'Dalilin da Ya Sa PDP ba Ta Ɗauki Mataki kan Wike ba duk da Zargin Cin Amana'
- Tsohon shugaban PDP na Anambra, Cif Ndubuisi Nwobu, ya ce Nyesom Wike ya na raba kan jam’iyyar tare da goyon bayan APC
- Nwobu ya ce Wike yana da tasiri sosai a PDP tun da yake gwamna, ya cika jam’iyyar da magoya bayansa a muhimman mukamai
- Ya bayyana cewa rashin hukunta Wike ya samo asali ne daga rinjayen da ke da shi a cikin jam’iyyar, musamman a tsakanin shugabanni da ke goyon bayansa
- Nwobu ya ce PDP ta fara rusa tsarin Wike, inda aka tube sakataren jam’iyya, kuma sabon shugabanci zai fito a taron NEC da ke tafe
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
FCT, Abuja - Tsohon shugaban jam’iyyar PDP a jihar Anambra, Cif (Dr.) Ndubuisi Nwobu ya yi magana kan rigimar da ke cikin jam'iyyar.

Kara karanta wannan
"Ba za ta tsira ba": Tsohon kakakin PDP ya hango babbar musibar da ke tunkaro APC
Nwobu ya kira Ministan Abuja, Nyesom Wike da matsoraci saboda goyon bayan jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Source: Facebook
An soki Wike kan goyon bayan Tinubu
Nwobu ya bayyana hakan ne yayin wata hira da wakilin Legit.ng a Awka, babban birnin jihar Anambra.
A cewarsa, Wike wanda ya yi shekaru takwas a matsayin gwamnan Rivers, bai da karfin gwiwa ya shiga APC duk da goyon bayan Tinubu.
Ya ce:
“Da Wike na da jarumta, da ya nemi katin zama mamba a APC, amma yana ikirarin PDP ne, yana goyon bayan Tinubu."
Ya ce ba za ka iya ikirarin biyayya ga jam’iyya guda ba, kana taimakawa wata jam’iyya, wannan ba daidai ba ne a siyasa.
Karfin da Wike ke da shi a PDP
Har ila yau, ya ce lokacin da Nyesom Wike ke gwamnansa, yana da karfin fada-a-ji sosai a PDP har yana zaben shugabannin jam’iyya.
Nwobu ya ce Wike ya dasa magoya baya musamman a cikin kwamitin NWC, inda suke kare masa baya har yanzu.

Kara karanta wannan
'Saura kiris': Gwamna ya tabbatar da shirin komawa APC bayan jita jitar barin PDP
Ya kara da cewa:
“Lokacin nan, yana nuna kamar yana taimakon PDP. Amma yanzu mun gane yana kokarin cimma muradunsa ne ta hanyar dasa magoya baya.
“A lokacin yana nuna yana aiki da PDP, amma yana tabbatar da cewa kowa ya dogara da shi. Yanzu ma yana ci gaba da basu kudi."

Source: Twitter
Dalilin kin hukunta Wike a jam'iyyar PDP
Nwobu ya ce dasa magoya baya da ya yi da ƙarfinsa ya sa ba a dauki mataki a kansa ba. Amma PDP ta fara yunkurin kwato jam’iyyar daga hannunsa.
“Mun riga mun tube sakataren jam’iyya. Sauran kuma zasu biyo baya. Sakataren kasa na da mahimmanci a kowace jam’iyya."
- Cewar Nwobu
Fubara ya nemi gafarar Wike
Kun ji cewa rahotanni sun ce dakataccen Gwamna Siminalayi Fubara ya kai ziyara gidan tsohon ubangidansa, Nyesom Wike domin neman yafiya.
Ziyarar ta biyo bayan ganawa da Simi Fubara ya yi da shugaban kasa Bola Tinubu a London kan rikicin siyasar Jihar Rivers.
Majiyoyi sun ce gwamna Dapo Abiodun da tsohon gwamna Olusegun Osoba ne suka raka Fubara har gida inda ya roƙi Wike.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng