Ganduje Ya Fadi Abin da zai Tilastawa Jam'iyyar APC Ta Amshi Kwankwaso

Ganduje Ya Fadi Abin da zai Tilastawa Jam'iyyar APC Ta Amshi Kwankwaso

  • Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa shirye suke su karɓi Rabiu Musa Kwankwaso idan zai koma APC
  • Ana ta jita-jitar cewa tsohon gwamnan Kano, wanda ke jagorantar NNPP, na shirin komawa APC, duk da cewa ba a tabbatar da hakan ba
  • A kalaman Ganduje, ya ce yana ganin dacewar taimaka wa Kwankwaso domin ceto shi, yana mai kwatanta shi da kifin da ya fita daga ruwa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce a shirye suke su karɓi tsohon gwamnan Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, idan zai koma jam'iyyarsu.

Sanata Kwankwaso, wanda yi takarar shugaban kasa a zaben 2023 a karkashin NNPP, shi ne wanda Ganduje ya gada a matsayin gwamnan Kano.

Kara karanta wannan

'Alo tsiya, alo danja,' Abdullahi Abbas ya ce APC za ta kwaci mulkin jihar Kano

Kwankwaso
Ganduje ya ce APC za ta ceci Kwankwaso idan ya dawo cikin APC Horo: Rabiu Musa Kwankwaso/Dr. Abdullahi Umar Ganduje OFR
Source: Facebook

Jaridar Vanguard ta ruwaito cewa an kwana biyu ana ta rade-radin cewa Kwankwaso na shirin sauya sheƙa zuwa jam’iyyar APC.

Sai dai jam’iyyarsa ta NNPP ta karyata wannan jita-jita, tana mai jaddada cewa tsohon Ministan Tsaro yana jin dadin zamansa a inda yake yanzu.

Ganduje ya magantu kan dawowar Kwankwaso APC

Daily Post ta ruwaito cewa yayin da yake zantawa da ’yan jarida a ranar Talata a Abuja, Ganduje ya ce APC a shirye take, ta buɗe ƙofa ga Kwankwaso idan yana son dawowa. Ganduje ya ce:

“APC na zurfafa da faɗaɗa dimokuraɗiyya a ƙasar nan. Kwankwaso kamar kifin da ya fita daga ruwa ne, yana ƙoƙarin komawa cikin ruwa. Ba za mu ce ba za mu iya karɓarsa ba, domin aboki a lokacin buƙata, aboki ne na hakika.”

Ganduje ya ce za su ceto siyasar Kwankwaso

Tsohon gwamnan Kano, kuma shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje, ya ce jam’iyyarsu za ta karɓi Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso domin ceto siyasarsa.

Kara karanta wannan

An zo wajen: Ministan Tinubu ya fadi sharadin karbar Kwankwaso a APC

Ganduje
Shugaban APC na ƙasa, Abdullahi Ganduje ya ce Kwankwaso ya shiga matsala Hoto: Dr. Abdullahi Umar Ganduje
Source: Twitter

Ya ce:

“Ba ma son barinsa haka nan ba tare da taimako ba. Har yanzu za mu iya karɓarsa idan yana son shiga jam’iyyarmu.
"Idan ka ga ɗanka yana neman wurin da zai samu mafaka, kuma kai ɗan uwa ne a babban gida, a ganina abin da ya dace shi ne ka karɓe shi. Don haka ba za mu ce ba za mu iya karɓarsa ba."

Alakar Kwankwaso da Ganduje

Rabiu Musa Kwankwaso da Abdullahi Umar Ganduje sun dade suna siyasa tare kafin rikici ya balle tsakaninsu wanda ya haifar da rabuwar kai da jam’iyya.

Kwankwaso shi ne ya zabi Ganduje a matsayin mataimakinsa lokacin yana gwamna a Kano a wa'adin 1999-2003 da 2011-2015.

Bayan nan sun shafe shekaru tare tun lokacin da Kwankwaso ke Ministan Tsaro a zamanin Obasanjo.

Bayan Kwankwaso ya kammala wa’adinsa na biyu a 2015, ya mara wa Ganduje baya har ya zama gwamna.

Kara karanta wannan

APC ta nakasa shirin Atiku, ƴan takarar gwamna 2 da mambobi 12,000 sun bar PDP da ACP

Sai dai matsalar ta fara ne bayan Ganduje ya karɓi mulki a Mayun 2015, inda aka fara samun bambancin ra’ayi da tsamin dangantaka.

Kwankwaso ya zargi Ganduje da bijirewa tsarin siyasar su na Kwankwasiyya, yayin da Ganduje kuma ke kallon Kwankwaso a matsayin wanda ke neman tsoma baki cikin harkokin mulki.

Daga baya rikicin ya kara tsananta, har Ganduje ya fice daga inuwar Kwankwasiyya, sannan ya kafa nasa gungu a cikin jam’iyyar APC a Kano.

Kwankwaso daga bisani ya fice daga APC zuwa PDP, daga nan kuma ya shiga jam’iyyar NNPP, inda ya tsaya takarar shugaban kasa a 2023.

Ganduje ya ce jam'iyyar su Kwankwaso ta mutu

A wani labarin, kun ji cewa ahugaban jam’iyyar APC na ƙasa, Dr Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa jam’iyyar adawa ta NNPP ta mutu, ta gama tasiri a kasar nan.

Ganduje ya bayyana haka ne yayin da ƙungiyar masu mara wa Shugaba Bola Ahmed Tinubu baya suka kai masa ziyarar girmamawa a sakatariyar APC ta ƙasa da ke Abuja.

Tsohon gwamnan Kano, Ganduje, ya ce jam’iyyar NNPP ta rasa duk wata kafa da tasiri da take da ita, musamman a jihar Kano inda da dama daga cikin ‘yan jam’iyyar suka fice.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng