APC Ta Ƙara Ƙarfi a Kano, Tsohon na Hannun Daman Kwankwaso Ya Koma jam'iyyar
- Tsohon na hannun daman Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya koma jam’iyyar APC tare da wasu tsofaffin mambobin PDP a Kano
- Yunusa Adamu Dangwani ya bayyana cikakken goyon bayansa ga APC, yana mai cewa jam’iyyar na da tsari da shugabanci mai karfi a matakin jiha da kasa
- Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya karbi sababbin mambobi, yana mai cewa hakan zai karfafa jam’iyyar kafin zaben 2027
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso ya rasa wani babban na hannun damansa jam'iyyar APC.
Tsohon na hannun daman Rabiu Musa Kwankwaso kuma jigo a siyasar Kano, Yunusa Adamu Dangwani, ya watsar da jam’iyyar PDP zuwa APC.

Source: Facebook
Dangwani ya bayyana hakan ne yayin wani bikin sauya sheka inda wasu daga tsofaffin ‘yan jam’iyyar PDP suka sanar da shiga APC, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kwankwaso ya hadu da Barau a filin jirgi
Wannan lamari na zuwa ne bayan haduwar Sanata Kwankwaso da mataimakin shugaban Majalisar Dattawa, Sanata Barau Jibrin.
Jagoran jam’iyyar NNPP, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya hadu da mataimakin shugaban majalisar dattawa, Sanata Barau Jibrin a Abuja.
An ce 'yan siyasar sun hadu ne a filin jirgin saman kasa da kasa na Nnamdi Azikiwe da ke Abuja.
Wasu hotuna da suka bayyana sun nuna lokacin da su biyun ke musabaha cikin girmamawa da dariya, alamar mutunta juna da nuna hadin kai duk da sabanin siyasa.
Alƙawarin da Dangwani ya yi ga APC
Yayin sauya shekar, Dangwani ya sha alwashin jajircewa don nasarar jam’iyyar a zaben shekarar 2027.
Taron ya samu jagorancin Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, kuma manyan jiga-jigan jam’iyyar sun halarta domin maraba da sababbin mambobin.
Yayin jawabi a wurin taron, Dangwani wanda ya taba zama amintaccen hadimin jagoran NNPP, Sanata Kwankwaso, ya bayyana kwarin gwiwa ga tsarin APC.
Ya ce:
“Muna shirin hada kai da shugabannin APC a duk matakai don tabbatar da nasarar jam’iyyar a 2027."

Source: Facebook
Dangwani ya fadi dalilin komawa APC
Ya ce sauya shekar nasu ya biyo bayan bukatar bin jam’iyya mai karfin cika alkawura ga ‘yan Najeriya.
Shigowar Dangwani na zuwa ne a daidai lokacin da APC ke samun karin manyan ‘yan siyasa musamman duba da muhimmancin jihar Kano.
Matakin na Dangwani ya kara nuna yadda APC ke kara karfi a jihar domin fuskantar zaben 2027 da kwarin gwiwa.
Shugaban APC na Kano, Abdullahi Abbas, ya tarbi sababbin mambobin, yana mai cewa hakan zai kara karfin jam’iyyar a matakin kasa da jiha.
Bichi ya zargi Abba da barna fiye da Ganduje
Mun ba ku labarin cewa tsohon jami'i a gwamnatin Kano, Abdullahi Baffa Bichi ya ce gwamnatin Abba Kabir Yusuf ta fi gwamnatin Abdullahi Ganduje tafka barna.
Dakta Bichi ya ce yana da hujjoji da za su fallasa ayyukan barna da gwamnatin yanzu ke aikatawa cikin kasa da shekaru biyu.
A nata bangaren, gwamnatin Kano ta mayar da martani, tana cewa babu kamshin gaskiya a zarge-zargen da Baffa Bichi ya yi.
Asali: Legit.ng

