APC Ta Nakasa Shirin Atiku, Ƴan Takarar Gwamna 2 da Mambobi 12,000 Sun Bar PDP da ACD

APC Ta Nakasa Shirin Atiku, Ƴan Takarar Gwamna 2 da Mambobi 12,000 Sun Bar PDP da ACD

  • Tsofaffin ƴan takarar gwamna biyu sun jagoranci dubban mambobin PDP da ACP zuwa jam'iyyar APC a jihar Neja
  • Ɗan takarar gwamna a inuwar ACP a zaɓen da ya gabata a Neja, Bello Bwari ya musanta raɗe-raɗin cewa ya koma APC ne don a ba shi mataimakin gwamna
  • Amma a cewar tsohon ɗan takarar PDP, sun koma APC ne saboda ayyukan ci gaba da jihar Neja ta samu wanda ya yi daidai da manufarsa ta siyasa

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Jihar Niger - Guguwar sauya sheƙa ta dura kan jam'iyyun adawa a jihar Neja yayin da ake shirye-shiryen zaɓen ƙananan hukumomi a wannan shekara watau 2025.

Sama da mambobi 12,000 daga jam’iyyun PDP da ACP sun tattara kayansu sun koma jam’iyyar APC mai mulki.

Jam'iyyar APC.
APC ta ƙara yawa a jihar Neja da mambobin PDP da ACD akalla 12,000 suka sauya sheka zuwa jam'iyya mai mulki Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Channels TV ta tattaro cewa tsohon ɗan takarar gwamna a inuwar jam'iyyar ACP, Bello Bwari, ne ya jagoranci tawagar masu sauya sheƙar zuwa APC.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ƙara nakasa El Rufai da Kwankwaso, jiga jigai sun bar PDP da NNPP

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Shugabannin APC reshen jihar Neja sun tarbe su hannu bibbiyu a wani taro na musamman da aka shirya a sakatariyar jam'iyya da ke Minna.

Meyasa ƴan takarar gwamna suka koma APC?

Da yake magana da manema labarai, Bello ya karyata jita-jitar da ke yawo cewa yana da muradin zama mataimakin Gwamna Umaru Bago shiyasa ya koma APC.

Mutane sun fara yaɗa jita-jitar cewa Bello Bwari na neman zama mataimakin gwamnan Neja a daidai lokacin da ake zargin alaƙa ta yi tsami tsakanin Umaru Bago da mataimakinsa.

Sai dai Bello ya ƙaryata jita-jitar, yana mai cewa babu kanshin gaskiya a cikinta, amma duk da haka ya ce idan damar hakan ta samu zai karba ya gode ma Allah.

A halin da ake ciki kuma, Gwamna Umaru Bago ya ce yana da kyakkyawar alaka da mataimakinsa, kuma ya ce babu wanda zai iya raba su.

Gwamna Bago da Yakubu Garba.
Tsofaffin ƴan takarar gwamna da magoya bayansu sun koma APC a Neja Hoto: Mohammed Umaru Bago
Source: Twitter

APC ta ƙara nakasa shirin Atiku na haɗaka

Kara karanta wannan

"Mace mai kamar maza": Ƴar takarar mataimakiyar gwamna a 2023 ta koma APC

Tsohon dan takarar gwamnan PDP a 2023 kuma tsohon dan majalisar wakilai, Sani Kutigi, wanda ke ciki masu sauya sheƙar, ya ce sun koma APC ne saboda ayyukan alherin da take yi.

Ya nanata cewa ya zaɓi shiga APC ne bayan ya lura da irin ci gaban da aka samu a jihar Neja, wanda ya dace da burinsa na siyasa.

Sakataren jam’iyyar APC a jihar Neja, Adamu Gani, ya ce kofa a bude take ga duk wanda ke sha'awar shiga jam'iyya mai mulki.

Ana ganin sauya shekar dubban ƴan siyasar ya ƙara karfafawa APC gwiwa a shirin tunkarar zaben 2027 kuma naƙasu ne ga shirin haɗakar Atiku Abubakar.

'Yan NNPP da PDP sun koma APC a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa manƴan ƴan siyasa da mambobi sama da 300 a Kawo jihar Kaduna sun fice daga PDP da NNPP zuwa APC.

Masu sauya sheƙar sun bayyana cewa ba komai ya sa suka koma APC sai don ganin irin ci gaban da Gwamna Uba Sani ke kawo wa al'umma a Kaduna.

Da yake karbar masu sauya shekar a madadin Gwamna Uba Sani, shugaban APC na Kaduna ta Arewa, Alhaji Suleiman Wada Usman, ya ce za su samu damar kamar kowa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262