Kifar da Tinubu: 'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nuna Alamar Janyewa Peter Obi

Kifar da Tinubu: 'Dan Takarar Shugaban Kasa Ya Nuna Alamar Janyewa Peter Obi

  • 'Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar SDP a zaben 2023 da ya gabata, Adewole Adebayo, ya nuna alamar janye wa Peter Obi a zaben 2027
  • Adebayo ya bayyana hakan ne yayin wata tattaunawa da 'yan jarida, inda ya ce ana gudanar da shawarwari a boye don kifar da Bola Tinubu
  • Ya jaddada cewa fafatawar zaben 2027 ba wai batun sauya sheka ba ne ko hayaniyar siyasa, illa dai burin ceto Najeriya daga halin da take ciki

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - Adewole Adebayo da ya yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 karkashin jam’iyyar SDP ya nuna alamar janyewa domin bai wa Peter Obi damar mara masa baya a 2027.

Da siyasar ya yi magana ne yayin da ake cigaba da tattauna lamarin siyasar Najeriya da zaben 2027.

Kara karanta wannan

"Ba zan janye wa Atiku ba," Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa ya kawo cikas a shirin 2027

Adewole Adebayo
Dan takarar SDP ya nuna alamar janye takara wa Peter Obi a 2027. Hoto: Adewole Adebayo
Source: Twitter

Adebayo ya bayyana haka ne yayin wata hira da ya yi a shirin siyasa na Channels TV a ranar Laraba, inda ya tofa albarkacin bakinsa kan shirin wasu ’yan adawa na yin hadaka.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A cewarsa, akwai wata babbar tattaunawa a boye da ake yi don samun hadin kai domin sauke shugaban kasa Bola Tinubu daga mulki a 2027.

“Ina jin dadin abin da Obi ke yi” — Adebayo

Adebayo ya ce ko da yake har yanzu bai dauki cikakken matsayi ba, yana yaba wa irin yadda Peter Obi ke tafiyar da harkokinsa na siyasa cikin kwarewa da kwanciyar hankali.

Jaridar Tribune ta wallafa cewa ya ce:

“Maganar janye takara za ta zo daga baya, amma ina son yadda Obi yake tafiyar siyasa. Yana tattaunawa cikin hikima, kuma ba ya hayaniya.”

SDP na tattauna batun kayar da Tinubu

Ya kara da cewa yanzu haka jam’iyyarsu ta SDP na tuntubar wasu ’yan siyasa daga waje don hada kai da su, yana mai cewa na su tsarin yana tafiya ne a sirrance.

Kara karanta wannan

Wasu manya daga Arewacin Najeriya sun cimma matsaya kan wanda za su zaɓa a 2027

Adebayo ya ce ba wai duk lokacin da suka tattauna sai sun dauki hoto domin nunawa duniya ba kamar yadda wasu ke yi.

Adebayo ya ce Obi zai taka rawar gani a 2027

Adebayo ya jaddada cewa yakin neman zaben 2027 ba zai kasance kan sauya sheka da yaudarar jama’a ba, sai dai hadin gwiwa da dinke sabani domin fuskantar jam’iyya mai mulki.

A cewarsa, gwamnatin Tinubu ba ta cika burin ’yan Najeriya ba, kuma mutane sun riga sun yanke hukunci cewa idan ba a yi gyara cikin shekaru biyu masu zuwa ba, akwai yiwuwar zai fadi zabe.

Adebayo ya ce nasarar da ’yan adawa za su iya samu a 2027 na bukatar hadin kai mai karfi, kuma yana ganin Obi na iya taka rawar gani wajen shirin hakan.

Peter Obi
Adewole Adebayo ya yaba da rawar da Peter Obi ke takawa a siyasar Najeriya. Hoto: Mr Peter Obi
Source: UGC

ADC za ta yi taro kan hadaka a Abuja

A wani rahoton, kun ji cewa shugaban ADC ya tabbatar da cewa jam'iyyar na shirye shirye kan maganar hadaka a 2027.

ADC ta ce ta shafe rabin shekara tana tattaunawa da 'yan adawa domin fitar da matsayar siyasa a zaben 2027 domin tunkarar Bola Tinubu.

Shugaban jam'iyyar ya ce idan suka kammala tattaunawa da kwamitocin da suka kafa za su fitar da sanarwa a hukumance.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng