Ana Shirin Hadaka, Peter Obi Ya Fara Magana kan Hakura da Takara

Ana Shirin Hadaka, Peter Obi Ya Fara Magana kan Hakura da Takara

  • Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya taɓo batun lokacin da zai neman takara
  • Peter Obi ya nuna cewa da wuya idan zai sake tsayawa takarar wani muƙami bayan babban zaɓen shekarar 2027
  • Sai dai, Peter Obi ya bayyana cewa ko da ya daina neman muƙami, zai ci gaba da goyon bayan matasa masu kishin kawo sauyi a Najeriya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023, Peter Obi, ya yi magana kan lokacin da zai daina tsayawa takara.

Peter Obi ya bayyana cewa babban zaɓen 2027 na iya zama lokaci na ƙarshe da zai nemi kujerar shugaban ƙasa.

Peter Obi
Peter Obi na iya hakura da takara bayan 2027 Hoto: @peterobi
Source: Facebook

Jaridar The Puncha bayyana hakan ne a cikin wani bidiyo wanda ya karade dandalan WhatsApp na jam’iyyar LP yayin wani jawabi da ya yi ga matasan Najeriya.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: 'Yan majalisa sun yi matsaya kan tazarcen Gwamna Radda a Katsina

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Peter Obi zai haƙura da neman takara

Peter Obi, wanda ya tabbatar da cewa zai sake tsayawa takara a 2027 a ƙarƙashin jam’iyyar LP, ya nuna yiwuwar ficewa daga siyasa gaba ɗaya bayan wannan karo.

Tsohon gwamnan na jihar Anambra ya bayyana cewa zai cika shekara 65 a 2027, kuma wataƙila ba zai kasance da sha’awar ci gaba da neman wani muƙamin gwamnati ba bayan wannan shekarun.

“Ina ganin ya kamata mu samu shekaru na ritaya ga ƴan siyasa. A 2027 zan cika 65. Idan shugaban ƙasa ya koma Arewacin ƙasar nan a 2031, wataƙila ba zai dawo Kudu ba sai 2039, a lokacin zan kai shekara 77."
"Ba zan so na sake neman wani muƙami a wannan shekarun ba. Zai lalata komai."

- Peter Obi

Duk da ya nuna cewa ba zai sake tsayawa takara bayan 2027 ba, Peter Obi ya tabbatar wa masu sauraronsa cewa zai ci gaba da goyon bayan matasa masu kishin sauyi na gaskiya a ƙasar nan.

Kara karanta wannan

LP: Ana maganar hadaka, Peter Obi ya fadi jam'iyyar da zai yi takarar 2027

“Ko da zan daina tsayawa takara, zan ci gaba da goyon bayan ku masu neman sauyi na gaskiya, da duk abin da zan iya bayarwa."

- Peter Obi

Ko da yake ba a tabbatar da ranar da aka ɗauki bidiyon ba, hadimin Peter Obi kan harkokin yaɗa labarai, Umar Ibrahim, ya tabbatar da cewa sabon bidiyo ne.

“Sabon bidiyo ne, kusan makon jiya ne, eh. Amma ban iya tuna takamaiman ranar da aka ɗauka ba."

- Umar Ibrahim

Peter Obi
Peter Obi ya nuna yatsa.ga gwamnati Hoto: @peterobi
Source: Twitter

Peter Obi ya taɓo batun raunana ƴan adawa

Yayin da yake magana kan rikicin cikin gida a jam’iyyun adawa, Peter Obi ya ɗora alhakin faruwar hakan a kan gwamnati mai ci, yana cewa gwamnati ce ke haddasa rikicin da ke faruwa a jam’iyyar LP da PDP.

Ya bayyana cewa yin katsalandan cikin harkokin jam'iyya, wani shiri ne da aka kitsa domin raunana jam'iyyun adawa.

“Abin da ke faruwa a jam’iyyar LP da PDP gwamnati ce ta haddasa. Ku ce nina faɗa a ko ina."

- Peter Obi

Peter Obi ya musanta ganawa da Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa ɗan takarar shugaban ƙasa na LP a 2023, Peter Obi ya musanta batun ganawa da Shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan

Ana batun hadaka, jigo a APGA ya ba Atiku shawara kan zaben 2027

Peter Obi ya bayyana cewa rahotan da ke cewa ya gana da Tinubu kan bashin N225bn na bankin Fidelity babu ƙamshin gaskiya a ciki.

Ya nuna cewa ko kaɗan bai nemi ya gana da shugaban ƙasan ba domin yin magana kan bashin da ya shafi bankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng