APC: Yahaya Bello Ya Yi Magana da aka Ce zai Buga da Tinubu a Zaben 2027

APC: Yahaya Bello Ya Yi Magana da aka Ce zai Buga da Tinubu a Zaben 2027

  • Tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello, ya bayyana cewa bai da wata niyya ta tsayawa takarar shugaban ƙasa a 2027
  • Yahaya Bello ya musanta wani bidiyo da ya sake bayyana a kafafen sada zumunta yana nuna kamar zai kara da Bola Tinubu
  • Tsohon gwamnan ya ce ya mika cikakken goyon baya ga sake zaɓen shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027 mai zuwa

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, ya nesanta kansa daga rade-radin da ke yawo a kafafen sada zumunta da ke cewa yana shirin tsayawa takarar shugaban ƙasa a shekarar 2027.

Yahaya Bello ya bayyana haka ne cikin wata sanarwa da daraktan yaɗa labaransa, Michael Ohiare, ya fitar a ranar Juma’a 24 ga Mayu, 2025.

Kara karanta wannan

Babban Malami ya tsunduma siyasa, ya bayyana kujerar da zai nema a takarar 2027

Yahaya Bello
Yahaya Bello ya ce ba zai kara da Tinubu ba. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Punch ta wallafa cewa Yahaya Bello ya ce bidiyon da ya bayyana a intanet yana nuni ne da wani taron da ya gudana a 2022.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sanarwar ta ce bidiyon yana ƙoƙarin jefa shi cikin rikici da shugaban ƙasa Bola Tinubu, wanda ya ce yana da cikakken goyon bayan sake zaɓensa.

Yahaya Bello ya yi magana kan takarar 2027

A cewar Ohiare, bidiyon da ke yawo yana ɗauke da bayanai ne da aka yi a shekarar 2022, wadda wasu suka sake wallafawa suna yi wa jama’a ƙaryar cewa sabuwar fafutuka ce ta siyasa.

Ya ce masu yaɗa bidiyon sun yi watsi da rubutun shekarar 2022 da ke bisa tutoci da allunan talla a wurin taron, suna ƙoƙarin rudar da mutane.

Ya bayyana hakan a matsayin wani sabon salo daga hannun maƙiya da ke ƙoƙarin jawo sabani tsakaninsa da shugaban ƙasa, da sunan nuna cewa yana son bugawa da Tinubu a 2027.

Kara karanta wannan

Wasu manya daga Arewacin Najeriya sun cimma matsaya kan wanda za su zaɓa a 2027

Lamarin ya dauki hankali ne duba da yadda gwamnoni da shugabannin APC suka ayyana Bola Tinubu a matsayin dan takararsu a zaben 2027 mai zuwa.

2027: Yahaya Bello zai goyi bayan Tinubu

Yahaya Bello ya bayyana cikakken biyayyarsa da goyon bayansa ga shugaba Bola Tinubu, yana mai cewa nasarorin gwamnatin yanzu sun isa su ba shi damar sake samun yardar 'yan Najeriya.

Sanarwar ta kuma bayyana cewa ya kamata 'yan Najeriya su watsar da irin waɗannan ruwayoyi marasa tushe da ƙwaƙwalwar masu ƙirƙirarsu ke gaza gane gaskiya.

Yahaya Bello
Yahaya Bello ya ce yana goyon bayan Tinubu. Hoto: Alhaji Yahaya Bello
Source: UGC

Yahaya Bello ya jaddada cewa ba shi da wata manufa ta neman mulki a 2027, kuma zai ci gaba da aiki tare da shugaba Tinubu domin cigaban Najeriya.

'Yan APC a Arewa sun goyi bayan Tinubu

A wani rahoton, kun ji cewa 'yan APC a Arewa ta Tsakiya sun yi taro na musamman domin nuna goyon baya ga shugaba Bola Ahmed Tinubu a zaben 2027.

Taron ya hada da gwamnonin Arewa ta Tsakiya biyar, ministoci, yan majalisa da dukkan masu ruwa da tsaki na jam'iyyar APC a yankin.

An hango tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello da shugaban APC na kasa Abdullahi Umar Ganduje a wajen taron.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng