Jam'iyyar APC Ta Ƙara Nakasa El Rufai da Kwankwaso, Jiga Jigai Sun Bar PDP da NNPP

Jam'iyyar APC Ta Ƙara Nakasa El Rufai da Kwankwaso, Jiga Jigai Sun Bar PDP da NNPP

  • Jiga-jigan PDP da NNPP sama da 300 sun sauya sheka zuwa jam'iyyar APC a yankin ƙaramar hukumar Kaduna ta Arewa a Kaduna
  • Masu sauya sheƙar sun bayyana cewa gamsuwa da salon mulkin Gwamna Uba Sani ne ya ja hankalinsu suka rungumi APC mai mulki
  • Gwamna Uba Sani wanda ya gaji El-Rufai ya yi maraba da ƴan siyasar tare da alƙawarin za a tafi da su ba tare da nuna banbanci ba

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Kaduna - Akalla jiga-jogai da mambobi 300 na NNPP da PDP sun fice daga jam'iyyinsu zuwa APC a mazabar Kawo, karamar hukumar Kaduna ta Arewa.

Hakan ya zo ne a daidai lokacin da tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai, wanda ɗan Kaduna ta Arewa ne, ya haɗa kai da ƴan adawa.

Kara karanta wannan

"Ku kwantar da hankalinku," Gwamna Adeleke ya yi maganar batun ficewa daga PDP

Gwamna Uba Sani.
PDP da ƙara rasa kusoshinta Kaduna Hoto: Uba Sani
Source: Facebook

Jaridar The Nation ta tattaro cewa jiga-jigan siyasar sun tabbatar da komawa APC ne a wani taro da aka shirya domin tarbarsu a Kaduna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Nasarorin gwamna sun jawo ƴan adawa

Da yake jawabi a taron, jami'in hukumar SUBEB ta Kaduna, Dr Jamilu Haruna, ya ce wannan sauya sheka alama ce da ke nuna Gwamna Uba Sani yana kan turbar gaskiya.

Dr Jamilu, wanda ya shirya taron, ya ce Gwamna Uba Sani ya kafa shugabanci mai nagarta a cikin shekaru biyu da suka gabata.

"Wannan sauya sheka ba abin mamaki ba ne domin duk masu hangen nesa daga bangaren adawa sun shaida irin nasarorin da Gwamna Uba Sani ke samu wajen inganta tsaro, ilimi, wadatar abinci da jin dadin jama’a.
"Nasarorin sun sanya gwamnanmu ya fita daban a tsakanin takwarorinsa kuma hakan ya kara jawo masa soyayya daga wajen Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu."

- In ji Dr. Jamilu.

Kara karanta wannan

Saƙon APC ga gwamnan PDP bayan ya fara shinshinar shiga jam'iyyar

Ya kara da cewa za a mutunta wadanda suka sauya shekar daidai da kowane ɗan APC, kuma za su samu damar ba da gudummuwa wajen bunkasa jam'iyya a jiha baki ɗaya.

APC ta ƙara nakasa Kwankwaso da PDP

Da yake karbar masu sauya shekar a madadin Gwamna Uba Sani, shugaban APC na karamar hukumar Kaduna ta Arewa, Alhaji Suleiman Wada Usman, ya miƙa godiyarsa ga mahalarta taron.

Ya kuma tabbatar wa waɗanda suka shiga APC cewa za a dauke su da mutunci da adalci, ba za a nuna masu wariya ba.

APC mai mulki.
Gwamna Uba Sani ya karɓi masu canza sheka a Kaduna Hoto: @OfficialAPCNig
Source: Getty Images

Jagoran masu sauya sheƙar, tsohon dan takarar Sanatan Kaduna ta Tsakiya a inuwar PDP, Farfesa Usman Muhammad, ya ce sun shiga APC ne saboda sun gamsu da mulkin Uba Sani.

Ya ce PDP ta mayar da shi da wasu dattawan jam’iyyar marasa amfani duk da kwarewarsu da iliminsu, sannan kuma jam’iyyar na fama da rikicin da babu ranar shawo kansa.

Uba Sani ya shimfiɗa mulki na adalci

Wani ɗan APC a Kaduna ta Arewa, Aliyu Zaharadeen ya shaidawa wakilin Legit Hausa cewa wannan ba abin mamaki ba ne duba da yadda jihar ta ɗauki saiti bayan zuwan Uba Sani.

Kara karanta wannan

'Saura kiris': Gwamna ya tabbatar da shirin komawa APC bayan jita jitar barin PDP

Aliyu ya ce idan har mutum yana kishin Kaduna, babu dalilin da zai zauna a tsagin adawa domin mai girma gwamna na ƙoƙari wajen inganta walwalar talaka.

"Duk da siyasa sai da adawa amma a batu na gaskiya, Uba Sani shi ne mafita a Kaduna, ba ya nuna banbancin siyasa, kowane ɗan Kaduna na shi ne," in ji shi.

SDP ta samu ƙaruwa a Kaduna

A wani labarin, kun ji cewa jam’iyyar SDP na ci gaba da samun karɓuwa a jihar Kaduna tun bayan ficewar tsohon gwamna, Malam Nasir El-Rufai daga APC zuwa SDP.

Gaba ɗaya shugabannin jam’iyyar APC da NNPP na yankin mazaɓar Kargi da ke ƙaramar hukumar Kubau sun fice daga jam’iyyunsu zuwa SDP.

An tattaro cewa jam’iyyar SDP na kara shiga cikin harkokin siyasa da karfi a wasu ƙananan hukumomi a jihar Kaduna.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262