'Aikin ka Yana Kyau,' Matasan Kaduna Sun Yiwa Tinubu Alkawarin Ruwan Kuri'a a 2027

'Aikin ka Yana Kyau,' Matasan Kaduna Sun Yiwa Tinubu Alkawarin Ruwan Kuri'a a 2027

  • Kungiyar matasan yankin Kaduna ta Kudu ta yaba da taimakon Shugaba Bola Tinubu wajen kai masu manyan ayyuka biyu don cigabansu
  • Daya daga cikin jagororin kungiyar, Injiniya Seth Habila Bakut ya bayyana cewa za su sakawa Tinubu da abubuwan da ya yi masu idan ya tsaya takara
  • Baya ga Tinubu, gwamna Uba Sani ya shiga cikin mutanen da kungiyar ta ce suna kawo masu ayyukan ci gaba a sassa daban daban na jihar

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

FCT Abuja – Kungiyar Matasa a Kudancin Kaduna ta Southern Kaduna Youth Stakeholders Forum ta ce Shugaba Bola Tinubu ya share masu hawaye.

Daya daga cikin jagororin kungiyar, Injiniya Seth Habila Bakut ya bayyana cewa za su sakawa alherin Tinubu da alheri a babban zaben 2027 mai zuwa.

Kara karanta wannan

Ranar yara: Tinubu ya kaddamar da shirin yaki da cutar da yara a Najeriya

Tinubu
Matasan Kaduna sun ji dadin ayyukan Bola Tinubu Hoto: Asiwaju Bola Ahmed Tinubu
Source: Facebook

Vanguard ta ruwaito cewa ya fitar bayanin a cikin wata sanarwa da ya fitar, inda ya nanata cewa ba za su manta da gagarumin aikin da Tinubu ya kai yankinsu ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Aikin da ya jawo soyayyar Tinubu a Kaduna

Injiniya Bakut ya yaba wa Gwamnan Kaduna, Uba Sani kan aiki a Asibitin Sir Patrick Ibrahim Yakowa da ke Kafanchan, wanda hakan ya taimaka wajen kafuwar Cibiyar Kiwon Lafiya ta Tarayya (FMC) a yankin.

Tinubu
Matasan Kaduna sun yi alkawarin zazzagawa Tinubu kuri'a Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Haka kuma ya jinjinawa Gwamna Uba Sani bisa ware fiye da hekta 170 na ƙasa domin gina sabon Kwalejin Fasaha na Tarayya da aka amince da shi a Kachia.

Ya ce:

“Wannan hali na karamci da Gwamna Uba Sani ya nuna, ba za a manta da shi ba."

Mazauna Kaduna sun yabi dan majalisarsu

Kungiyar ta kuma yabawa Dan Majalisar Tarayya mai wakiltar Kachia/Kagarko, Dr. Amos Gwamna Magaji, bisa jajircewarsa wajen ci gaban Kudancin Kaduna.

Kara karanta wannan

Bola Tinubu ya sha yabo da ya sace gwiwar Nyesom Wike a Abuja

Kungiyar ta yaba da rawar da ya taka wajen ganin an kafa FMC a Kafanchan duk da turjiya daga wasu bangarori.

Jawabin ya ce:

“Mun yaba da kokarin Hon. Amos Gwamna Magaji wajen jawo manyan ayyukan raya kasa da suka kai daruruwan biliyoyi zuwa yankinmu, wanda hakan ya rage matsalar rashin abubuwan more rayuwa da muke fama da su tsawon shekaru.”

Kungiyar ta bayyana cikakken goyon bayanta ga Shugaba Tinubu, Gwamna Uba Sani da sauran shugabannin APC, inda ta sha alwashin tara kuri’u fiye da miliyan daya a zaben 2027.

Haka kuma ta nuna godiyarta ga al’ummar Kudancin Kaduna bisa goyon bayan da suke bai wa jam’iyyar APC da shugabanninta.

Kaduna: Ana son Tinubu fiye da El-Rufai

A baya, kun samu labarin cewa Gwamnan Nasarawa, Abdullahi Sule, ya bayyana cewa farin jinin Shugaba Bola Tinubu a Kaduna ya zarce na lokacin mulkin tsohon Gwamna Nasir El-Rufai.

Gwamnan ya bayyana hakan ne a wata hira da aka yi da shi da yammacin Talata, 14 ga watan Mayu, 2025, inda ya mayar da martani kan wasu kalamai da El-Rufai ya yi kwanan nan.

A cewar Gwamna Sule, kalaman da El-Rufai ya yi na cewa goyon bayan da Shugaba Bola Tinubu ke da shi a Arewacin Najeriya yana raguwa, ba haka ba ne, don har ya fi shi masoya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng