Daga Fara Maganar Hakaɗa a ADC, Ana Zargin Gwamnan APC Ya Fara Shirin Komawa
- Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue ya ƙauracewa taron da APC ta shirya don mara wa Bola Tinubu baya a 2027
- Alia yana cikin rikici da shugabannin APC na jihar, ciki har da George Akume da sauran jiga-jigan jam'iyyar
- Rahotanni sun ce Alia yana tattaunawa da jam’iyyar ADC, tare da taimakon tsohon gwamna Gabriel Suswam, wanda ke PDP
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Makurdi, Benue - Ana zargin Gwamna Hyacinth Alia na jihar Benue yana ƙara nesanta kansa daga jam’iyyar APC.
Zarge-zargen ya biyo bayan ƙauracewa amincewar jam’iyyar da Bola Ahmed Tinubu a matsayin ɗan takararta a 2027.

Source: Twitter
Gwamna ya guji taron goyon bayan Tinubu
Pulse ta ruwaito cewa an amince da Tinubu a wani taron APC da kwamitin gudanarwa na ƙasa ya shirya a 'Banquet Hall' na Fadar Shugaban Ƙasa.

Kara karanta wannan
2027: An samu wanda zai buga da Tinubu, jigo zai fito takarar shugaban ƙasa a APC
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
An shirya taron ne domin ƙarfafa haɗin kan jam’iyya kafin zagayen zaɓe mai zuwa.
Wani majiya ya bayyana cewa rashin halartar Gwamna Alia a taron ya janyo cece-kuce daga jami’an jam’iyyar, inda suka danganta hakan da rikice-rikicen cikin gida.
Wasu majiyoyi sun ce Alia yana son jam’iyya ta mara masa baya a takararsa ta wa’adi na biyu a lokaci guda da Tinubu a taron.
Da aka ƙi amincewa da bukatarsa, rahotanni sun nuna cewa Alia ya janye daga tattaunawar sannan ya ƙi halartar taron amincewar.
Wannan na faruwa ne yayin da rikicin siyasa ke ƙaruwa tsakanin Alia da manyan shugabannin APC a Benue, ciki har da Sanata George Akume.

Source: Twitter
Rikice-rikicen gwamna da jiga-jigan APC
A baya, Gwamna Alia ya yi ƙoƙarin cire Austin Agada daga shugabancin APC na jihar, wanda ke goyon bayan Akume, amma kotu ta dakatar da hakan a ranar 28 ga Nuwamba, 2024.
Kotun tarayya da ke Makurdi ta dawo da Agada a matsayinsa na shugaban jam’iyyar jihar, ta dakile ƙoƙarin Alia na ɗaukar ikon jam’iyyar.
Sai dai duk da hukuncin kotu, Alia yana ci gaba da tafiyar da wata sabuwar ɓangare a cikin APC na jihar, wanda ke ƙara rikita lamarin.
Zargin shirin sauya sheka zuwa ADC
Rahotanni sun ce Alia ya fara tattaunawa da jam’iyyar ADC, abin da ke nuna yiwuwar sauya sheƙa daga APC, cewar Daily Post.
Tsohon Gwamna Gabriel Suswam da wasu jiga-jigan ADC na da hannu a cikin waɗannan tattaunawa da aka ce sun kai wani matsayi.
Ana kuma zargin akwai wata yarjejeniya a asirce tsakanin Alia da Suswam, wanda ke cikin jam’iyyar adawa ta PDP.
Rahotanni sun ce Alia ya mara wa Suswam baya a yunƙurinsa na zama shugaban ƙasa na PDP, duk da cewa ya fadi.
2027: Yan majalisa sun goyi bayan Tinubu
A wani labarin, shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu na ci gaba da samun goyon baya yayin da ake shirye-shiryen tunkarar zaɓen 2027.
Sanatoci biyu da ƴan Majalisar Wakilai 10 na APC daga jihar Benue sun ayyana goyon bayansu ga Tinubu.
Sun kuma buƙaci gwamnan jihar Benue, Rabaran Hyacinth Alia ya haɗa kai da gwamnatin tarayya wajen magance matsalar tsaro.
Asali: Legit.ng
