Gwamna Hope Uzodinma, tare da gwamnan Ebonyi da mataimakin kakakin majalisar wakilai. Mu ne muka fara goyon bayan a ƙasa baki ɗaya."
- Sanata Orji Kalu
Jigon PDP ga yabi Tinubu
A wani labarin kuma, kun ji cewa jigo a jam'iyyar PDP kuma babban ɗan jarida, Dele Momodu, ya yabawa shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.
Dele Momodu ya yabi shugaban ƙasan ne kan matakin da ya ɗauka na hana Nyesom Wike rufe sakatariyar PDP ta ƙasa da ke Abuja.
Ya ce matakin da shugaban ƙasan ya ɗauka ya nuna cewa ba kodayaushe ake barin Wike yana cin karensa babu babbaka ba.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

