Gwamnan APC Ya Tsage Gaskiya kan Shirin Ficewa daga Jam'iyyar

Gwamnan APC Ya Tsage Gaskiya kan Shirin Ficewa daga Jam'iyyar

  • An yaɗa jita-jitar cewa Gwamna Hyacinth Iormem Alia na jihar Benue na shirin ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki
  • Babban sakataren yaɗa labaran Gwamna Alia ya fito ya yi martani inda ya bayyana matsayar gwamnan kan ficewa daga APC
  • Tersoo Kula ya bayyana cewa ko kaɗan babu ƙamshin gaskiya a jita-jitar da ke cewa ubangidansa zai fice daga jam'iyyar

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Benue - Gwamnan jihar Benue, Hyacinth Iormem Alia ya yi magana kan batun ficewa daga jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya.

Gwamna Hyacinth Alia ya bayyana cewa ko kaɗan bai da shirin ficewa daga jam'iyyar APC wacce ya lashe zaɓe a ƙarƙashinta a shekarar 2023.

Gwamna Hyacinth Alia na Benue
Gwamna Alia ya musanta cewa zai bar APC Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Source: Facebook

Jaridar The Cable ta rahoto cewa Tersoo Kula, sakataren yaɗa labarai na musamman ga Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue, ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Lahadi, 25 ga watan Mayun 2025.

Kara karanta wannan

Daga fara maganar hakaɗa a ADC, ana zargin gwamnan APC ya fara shirin komawa

Gwamna Alia ya musanta shirin barin APC

Tersoo Kula ya bayyana cewa ubangidansa ba shi da wani shiri na barin jam’iyyar APC mai mulki.

Sakataren yaɗa labaran gwamnan ya bayyana rahoton da ke cewa Gwamna Alia na shirin ficewa daga APC saboda rikicin da ke cikin reshen jam’iyyar a jihar Benue a matsayin abin dariya kuma mara tushe.

Tersoo Kula ya ce goyon bayan Gwamna Alia ga APC ba shi da wata shakka, yana mai jaddada cewa babu wani rikici a cikin reshen jam’iyyar APC na jihar Benue.

Hadimin gwamnan ya ce Gwamna Alia na da kyakkyawar alaƙa da Benjamin Omale, shugaban jam’iyyar APC na jihar Benue.

Gwamna Alia zai ci gaba da zama a APC

“Babu wata shakka game da biyayyar Gwamna Hyacinth Alia ga jam’iyyar APC."
"Ya kasance mai himma da aiki tuƙuru a cikin harkokin jam’iyyar, ciki har da goyon bayan da aka bayar kwanan nan ga Shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takarar jam’iyyar APC ɗaya tilo a zaɓen shugaban ƙasa na 2027."

Kara karanta wannan

2027: El Rufai ya fara fuskantar matsala a SDP bayan Atiku, Obi sun zaɓi jam'iyya

"Halartar gwamnan a taron yanki da na ƙasa wanda aka gudanar a ɗaƙin taro na Aso Rock Villa ya ƙaryata jita-jitan da ake yaɗawa na cewa akwai saɓani tsakaninsa da fadar shugaban ƙasa."
"Hakazalika, shugabancin jam’iyyar APC a jihar Benue ba ya cikin wata matsala kamar yadda rahoton da bai da tushe ya nuna."
"Jam’iyyar ƙarƙashin jagorancin Hon. Benjamin Omale na da kyakkyawar mu’amala da gwamnan, kuma tana aiwatar da ayyukanta yadda ya kamata a matakin jiha da na ƙasa, kamar yadda aka gani a kwanan nan yayin taron ƙoli na APC da aka gudanar a Abuja."

- Tersoo Kula

Gwamna Hyacinth Alia
Gwamna Alia ya ce ba zai fice daga APC ba Hoto: Rev. Hyacinth Iormem Alia
Source: Facebook

Gwamnan PDP ya shirya komawa APC

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya taɓo batun ficewa daga PDP zuwa jam'iyyar APC.

Gwamna Eno ya fito ƙarara ya bayyana shirinsa na komawa jam'iyyar APC wacce ke yin adawa a jihar Akwa Ibom.

Hakazalika ya umarci dukkanin muƙarrabansa da su yi murabus idan ba za su bi shi zuwa jam'iyyar APC ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng