Sule Lamido Ya Hango Wanda Zai Zama Shugaban Kasa idan PDP Ta Rushe Kafin 2027
- Sule Lamido ya ce Najeriya za ta faɗa hannun shugabanni ƴan kama karya da danniya matuƙar aka rasa PDP a siyasar ƙasar nan
- Tsohon gwamnan Jigawa ya ce PDP ke da kaso mafi tsoka a tarihin dimokuradiyyar ƙasar nan, don haka idan ta mutu, Najeriya ta mutu
- Sule ya kuma nanata cewa ba zai bar jam'iyyar PDP ba duk da rikice-rikicen cikin gida da suka dabaibaye ta
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawonshekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja - Tsohon Gwamnan jihar Jigawa kuma ɗaya daga cikin waɗanda suka kafa PDP, Sule Lamido, ya ce PDP wani ɓangare ne mai girma a tarihin dimokuraɗiyyar Najeriya.
Sule Lamido ya bayyana cewa Najeriya za ta ci gaba da wanzuwa ne idan jam'iyyar PDP ta nan nan a kan ƙafafunta.

Source: Facebook
Tsohon gwamnan ya faɗi haka ne a wata hira da aka yi da shi a shirin Political Paradigm na tashar Channels TV a ranar Talata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Jam'iyyar PDP bango ce a siyasar Najeriya'
Sule Lamido ya bayyana cewa, idan PDP ta rushe, Najeriya za ta shiga babban haɗari na samun shugabann ƙasar kama-karya, wanda zai yi mulkin danniya.
“Idan PDP ta rushe, to Najeriya za ta rushe. Idan babu jam’iyyar adawa, za mu samu shugaba mai mulkin danniya, kuma su shugabanni ƴan kama karya haɗama ke cinsu.
"PDP ce kusan gaba ɗaya tarihin Najeriya na tsawon shekaru 25, don haka idan ka yi duba ta wannan mahangar, PDP na mutuwa, za ta shafe mafi yawan tarihin Najeriya."
- Sule.Lamido.
"PDP ta taimaki Buhari da Tinubu" - Lamido
Sule ya kara da cewa ba don PDP ta dawo da dimokuraɗiyya a 1999 ba, da tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari na APC ba zai taba samun damar hawa mulki a 2015 ba.
Ya ce shugaban kasa Bola Tinubu ba zai samu nasara a 2023 ba, idan ba don tushen da PDP ta gina tun daga farkon mulkin demokuraɗiyya na jamhuriya ta hudu ba.
Tsohon ministan ya jaddada cewa PDP na da matuƙar muhimmanci ga shugaba Tinubu, domin tana sa ido da matsa masa ya yi abin da ya kamata.

Source: Facebook
Shugaba Bola Tinubu na bukatar PDP
“Fiye da kowa, Tinubu na bukatar PDP ta rika bibiyarsa domin ta sanya shi cikin shiri da tsoron adawa. Idan PDP ta rushe, ba wanda zai rika bibiyar ayyukan shugaban kasa," in ji shi.
Tsohon gwamnan na Jigawa ya kuma bayyana a fili cewa, duk da rikice-rikicen da PDP ke fuskanta, ba zai fice daga jam’iyyar ba, jaridar Vanguard ta ruwaito.
Jigon PDP ya roki a dawo da Peter Obi
A wani labarin, kun ji cewa babban jigo a PDP, Segun Sowunmi ya ce lokaci ya yi da ƴan jam'iyyar za su dawo da tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi.
Sowunmi na ganin ya zama dole PDP ta koma ta nemi Obi, musamman ganin yadda goyon bayan da yake samu daga matasa da masu kishin ƙasa ke kara karfi.
Obi, tsohon gwamnan jihar Anambra ya bar PDP ne a 2022 saboda abin da ya kira maguɗi a zaɓen fidda ɗan takarar shugaban ƙasa na wancan lokacin.
Asali: Legit.ng

