Hadakar Adawa: Atiku, Peter Obi Sun Baza Koma, An Gana da 'Yan Siyasar Arewa
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar da tsohon dan takarar shugaban kasa, Peter Obi sun gana da manyan ‘yan siyasa daga jihohin Arewa 19
- An gudanar da taron ne a karkashin kungiyar Arewa ta National Political Consultative Group (NPCG), wanda jiga jigan Arewa suka halarta a Abuja
- Duk da an bayyana cewa an gudanar da taron ne don gano matsalolin kasa, wasu na kallon wannan babban mataki ne ga zaben 2027 mai karatowa
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, da dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar LP a 2023, Peter Obi, sun gana da manyan ‘yan siyasa daga jihohin Arewa 19.
An gudanar da taron wanda ya hada daruruwan manyan ‘yan siyasa a karkashin tutar National Political Consultative Group (NPCG) yayin da magana kan hadakar adawa ta yi nisa.

Source: UGC
Daily Trust ta ruwaito cewa Atiku da Obi sun halarci taron tare da wasu fitattun shugabanni ciki har da tsohon gwamnan Ribas, Rotimi Amaechi; da tsohon gwamnan Kogi, Idris Wada.
Sauran sun hada da tsohon Antoni Janar na Tarayya kuma Ministan Shari’a, Abubakar Malami (SAN), wanda ya gabatar da jawabi kan matsalar rashin tsaro a Arewacin Najeriya.
Wadanda suka halarci taron hadakar
Jaridar The Punch ta ce wasu daga cikin wadanda suka halarci taron sun hada da tsohon shugaban majalisar dattawa kuma shugaban kwamitin amintattu na PDP, Adolphus Wabara.
Sauran sun hada da tsohon Ministan Harkokin Waje, Ambasada Aminu Wali; tsohon Ministan Harkokin ‘Yan sanda, Adamu Maina Waziri; da kuma tsohon Sakataren Gwamnatin Tarayya, Babachir Lawal.

Source: Facebook
Taron ya kuma samu halartar tsohon mataimakin shugaban jam’iyyar APC na kasa daga Arewa, Salihu Lukman; Sanata Ben Obi; da tsohon Ministan Harkokin Matasa, Bolaji Abdullahi, da sauran su.
Dalilin masu shirin hadakar da manyan Arewa
Ko da yake wasu daga cikin mahalarta taron sun bayyana cewa taron na da nufin nemo mafita ga matsalolin da ke addabar Arewacin Najeriya, ana ganin batun ya fi kama da na siyasa.
Wasu masu lura da harkokin siyasa na ganin cewa hakikanin manufar taron ita ce yadda za a karbe mulki daga hannun Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.
Haka kuma, ganin irin manyan mutane daga sassa daban-daban na kasar da suka halarci taron na jiya, zai iya taimakawa wajen tafiyar hadakar adawa.
Hadakar adawa na dab da cimma matsaya
A baya, mun ruwaito cewa Shugaban jam'iyyar ADC na ƙasa, Dr. Ralphs Okey Nwosu, ya bayyana cewa tattaunawar kafa hadakar jam'iyyun adawa na ci gaba da samun nasara.
Dr. Nwosu ya bayyana cewa kwamitocin da jam'iyyar ta kafa sun riga sun gana da jiga-jigan 'yan siyasa da ke da ruwa da tsaki a kan maganar hadakar, ciki har da Atiku Abubakar.
A cewarsa, jam'iyyar ADC ta fara wannan tsari tun watanni 16 da suka wuce, kuma bayan tattaunawar siyasa da shugabanni da sauran jama'ar kasa da za a wakilta.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

