'Yan Bangaren Buhari CPC Sun Koka da Tafiyar APC, Sun Yi Matsaya kan Hadaka
- Tsofaffin shugabannin jihohi na jam’iyyar CPC sun bayyana cewa biyayyarsu ga Muhammadu Buhari ya sa suke nan a APC duk da ana wulakanta su
- Sun ce ko da yake ana samun tsaiko a rarraba mukamai da wakilci, amma suna da niyyar ci gaba da aiki da Bola Tinubu don ciyar da jam’iyyar gaba
- Sun nisanta kansu daga rade-radin cewa wasu cikinsu za su kafa kawance da ‘yan adawa, suka ce suna nan daram a jam'iyyar APC mai rike da mulki
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja - Yayin da ake magana kan zaben 2027, wasu daga cikin tsofaffin shugabannin jihohin da suka fito daga tsohuwar jam’iyyar CPC sun fadi dalilansu na ci gaba da zama a APC.
A sanarwar da sakataren kungiyar, Sulaiman Oyaremi ya fitar a ranar Lahadi, shugabannin sun ce biyayya ga tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari ne ya sanya su zama a jam'iyyar.

Source: Twitter
Punch ta wallafa cewa sun kuma koka kan yadda ake ware su, musamman wajen rabon mukamai da tsarin jam’iyya, duk da rawar da suka taka wajen kafa APC.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
'Yan CPC sun ce suna tare da Buhari da Tinubu
Tsoffin shugabannin CPC sun bayyana cewa suna nan a jam’iyyar APC ne saboda biyayyarsu ga Muhammadu Buhari, wanda suka bayyana a matsayin jagoransu har yanzu.
Sanarwar ta bayyana cewa:
“Baya ga kadan daga cikinmu, yawancinmu mun amince da ci gaba da zama a jam’iyyar tare da jagoranmu, Buhari.
"Kuma hakan ba ya nufin ba za mu goyi bayan shugaba Tinubu ba.”
Sun jaddada cewa suna son ganin an gina jam’iyya da za ta dama da kowa da kowa, ba tare da nuna wariya ko takura ga wani bangare ba.
'Yan CPC sun yi korafi kan tafiyar APC
A cewar sanarwar, duk da irin gudunmawar da tsofaffin 'yan CPC suka bayar wajen nasarar APC a matakai daban-daban, ba a musu adalci wajen rabon mukamai da wakilci ba.

Kara karanta wannan
Obi, Okowa da mutanen da Atiku ya jawo jiki, amma suka fice daga PDP suka bar shi
Sanarwar ta ce:
“Yawancin tsofaffin shugabannin jihohi da mambobin CPC ba su samu wakilci mai kyau ba a matakin jihohi da na tarayya, duk da irin sadaukarwarsu,”
Sun kuma musanta rade-radin cewa za su kafa kawance da Atiku, El-Rufai ko Peter Obi, inda suka bayyana cewa hakan ba daga bakinsu ya fito ba.

Source: Facebook
'Yan tsohuwar CPC sun yi kira ga Tinubu
Kungiyar ta ce ko da yake wasu sun yanke shawarar ficewa daga APC, su dai sun zauna ne bisa turbar dimokradiyya da biyayya ga Buhari.
Daga karshe, sun bukaci gwamnatin Tinubu da ta maida hankali wajen magance matsalolin tsaro da tattalin arziki, maimakon shirin kamfen din 2027.
Asalin CPC, rawar da ta taka, da tasirinta a siyasar zamani
Tsohuwar jam’iyyar Congress for Progressive Change (CPC) ta kasance wata muhimmiya a tarihin siyasar Najeriya, musamman a lokacin da Muhammadu Buhari ya kasance gwarzonta.
Jam’iyyar ta bayyana a matsayin amsar rashin gamsuwa da jam’iyyun wancan lokacin, tare da mayar da hankali kan adalci, yaki da cin hanci da rashawa, da kuma kare muradun talakawa.
Duk da cewa CPC ta kasance karama a yawan mambobi idan aka kwatanta da jam’iyyun PDP da ANPP a lokacin, sai dai ta samu karɓuwa sosai a yankunan Arewa, musamman saboda karfin gwiwar da mutane suke dashi kan Buhari.
Bayan kafa jam’iyyar APC ta hanyar haɗakar CPC, ACN, ANPP, da wasu ‘yan bangarori daga PDP, abubuwa da dama sun sauya.
Amma tsoffin jagororin CPC sun ci gaba da rike akidarsu tare da biyayya ga tsohon shugaban kasa Buhari.
Wannan matsayi na biyayya, duk da korafe-korafe kan rabon mukamai, yana nuni da irin karfi da tasirin da CPC ke da shi har yanzu cikin tafiyar siyasa.
Har ila yau, irin wannan ɗorewar biyayya da hakuri da juriya da suka nuna na iya zama wani ginshiƙi wajen tabbatar da haɗin kai da kwanciyar hankali cikin jam’iyyar APC yayin da kasar ke tunkarar zaɓen 2027.
Malami ya yi magana kan tafiyar CPC
A wani rahoton, kun ji cewa tsohon ministan shari'a a lokacin shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan 'yan bangaren CPC da ke cikin APC.
Abubakar Malami SAN ya ce tsohon gwamnan jihar Nasarawa ba shi da hurumin yanke matsaya kan 'yan CPC da suka shiga jam'iyyar APC.
Malami ya bayyana haka ne bayan Sanata Tanko Al-Makura ya ce 'yan bangaren Buhari na CPC suna tare da shugaba Bola Ahmed Tinubu.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

