Jerin Wadanda ke Goyon Bayan Shugaba Bola Tinubu Ya Zarce a 2027
- Yayin da siyasar 2027 ke daukar zafi, akwai alamun da ke nuna cewa Bola Tinubu zai nemi karin wa'adi, domin ya ci gaba da mulki bayan 2027
- An gano yadda kungiyoyi da manyan yan siyasa a APC da jam'iyyun adawa ke fitowa suna bayyana goyon baya Tinubu ya zarce a Aso Rock
- Duk da Tinubu bai karyata cewa ba zai ki tsayawa takara ba, amma ya gargadi kunnen masoyansa da a tsahirta da yi masa kamfe tun yanzu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Yayin da shirye-shiryen zaben 2027 ke sauya salo, yunkurin shugaban kasa Bola Tinubu na sake tsayawa takara ya samu karfin gwiwa daga masu mara masa baya a fadin kasar.
Bola Tinubu ya hau kujerar shugabancin kasa ne a ranar 29 ga Mayu, 2023, kuma ana sa ran zai kammala wa’adinsa na farko a Mayu 2027.

Source: Twitter
A cewar jaridar The Nation, akwai alamun da ke nuna cewa shugaban kasa zai sake tsayawa takara a zaben shugaban kasa mai zuwa na 2027.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A wata sanarwa da aka fitar a ranar 13 ga Afrilu, Tinubu ya roki magoya bayansa da su dakatar da kamfen din don kada su karya dokokin Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta (INEC).
Ana son Bola Tinubu ya yi tazarce
Rahoton ya ce Shugaba Tinubu na samun gagarumin goyon baya daga kusan kowane bangare, ciki har da:
- Gwamnoni 22 na jam’iyyar APC
- Kungiyar shugabannin APC na Arewa ta Tsakiya.
Sauran wadanda ke tare da Tinubu sun hada da
- APC reshen Enugu ta Arewa
- Gwamna Umo Eno
- Dr. Bello Muhammad Matawalle da kuma
- Wata kungiyar siyasa ta Asiwaju.

Source: Facebook
Haka zalika, akwai:
- Festus Keyamo
- Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio
- Shugaban Majalisar Wakilai, Tajudeen Abbas
- Mataimakin Shugaban Majalisar Wakilai, Benjamin Kalu da kuma
- Gwamna Monday Okpebholo.
Wadannan manyan 'yan siyasa masu rike da mukaman gwamnati sun nuna za su so Bola Tinubu ya cigaba da mulki har Mayun 2027.
Sauran sun hada da:
- Gwamna Mohammed Umar Bago
- Gwamna Charles Soludo
- Jagororin APC na Arewa ta Tsakiya
- Nyesom Wike
- Tsohon jagoran tsageru, Government Ekpemupolo
Kungiyoyin siyasa na son Tinubu ya zarce
Jam'iyyun siyasa kamar APGA, Majalisar kasa ta goyon bayan Shugaban sasa (NCPS), Cif Ayirimi Emami da kuma sanatoci uku na PDP daga jihar Osun sun nuna goyon bayansu ga Tinubu.
- Fadeyi Oluwole Olubiyi
- Fadahunsi Francis Adenigba
- Oyewumi Kamorudeen Olalere
Har ila yau, akwai kungiyar na APC daga majalisar tarayya ta jihar Binuwai, wasu 'yan majalisa na APC da kuma kungiyar Northern Minority Alliance for Balanced Leadership (NOMAL) da ke mara wa Tinubu baya.
An kusa cimma matsaya kan hana Tinubu tazarce
A baya, kun ji cewa Shugaban jam’iyyar ADC na ƙasa, Dr. Ralphs Okey Nwosu, ya bayyana cewa tattaunawa kan kafa hadakar jam’iyyun adawa a Najeriya na cigaba da gudana gabanin 2027.
Dr. Nwosu ya ce hadakar na duba yiwuwar amfani da jam’iyyar ADC a matsayin jam’iyyar da za ta tsaya takarar shugaban ƙasa a zaben 2027 domin kalubalantar jam’iyyar APC mai mulki.
Ya bayyana cewa ya ce wannan yunƙuri ba sabon abu ba ne, domin tun watanni 16 da suka gabata ADC ta fara tsara dabarun hadakar siyasa da nufin kawo sauyi ga tafiyar siyasar Najeriya.
Asali: Legit.ng


