Malami: Ministan Buhari Yi Yi wa Tinubu, Ganduje da 'Yan APC Rubdugu kan Tsaro
- Tsohon Ministan Shari’a, Abubakar Malami, ya soki jam’iyyar APC bisa nuna goyon baya ga Bola Tinubu a 2027 duk da halin da kasa ke ciki
- Malami ya ce gwamnati ta fi maida hankali kan siyasa maimakon warware matsalolin da ke damun talakawa musamman a Arewacin ƙasar
- Ya yi magana ne yayin da wasu 'yan siyasa a Arewa suka cimma matsaya kan hada kai don samun madafa mai ƙarfi a siyasar Najeriya
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Tsohon ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), ya bayyana damuwa kan yadda jam’iyyar APC mai mulki ke fifita siyasa a kan halin ƙunci da ‘yan ƙasa ke ciki.
Malami ya bayyana hakan ne a wani taron 'yan siyasar Arewa da aka gudanar a Abuja a ranar Lahadi, 25 ga Mayu, 2025.

Kara karanta wannan
ADC: Maganar hadakar adawa ta yi nisa, ana dab da cimma matsaya kan zaben jam'iyya

Source: Facebook
Rahoton Arise News ya nuna cewa Malami ya zargi jam’iyyar da yin watsi da mulki a lokacin da ƙasa ke cikin mawuyacin hali.
Malami ya soki tsare-tsaren Tinubu da APC
Malami ya caccaki yarda da Tinubu a matsayin ɗan takarar APC a 2027, yana mai cewa hakan ya nuna APC ta yi watsi da matsalolin rashin tsaro da talauci da kuma karancin abinci.
The Cable ta ce ya bayyana cewa cire tallafin mai ba tare da tsari ba da kuma gaza kula da iyakokin ƙasa na daga cikin abubuwan da suka durƙusar da tattalin arzikin Arewa.
A cewarsa:
"Manoman Arewa sun shiga cikin mawuyacin hali saboda rashin tsaro da hauhawar farashi."
Malami ya kara da cewa ba daidai ba ne gwamnati ta mayar da hankali kacokan ga burin sake lashe zaɓe a 2027, alhali jama’a na cikin ƙunci da rashin mafita.

Source: Facebook
An buƙaci Arewa ta yi magana da murya ɗaya

Kara karanta wannan
Duk da gargaɗin Tinubu ga masu sauya sheƙa, ɗan majalisa ya tattara kayansa zuwa APC
A wata sanarwa da tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal ya fitar bayan taron, an bayyana cewa lamarin rashin tsaro a yankin Arewa ya kai wani matsayi mai tayar da hankali.
Sanarwar ta ce lamarin ya haddasa ƙara talauci, yawaitar marasa aikin yi, da durƙushewar ilimi a matakin firamare da sakandare.
Abubakar Malami ya ce Arewa za ta farka
Taron ya samu goyon jiga-jigan siyasar Kudu, ciki har da Rotimi Amaechi daga Kudu maso Kudu, Peter Obi daga Kudu maso Gabas da kuma Rauf Aregbesola daga Kudu maso Yamma.
A ƙarshe, Malami da sauran wakilan Arewa sun bayyana cewa lokaci ya yi da yankin zai farka daga dogon barci, ya fito da tsari da murya ɗaya domin samun wakilci mai ƙarfi a siyasar ƙasa.
An nemi Tinubu ya sauya mataimaki a 2027
A wani rahoton, kun ji cewa wata kungiyar Musulmai a Arewacin Najeriya ta yi kira ga Bola Tinubu da APC su ajiye Kashim Shettima.
Kungiyar ta ce ya kamata Bola Tinubu ya dauki Kirista a matsayin mataimakin shugaban kasa a zabe mai zuwa a 2027.
Shugaban kungiyar ya ce Kiristoci sun taka rawar gani wajen mara baya ga tikitin Muslim Muslim a zaben 2023.
Asali: Legit.ng