2027: Buba Galadima Ya Hada Tinubu, Atiku da El Rufa'i, Ya Gyara Musu Zama

2027: Buba Galadima Ya Hada Tinubu, Atiku da El Rufa'i, Ya Gyara Musu Zama

  • Jigo a NNPP, Buba Galadima, ya bayyana cewa tsohon gwamnan Kaduna, Nasir El-Rufai, wakili ne kawai na Atiku Abubakar a jam’iyyar SDP
  • Buba Galadima ya gargadi Atiku da kada ya sake tsayawa takarar shugaban kasa a 2027, yana mai cewa hakan zai kara dagula lamarin siyasar kasar
  • Ya zargi gwamnatin APC da kokarin rushe NNPP da gwamnatin Kano, yana mai cewa duk wani yunkuri na karkato da ‘yan jam’iyyarsu zai ci tura

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Kano - Dan siyasa a Najeriya kuma jigo a NNPP, Buba Galadima ya ce tsohon gwamnan jihar Kaduna, Nasir El-Rufai, wakili ne kawai na Atiku Abubakar a SDP.

Buba Galadima ya yi watsi da ra’ayoyin da ke cewa NNPP na aiki da APC, yana mai cewa gwamnatin tarayya na amfani da jami’an tsaro don durkusar da gwamnati a Kano.

Kara karanta wannan

'Dalilin da ya sa Tinubu ka iya fuskantar cikas a takararsa na zaben 2027'

Buba Galadima
Buba Galadima ya bukaci Atiku ya hakura da takara a 2027. Hoto: Kwankwasiyya Reporters
Source: Facebook

A hira da ya yi da Punch, Buba Galadima ya nuna damuwa kan yunkurin sake fitowa takarar shugaban ƙasa da Atiku ke yi, yana mai cewa hakan ba zai amfanar da ‘yan Najeriya ba.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

El-Rufai ba zai iya jagoranci ba inji Galadima

Buba ya bayyana cewa El-Rufai ba zai iya zama shugaban ‘yan adawa ba, yana mai cewa ba zai karbu ba a idon jama’a saboda yadda ya cuci mutane da dama a baya.

A cewarsa, El-Rufai mutum ne mai cin amanar abokansa, ya ci amanar Atiku Abubakar, Olusegun Obasanjo da sauransu kuma ba wanda zai yarda ya biyo bayansa.

Ya kara da cewa El-Rufai ba mai kafa jam’iyya ba ne, amma dai ana amfani da shi ne kawai don ya rike jam’iyyar SDP har sai wanda ake jira ya karba daga baya.

Buba Galadima
Buba Galadima ya ce El-Rufa'i ba zai iya jagorantar 'yan adawa ba. Hoto: Nasir El-Rufa'i.
Source: Twitter

Kano: Buba Galadima ya soki jam'iyyar APC

Buba Galadima ya zargi jam’iyyar APC da kokarin durkusar da gwamnatin Kano da ke karkashin NNPP, yana mai cewa ana kokarin hana shi aiki yadda ya kamata.

Kara karanta wannan

Jam'iyyar APC ta ƙara nakasa El Rufai da Kwankwaso, jiga jigai sun bar PDP da NNPP

Ya bayyana cewa ana bai wa wasu ‘yan siyasa makudan kudi da ayyuka don su juya akalar NNPP a Kano.

A cewarsa, wannan tsarin ba zai karbu a Kano ba domin mutane sun gane makircin, kuma ba za su juya baya ga jam’iyyar da ta kawo musu ci gaba ba.

Buba Galadima ya kare Kwankwaso daga zargi

A kan zargin cewa Kwankwaso yana goyon bayan gwamnatin Tinubu, Galadima ya ce ba gaskiya ba ne, yana mai cewa APC ita ce ke kokarin rushe NNPP da gwamnatin Kano.

Ya bayyana Kwankwaso a matsayin ɗan siyasa da ke da farin jini fiye da kowa a Najeriya, yana mai cewa babu wani da ya fi karbuwa a wajen talakawa sama da shi.

A karshe Buba Galadima ya ce Bola Tinubu abokinsa ne, amma yana kiransa da cewa kokarin rusa 'yan adawa ba zai jawo masa nasara a siyasa ba.

Sauyi a siyasar Najeriya

Tsarin siyasa a Najeriya na fuskantar sauye-sauye da kalubale da ke kara nuna buƙatar sake duba yadda ake gudanar da lamarin siyasa da mulki.

Kara karanta wannan

Musa Kwankwaso ya faɗi maƙarƙashiyar da ake shiryawa NAHCON, Sheikh Pakistan

Akwai alamun gajiya da tsarin da ya jima yana karakaina ba tare da wani tasiri kan al'ummar kasar ba, musamman talakawa.

Sai dai, a irin tafiyar da su El-Rufai suka dauko, lamari da ke kama da rasa samun damar rike wani mukami da ya kai ga suka tunzura zuwa wata tafiyar.

A lokuta da dama, El-Rufai kan bayyana cewa, ya sauya tafiya ne duba da yadda wannan mulkin na Tinubu bai da damu da lamarin gwamnati ba.

Duk da haka, akwai wadanda ke yi masa kallon mai neman mafaka don tabbatar da an kawo karshen gwamnatin APC a zaben 2027 duk da kasancewarsa daya daga wadanda suka assasata.

Badakalar N2bn: Abba Kabir ya wanke Kwankwaso

A wani rahoton, kun ji cewa Abba Kabir Yusuf ya wanke Sanata Rabiu Musa Kwankwaso daga zargin da ake yi masa.

Abba Kabir Yusuf ya ce zargin da ake yi na cewa Kwankwaso na karbar N2bn duk wata daga asusun Kano ba gaskiya ba ne.

Gwamnan ya yi magana ne a matsayin martani ga ikirarin sakataren gwamnatin jihar da aka sallama, Dr Abdullahi Baffa Bichi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng