Zaben 2027: Jigo a APC Ya Cika Baki kan Tazarcen Shugaba Tinubu
- Tsohon ɗan takarar gwamnan jihar Legas a zaɓen 2023, Abdul-Azeez Adeniran, ya taɓo batun tazarcen Shugaba Bola Tinubu
- Adeniran ya bayyana cewa babu abin da zai hana Tinubu yin tazarce a kan mulki a 2027 idan ya yi niyyar tsayawa takara
- Ya nuna cewa gamsuwa da kamun ludayin mulkin Shugaba Tinubu ne ya sanya ya koma jam'iyyar APC mai mulki daga PDP
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Jigo a APC kuma tsohon ɗan takarar gwamna na jam’iyyar PDP a jihar Legas a shekarar 2023, Abdul-Azeez Adeniran ya yi magana kan tazarcen Shugaba Bola Tinubu a 2027.
Abdul-Azeez Adediran (wanda aka fi sani da Jandor), ya bayyana cewa sake zaɓen Shugaba Bola Ahmed Tinubu a shekarar 2027 abu ne da ba za a iya hana faruwa ba.

Kara karanta wannan
Jam'iyyar SDP ta zo da sabon shiri, ta saɓawa Atiku da El Rufai kan kifar da Tinubu a 2027

Source: Facebook
Ya bayyana hakan ne yayin gangamin da aka shirya don sanar da komawarsa APC a unguwar Ojo da ke jihar Legas a ranar Juma’a, cewar rahoton jaridar The Nation.
Abdul-Azeez Adediran ya fice daga PDP ne a ranar 3 ga watan Maris, inda ya sanar da komawarsa jam’iyyar APC da ya taɓa kasancewa cikinta a baya.
Batun takarar Bola Tinubu a 2027
Tsohon ɗan takarar gwamnan ya bayyana cewa aikin da ke gabansa yanzu shi ne ya yi aiki tukuru domin ganin an sake zaben Shugaba Bola Tinubu a 2027, rahoton The Guardian ya tabbatar.
Adediran ya ce manufofi masu amfani da shugaban kasa ke aiwatarwa da kuma yawaitar masu sauya sheƙa zuwa APC, ya tabbatar da cewa sake zaɓensa a 2027 ba zai samu tangarda ba, idan har ya yanke shawarar tsayawa takara.
"Abin da ya sa muka yanke shawarar dawowa gida (APC) shi ne sakamakon gyare-gyaren da shugaban ƙasa ke yi.”

Kara karanta wannan
2027: APC ta dauki zafi da Atiku ya ambato mutanenta cikin masu son kifar da Tinubu
“Cire tallafin man fetur ya nuna cewa Tinubu shugaba ne mai sadaukar da kai, domin da yana son kawai ya tsaya don ya sake samun wa’adin mulki, da ya bar tallafin a haka."
“Shugaban ƙasa yana da niyyar yin abin da ya fi amfani ga al’umma, kuma gyare-gyaren da yake yi sun riga sun fara haifar da ɗa mai ido."
“Hakan ne ya sa za mu yi duk abin da zai yiwu domin ganin mun yi aiki tuƙuru don sake zabensa.”
“Babban burinmu shi ne ganin wannan mutum ya koma kujerar shugabanci a 2027 domin ci gaba da gyara ƙasar nan,”
- Abdul-Azeez Adediran

Source: Twitter
Jandor ya taɓo batun takara a 2023
Adediran ya ƙara da cewa duk da bai samu nasara a matsayin ɗan takarar PDP a 2023 ba, fafutukar da ya yi ta buɗe sababbin damammaki ga al’ummar yankin Badagry da ke cikin jam’iyyar APC.
A nasa bangaren, Shugaban jam’iyyar APC na jihar Legas, Cornelius Ojelabi, ya ce jam’iyyar na alfahari da dawowar Adediran da tawagarsa, inda ya bukaci shugabannin jam’iyyar da su rungume su hannu bibbiyu.
An buƙaci Tinubu ya kori minista
A wani labarin kuma, kun ji cewa wani ɗan gwagwarmaya, Theo Agada, ya taso shugaban ƙasa Bola Tinubu a gaba kan ya kori ɗaya daga cikin ministocinsa.
Theo Agada ya buƙaci Shugaba Tinubu da ya kori ministar al'adu da ƙirƙire-ƙirƙiren fikira, Hannatu Musa Musawa.
Ɗan gwagwamaryar ya buƙaci hakan ne saboda abin da ya kira rashin kataɓus da ministar ke yi tun bayan da aka naɗa ta a muƙamin..
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
